< Zabura 130 >

1 Waƙar haurawa. Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; 2 Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai. 3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya? 4 Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka. 5 Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata. 6 Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya. 7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa. 8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu.

< Zabura 130 >