< Zabura 46 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala. 2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku, 3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. (Sela) 4 Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama. 5 Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe. 6 Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke. 7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. (Sela) 8 Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya. 9 Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta. 10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.” 11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. (Sela)

< Zabura 46 >