< Zabura 3 >

1 Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni! 2 Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” (Sela) 3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. 4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. (Sela) 5 Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. 6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba. 7 Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye. 8 Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. (Sela)

< Zabura 3 >