< Zabura 134 >

1 Waƙar haurawa. Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji. 2 Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji. 3 Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona.

< Zabura 134 >