< Zabura 126 >

1 Waƙar haurawa. Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki. 2 Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.” 3 Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki. 4 Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb. 5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki. 6 Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

< Zabura 126 >