< Nehemiya 13 >

1 A wannan rana aka karanta Littafin Musa da ƙarfi a kunnuwan mutane aka kuma sami an rubuta cewa kada a karɓi mutumin Ammon ko mutumin Mowab cikin taron Allah,
On that day they read in the book of Moses in the hearing of the people; and it was found written in it that an Ammonite and a Moabite should not enter into the assembly of God forever,
2 domin ba su taryi Isra’ila da abinci da ruwa ba amma suka yi hayar Bala’am don yă kira la’ana a kansu. (Amma Allahnmu, ya mai da la’anar ta zama albarka.)
because they didn’t meet the children of Israel with bread and with water, but hired Balaam against them to curse them; however, our God turned the curse into a blessing.
3 Sa’ad da mutane suka ji wannan doka, sai suka ware daga Isra’ila duk waɗanda suke na baƙon zuriya.
It came to pass, when they had heard the law, that they separated all the mixed multitude from Israel.
4 Kafin wannan, an sa Eliyashib firist yă lura da ɗakuna ajiyar gidan Allahnmu. Yana da dangantaka na kurkusa da Tobiya,
Now before this, Eliashib the priest, who was appointed over the rooms of the house of our God, being allied to Tobiah,
5 ya kuma tanada masa babban ɗakin da dā ake ajiyar hadayun hatsi da turare da kayayyaki haikali, da kuma zakan hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai da aka umarta don Lawiyawa, mawaƙa da kuma matsaran ƙofofi, da kuma sadakoki domin firistoci.
had prepared for him a great room, where before they laid the meal offerings, the frankincense, the vessels, and the tithes of the grain, the new wine, and the oil, which were given by commandment to the Levites, the singers, and the gatekeepers; and the wave offerings for the priests.
6 Amma yayinda dukan wannan yake faruwa, ba ni a Urushalima, gama a shekara ta talatin da biyu na Artazerzes sarkin Babilon na dawo wurin sarki. A wani lokaci daga baya na nemi izininsa
But in all this, I was not at Jerusalem; for in the thirty-second year of Artaxerxes king of Babylon I went to the king; and after some days I asked leave of the king,
7 sai na koma zuwa Urushalima. A nan na ji game da mugun abin da Eliyashib ya aikata da ya tanada wa Tobiya ɗaki a filayen gidan Allah.
and I came to Jerusalem, and understood the evil that Eliashib had done for Tobiah, in preparing him a room in the courts of God’s house.
8 Na ɓace rai ƙwarai na kuma zubar da dukan kayan gidan Tobiya daga ɗakin.
It grieved me severely. Therefore I threw all Tobiah’s household stuff out of the room.
9 Na umarta a tsarkake ɗakunan, sa’an nan na mayar da kayan gidan Allah a cikin ɗakunan, tare da hadayun hatsi da kuma turare.
Then I commanded, and they cleansed the rooms. I brought into them the vessels of God’s house, with the meal offerings and the frankincense again.
10 Na kuma ji cewa sassan da ake ba wa Lawiyawa ba a ba su ba, cewa kuma dukan Lawiyawa da mawaƙan da suke da hakkin hidima sun koma gonakinsu.
I perceived that the portions of the Levites had not been given them, so that the Levites and the singers, who did the work, had each fled to his field.
11 Sai na tsawata wa shugabanni na kuma tambaye su na ce, “Me ya sa aka ƙyale gidan Allah?” Sa’an nan na kira su gaba ɗaya na sa su a wuraren aikinsu.
Then I contended with the rulers, and said, “Why is God’s house forsaken?” I gathered them together, and set them in their place.
12 Dukan Yahuda suka kawo zakan hatsi, sabon ruwan inabi da mai cikin ɗakunan ajiya.
Then all Judah brought the tithe of the grain, the new wine, and the oil to the treasuries.
13 Na sa Shelemiya firist, Zadok marubuci, da wani Balawe mai suna Fedahiya su lura da ɗakunan ajiya na kuma sa Hanan ɗan Zakkur, ɗan Mattaniya ya zama mataimakinsu, domin an ɗauka waɗannan mutane amintattu ne. Aka ba su hakkin raban kayayyaki wa’yan’uwansu.
I made treasurers over the treasuries, Shelemiah the priest, and Zadok the scribe, and of the Levites, Pedaiah: and next to them was Hanan the son of Zaccur, the son of Mattaniah; for they were counted faithful, and their business was to distribute to their brothers.
14 Ka tuna da ni saboda wannan, ya Allahna, kuma kada ka shafe abin da na yi da aminci domin gidan Allahna da kuma hidimarsa.
Remember me, my God, concerning this, and don’t wipe out my good deeds that I have done for the house of my God, and for its observances.
15 A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi,’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana.
In those days I saw some men treading wine presses on the Sabbath in Judah, bringing in sheaves, and loading donkeys with wine, grapes, figs, and all kinds of burdens which they brought into Jerusalem on the Sabbath day; and I testified against them in the day in which they sold food.
16 Mutane daga Taya waɗanda suke zama a Urushalima suna shigar da kifi da kaya iri-iri na’yan kasuwa suna kuma sayar da su a Urushalima a ranar Asabbaci wa mutanen Yahuda.
Some men of Tyre also lived there, who brought in fish and all kinds of wares, and sold on the Sabbath to the children of Judah, and in Jerusalem.
17 Sai na tsawata wa manyan Yahuda na ce musu, “Wanda irin mugun abu ke nan kuke yi, kuna ƙazantar da ranar Asabbaci?
Then I contended with the nobles of Judah, and said to them, “What evil thing is this that you do, and profane the Sabbath day?
18 Kakanninku ba su yi irin waɗannan abubuwa ba, har Allahnmu ya kawo dukan masifun nan a kanmu da kuma a kan wannan birni? Yanzu kuna tsokanar fushi mai yawa a kan Isra’ila ta wurin ƙazantar da Asabbaci.”
Didn’t your fathers do this, and didn’t our God bring all this evil on us and on this city? Yet you bring more wrath on Israel by profaning the Sabbath.”
19 Sa’ad da inuwar yamma ya fāɗo a ƙofofin Urushalima kafin Asabbaci, na umarta a rufe ƙofofi kuma kada a buɗe sai Asabbaci ya wuce. Na kafa waɗansu mutanena a ƙofofin don kada a shigo da wani kaya a ranar Asabbaci.
It came to pass that when the gates of Jerusalem began to be dark before the Sabbath, I commanded that the doors should be shut, and commanded that they should not be opened until after the Sabbath. I set some of my servants over the gates, so that no burden should be brought in on the Sabbath day.
20 Sau ɗaya ko biyu,’yan kasuwa da masu sayar da kowane irin kaya suka kwana waje da Urushalima.
So the merchants and sellers of all kinds of wares camped outside of Jerusalem once or twice.
21 Amma na ja kunnensu na ce, “Me ya sa kuke kwana kusa da katanga? In kuka ƙara yin haka, zan kama ku.” Daga wannan lokaci har zuwa gaba ba su ƙara zuwa a ranar Asabbaci ba.
Then I testified against them, and said to them, “Why do you stay around the wall? If you do so again, I will lay hands on you.” From that time on, they didn’t come on the Sabbath.
22 Sai na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu su kuma tafi su yi tsaron ƙofofi don a kiyaye ranar Asabbaci da tsarki. Ka tuna da ni saboda wannan shi ma, ya Allahna, ka nuna mini jinƙai bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.
I commanded the Levites that they should purify themselves, and that they should come and keep the gates, to sanctify the Sabbath day. Remember me for this also, my God, and spare me according to the greatness of your loving kindness.
23 Ban da haka, a waɗannan kwanakin na ga mutanen Yahuda waɗanda suka auri mata daga Ashdod, Ammon da Mowab.
In those days I also saw the Jews who had married women of Ashdod, of Ammon, and of Moab;
24 Rabin’ya’yansu suna yaren Ashdod ko kuwa wani yare na waɗansu mutane, ba su kuwa san yadda za su yi Yahudanci ba.
and their children spoke half in the speech of Ashdod, and could not speak in the Jews’ language, but according to the language of each people.
25 Na tsawata musu na kuma kira la’ana a kansu. Na bugi waɗansu mutane na kuma ja gashin kansu. Na sa suka yi rantsuwa da sunan Allah na ce, “Kada ku ba da’ya’yanku mata aure ga’ya’yansu maza, ba kuwa za ku auri’ya’yansu mata wa’ya’yanku maza ko wa kanku ba.
I contended with them, cursed them, struck certain of them, plucked off their hair, and made them swear by God, “You shall not give your daughters to their sons, nor take their daughters for your sons, or for yourselves.
26 Ba don aure-aure irin waɗannan ne Solomon sarkin Isra’ila ya yi zunubi ba? A cikin yawancin al’ummai babu sarki kamar sa. Allahnsa ya ƙaunace shi, Allah kuma ya mai da shi sarki a kan dukan Isra’ila, amma duk da haka baren mata suka rinjaye shi ga zunubi.
Didn’t Solomon king of Israel sin by these things? Yet among many nations there was no king like him, and he was loved by his God, and God made him king over all Israel. Nevertheless foreign women caused even him to sin.
27 Yanzu za mu ji cewa ku ma kuna yin duk wannan mugunta kuna zama marasa aminci ga Allahnmu ta wurin auren baren mata?”
Shall we then listen to you to do all this great evil, to trespass against our God in marrying foreign women?”
28 Ɗaya daga cikin’ya’yan Yohiyada maza, ɗan Eliyashib babban firist, surukin Sanballat mutumin Horon ne. Na kuwa kore shi daga wurina.
One of the sons of Joiada, the son of Eliashib the high priest, was son-in-law to Sanballat the Horonite; therefore I chased him from me.
29 Ka tuna da su, ya Allahna, domin sun ƙazantar da aikin firist da kuma alkawarin aikin firist da na Lawiyawa.
Remember them, my God, because they have defiled the priesthood and the covenant of the priesthood and of the Levites.
30 Saboda haka na tsarkake firistoci da Lawiyawa daga kowane baƙon abu, na kuma ba su aikinsu, kowa ga aikinsa.
Thus I cleansed them from all foreigners and appointed duties for the priests and for the Levites, everyone in his work;
31 Na kuma yi tanadi don sadakokin itace a ƙayyadaddun lokuta, da kuma don nunan fari. Ka tuna da ni da alheri, ya Allahna.
and for the wood offering, at appointed times, and for the first fruits. Remember me, my God, for good.

< Nehemiya 13 >