< Zabura 123 >

1 Waƙar haurawa. Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama. 2 Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa. 3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa. 4 Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya.

< Zabura 123 >