< Zabura 121 >

1 Waƙar haurawa. Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo? 2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa. 3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba; 4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci. 5 Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka; 6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare. 7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka; 8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.

< Zabura 121 >