< Zabura 6 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Bisa ga sheminit. Ta Dawuda. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka. 2 Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo. 3 Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe? 4 Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka. 5 Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari? (Sheol h7585) 6 Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye. 7 Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana. 8 Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata. 9 Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata. 10 Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan.

< Zabura 6 >