< Ƙidaya 29 >

1 “‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni. 2 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda,’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji, duka su kasance marasa lahani. 3 Tare da bijimin za a kuma miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; 4 kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. 5 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara. 6 Waɗannan ƙari ne ga hadayun ƙonawa na wata-wata da na kullayaumi, tare da hadayun garinsu da hadayun sha yadda aka tsara. Hadayu ne da aka miƙa wa Ubangiji ta wuta don daɗin ƙanshi. 7 “‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba. 8 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da kuma’yan raguna bakwai,’yan bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 9 Tare da bijimin a miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; 10 kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. 11 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum; tare da hadaya ta garinta, da kuma hadayu na shansu. 12 “‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai. 13 A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 14 Da kowane bijimai goma sha uku nan, a miƙa hadaya ta gari, kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da ragunan biyu ɗin, a miƙa hadaya ta gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; 15 tare kuma da kowane’yan raguna goma sha huɗu, kashi ɗaya bisa goma. 16 A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa na kullum tare da hadayarta, ta gari da kuma hadaya ta sha. 17 “‘A rana ta biyu, a miƙa bijimai goma sha biyu, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 18 Tare da bijiman, ragunan da’yan ragunan a miƙa hadayarsu da gari da hadaya ta sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade. 19 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya, don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadayunsu ta sha. 20 “‘A rana ta uku za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, raguna biyu, da kuma’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 21 Tare da bijiman, ragunan da’yan raguna, a miƙa hadayun gari da hadayun sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade. 22 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha. 23 “‘A rana ta huɗu a miƙa bijimai goma, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 24 Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade. 25 A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha. 26 “‘A rana ta biyar a miƙa bijimai tara, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 27 Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan ragunan, a miƙa hadayu na gari, da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade. 28 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha. 29 “‘A rana ta shida a miƙa bijimai takwas, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 30 Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan raguna, a miƙa hadayunsu ta gari da hadayu na sha bisa adadin da a ƙayyade. 31 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadaya ta sha. 32 “‘A rana ta bakwai a miƙa bijimai bakwai, raguna biyu da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 33 Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari, da hadayun sha bisa ga adadin da a ƙayyade. 34 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha. 35 “‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba. 36 A miƙa hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, a yi hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 37 Tare da bijimin, ragon da kuma’yan ragunan, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade. 38 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha. 39 “‘Ban da abin da kuka yi alkawari, da kuma sadakokinku na yardar rai, a miƙa waɗannan ga Ubangiji a lokacin bukukkuwanku, hadayunku na ƙonawa, hadayu na gari, hadayu na sha da hadayu na salama.’” 40 Musa ya faɗa wa Isra’ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.

< Ƙidaya 29 >