< Zabura 120 >

1 Waƙar haurawa. Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini. 2 Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara. 3 Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara? 4 Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya. 5 Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar! 6 Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama. 7 Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.

< Zabura 120 >