< Ƙidaya 32 >

1 Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki.
Now the children of Reuben and the children of Gad had a very great multitude of livestock. They saw the land of Jazer, and the land of Gilead. Behold, the place was a place for livestock.
2 Saboda haka suka zo wurin Musa da Eleyazar da kuma shugabannin jama’a, suka ce,
Then the children of Gad and the children of Reuben came and spoke to Moses, and to Eleazar the priest, and to the princes of the congregation, saying,
3 “Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon,
“Ataroth, Dibon, Jazer, Nimrah, Heshbon, Elealeh, Sebam, Nebo, and Beon,
4 ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban mutane Isra’ila, suna da kyau don dabbobi, bayinku kuma suna da dabbobi.”
the land which Yahweh struck before the congregation of Israel, is a land for livestock; and your servants have livestock.”
5 Suka ce, “In mun sami tagomashi daga gare ka bari a ba da wannan ƙasa ga bayinka, tă zama mallakanmu. Kada ka sa mu haye Urdun.”
They said, “If we have found favor in your sight, let this land be given to your servants for a possession. Don’t bring us over the Jordan.”
6 Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan?
Moses said to the children of Gad, and to the children of Reuben, “Shall your brothers go to war while you sit here?
7 Don me za ku karya zuciya Isra’ilawa daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?
Why do you discourage the heart of the children of Israel from going over into the land which Yahweh has given them?
8 Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh Barneya don su dubo ƙasar.
Your fathers did so when I sent them from Kadesh Barnea to see the land.
9 Gama bayan suka haura Kwarin Eshkol suka hangi ƙasar, sai suka karya zuciyar Isra’ilawa daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.
For when they went up to the valley of Eshcol, and saw the land, they discouraged the heart of the children of Israel, that they should not go into the land which Yahweh had given them.
10 A ranar kuwa Ubangiji ya husata har ya yi wannan rantsuwa cewa,
Yahweh’s anger burned in that day, and he swore, saying,
11 ‘Tabbatacce ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, domin ba su bi ni sosai ba,
‘Surely none of the men who came up out of Egypt, from twenty years old and upward, shall see the land which I swore to Abraham, to Isaac, and to Jacob; because they have not wholly followed me,
12 ba ko ɗaya sai dai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze da Yoshuwa ɗan Nun, don su ne kaɗai suka bi Ubangiji da zuciya ɗaya.’
except Caleb the son of Jephunneh the Kenizzite, and Joshua the son of Nun, because they have followed Yahweh completely.’
13 Ubangiji ya husata da Isra’ila har ya sa suka yi ta yawo a hamada shekara arba’in, sai da dukan tsaran da suka aikata wannan mugunta a gabansa, suka mutu.
Yahweh’s anger burned against Israel, and he made them wander back and forth in the wilderness forty years, until all the generation who had done evil in Yahweh’s sight was consumed.
14 “Ga shi ku kuma, tarin masu zunubi, kuna tsaya a matsayin kakanninku, kuna sa Ubangiji yă sāke husata da Isra’ila.
“Behold, you have risen up in your fathers’ place, an increase of sinful men, to increase the fierce anger of Yahweh toward Israel.
15 In kun juye daga binsa, zai sāke barin dukan wannan mutane a hamada, ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakarsu.”
For if you turn away from after him, he will yet again leave them in the wilderness; and you will destroy all these people.”
16 Sai suka zo wurin Musa, suka ce, “Muna so mu gina katangar dutse don dabbobinmu, da kuma birane don matanmu da’ya’yanmu a nan.
They came near to him, and said, “We will build sheepfolds here for our livestock, and cities for our little ones;
17 Matanmu da’ya’yanmu za su zauna a biranen da suke da katanga, don kāriya daga mazaunan ƙasar, amma mu, za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra’ilawa, har mu kai su wuraren zamansu.
but we ourselves will be ready armed to go before the children of Israel, until we have brought them to their place. Our little ones shall dwell in the fortified cities because of the inhabitants of the land.
18 Ba za mu koma gidajenmu ba sai kowane mutumin Isra’ila ya sami gādonsa.
We will not return to our houses until the children of Israel have all received their inheritance.
19 Ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayin gabashin Urdun.”
For we will not inherit with them on the other side of the Jordan and beyond, because our inheritance has come to us on this side of the Jordan eastward.”
20 Sai Musa ya ce musu, “In za ku yi haka, in za ku sha ɗamara da makamai a gaban Ubangiji, ku tafi yaƙi,
Moses said to them: “If you will do this thing, if you will arm yourselves to go before Yahweh to the war,
21 in kuma dukanku za ku yi ɗamara, ku ɗauki makaman yaƙi a hayin Urdun a gaban Ubangiji har lokacin da ya kori abokan gābansa daga gabansa,
and every one of your armed men will pass over the Jordan before Yahweh until he has driven out his enemies from before him,
22 to, sa’ad da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji, kwa kuɓuta daga alhakinku ga Ubangiji da kuma Isra’ila. Ƙasan nan kuwa za tă zama mallakarku a gaban Ubangiji.
and the land is subdued before Yahweh; then afterward you shall return, and be clear of obligation to Yahweh and to Israel. Then this land shall be your possession before Yahweh.
23 “Amma in ba ku yi haka ba, kun yi zunubi ke nan ga Ubangiji; kuma ku san cewa zunubinku zai tone ku.
“But if you will not do so, behold, you have sinned against Yahweh; and be sure your sin will find you out.
24 Ku gina birane domin matanku da’ya’yanku, ku gina katanga kuma domin dabbobinku, amma fa ku cika abin da kuka yi alkawari.”
Build cities for your little ones, and folds for your sheep; and do that which has proceeded out of your mouth.”
25 Mutanen Gad da mutanen Ruben, suka ce wa Musa, “Mu bayinka za mu yi yadda ranka yă daɗe ya umarta.
The children of Gad and the children of Reuben spoke to Moses, saying, “Your servants will do as my lord commands.
26 ’Ya’yanmu da matanmu, garkunan shanunmu da na tumakinmu, za su kasance a nan biranen Gileyad.
Our little ones, our wives, our flocks, and all our livestock shall be there in the cities of Gilead;
27 Amma bayinka, kowane mutum a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji, zuwa yaƙi kamar yadda ranka yă daɗe ya faɗa.”
but your servants will pass over, every man who is armed for war, before Yahweh to battle, as my lord says.”
28 Sai Musa ya yi wa Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu,
So Moses commanded concerning them to Eleazar the priest, and to Joshua the son of Nun, and to the heads of the fathers’ households of the tribes of the children of Israel.
29 ya ce, “In kowane sojan mutanen Gad da na mutanen Ruben, ya ɗauki makaman yaƙi, ya haye Urdun tare da ku a gaban Ubangiji, to, sa’ad da a ci ƙasar a gabanku, ku ba da ƙasar Gileyad tă zama mallakarsu.
Moses said to them, “If the children of Gad and the children of Reuben will pass with you over the Jordan, every man who is armed to battle before Yahweh, and the land is subdued before you, then you shall give them the land of Gilead for a possession;
30 Amma in ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo a wancan haye kamar sauran kabilun a Kan’ana.”
but if they will not pass over with you armed, they shall have possessions among you in the land of Canaan.”
31 Mutanen Gad da mutanen Ruben suka amsa, suka ce, “Barorinka za su yi abin da Ubangiji ya faɗa.
The children of Gad and the children of Reuben answered, saying, “As Yahweh has said to your servants, so will we do.
32 Za mu haye a gaban Ubangiji zuwa Kan’ana, amma mallakarmu ta gādo, za tă kasance a wannan hayi na Urdun.”
We will pass over armed before Yahweh into the land of Canaan, and the possession of our inheritance shall remain with us beyond the Jordan.”
33 Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.
Moses gave to them, even to the children of Gad, and to the children of Reuben, and to the half-tribe of Manasseh the son of Joseph, the kingdom of Sihon king of the Amorites, and the kingdom of Og king of Bashan; the land, according to its cities and borders, even the cities of the surrounding land.
34 Mutanen Gad suka gina Dibon, Atarot, Arower,
The children of Gad built Dibon, Ataroth, Aroer,
35 Atrot Shofan, Yazer, Yogbeha,
Atroth-shophan, Jazer, Jogbehah,
36 Bet-Nimra, da Bet-Haran a matsayin birane masu katanga, suka kuma gina katanga don dabbobinsu.
Beth Nimrah, and Beth Haran: fortified cities and folds for sheep.
37 Mutanen Ruben suka sāke gina Heshbon, Eleyale, da Kiriyatayim,
The children of Reuben built Heshbon, Elealeh, Kiriathaim,
38 haka kuma suka gina Nebo da Ba’al-Meyon (an canja waɗannan sunaye) suka kuma gina Sibma. Suka ba wa biranen da suka sāke ginawa sunaye.
Nebo, and Baal Meon, (their names being changed), and Sibmah. They gave other names to the cities which they built.
39 Zuriyar Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori mutanen Amoriyawa da suke can.
The children of Machir the son of Manasseh went to Gilead, took it, and dispossessed the Amorites who were therein.
40 Saboda haka Musa ya ba da Gileyad ga mutanen Makir, zuriyar Manasse, suka kuma zauna a can.
Moses gave Gilead to Machir the son of Manasseh; and he lived therein.
41 Yayir, wani ɗan Manasse, ya ci ƙauyukansu da yaƙi, ya kuma ba su sunan Hawwot Yayir.
Jair the son of Manasseh went and took its villages, and called them Havvoth Jair.
42 Noba kuma ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya kuma ba ta suna Noba, bisa ga sunansa.
Nobah went and took Kenath and its villages, and called it Nobah, after his own name.

< Ƙidaya 32 >