< Zabura 52 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.” Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum? Me ya sa kake fariya dukan yini, kai da kake abin kunya a idanun Allah? 2 Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu. 3 Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri, ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. (Sela) 4 Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu! 5 Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka. Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka; zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. (Sela) 6 Masu adalci za su ga su ji tsoro; za su yi masa dariya, suna cewa, 7 “Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!” 8 Amma ni kamar itace zaitun ne ina haɓaka a gidan Allah; na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah har abada abadin. 9 Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.

< Zabura 52 >