< Mattiyu 5 >

1 Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa,
When Jesus saw the crowds following him he went up a mountain. There he sat down together with his disciples.
2 sai ya fara koya musu. Yana cewa,
He began teaching them, saying:
3 “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.
“Blessed are those who recognize they are spiritually poor, for the kingdom of heaven is theirs.
4 Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya.
Blessed are those who mourn, for they shall be comforted.
5 Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u, gama za su gāji duniya.
Blessed are those who are kind for they will own the whole world.
6 Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci, gama za a ƙosar da su.
Blessed are those whose greatest desire is to do what is right, for they will be satisfied.
7 Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.
Blessed are those who are merciful, for they will be shown mercy.
8 Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.
Blessed are those who have pure minds, for they will see God.
9 Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su’ya’yan Allah.
Blessed are those who work to bring peace, for they will be called children of God.
10 Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci, gama mulkin sama nasu ne.
Blessed are those persecuted for what is right, for the kingdom of heaven is theirs.
11 “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.
Blessed are you when people insult you and persecute you, and accuse you of all kinds of evil things because of me.
12 Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.
Be glad, be really glad, for you will receive a great reward in heaven—for they persecuted the prophets who came before you in just the same way.
13 “Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
You are the salt of the earth, but if the salt becomes tasteless, how can you make it salty again? It's good for nothing, so it's thrown out and trodden down.
14 “Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa.
You are the light of the world. A city built on a hill can't be hidden.
15 Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida.
No one lights a lamp and then puts it under a bucket. No, it's placed on a lamp-stand and it provides light to everyone in the house.
16 Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.
In the same way you should let your light shine before everyone so they can see the good things you do and praise your heavenly Father.
17 “Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su.
Don't think I came to abolish the law or the writings of the prophets. I didn't come to abolish them, but to fulfill them.
18 Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome.
I assure you, until heaven and earth come to an end, not a single letter, not a single dot of the law will come to an end before everything is fulfilled.
19 Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama.
So whoever disregards the least important commandment, and teaches people to do so, will be called the least in the kingdom of heaven; but whoever practices and teaches the commandments will be called great in the kingdom of heaven.
20 Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.
I tell you, unless your moral rightness is more than that of the religious teachers and the Pharisees, you can never enter the kingdom of heaven.
21 “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’
You've heard that the law said to the people of long ago: ‘You shall not murder, and anyone who commits murder will be condemned as guilty.’
22 Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta. (Geenna g1067)
But I tell you, anyone who is angry with his brother will be condemned as guilty. Whoever calls his brother an idiot has to answer to the council, but whoever verbally abuses others is liable to the fire of judgment. (Geenna g1067)
23 “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci,
If you're at the altar making an offering, and remember that your brother has something against you,
24 sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.
leave your offering on the altar and go and make peace with him first, and afterwards come back and make your offering.
25 “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.
While you're on the way to court with your opponent, make sure you settle things quickly. Otherwise your opponent might hand you over to the judge, and the judge will hand you over to the court official, and you will be thrown into jail.
26 Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.
I tell you the truth: you won't get out of there until you've paid every last penny.
27 “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’
You've heard that the law said, ‘Do not commit adultery.’
28 Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.
But I tell you that everyone who looks lustfully at a woman has already committed adultery with her in his mind.
29 In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. (Geenna g1067)
If your right eye leads you to sin, then tear it out and throw it away, because it's better to lose one part of your body than to have your whole body thrown into the fire of judgment. (Geenna g1067)
30 In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. (Geenna g1067)
If your right hand leads you to sin, then cut it off and throw it away, for it's better for you to lose one of your limbs than for your whole body to go into the fire of judgment. (Geenna g1067)
31 “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’
The law also said, ‘If a man divorces his wife, he should give her a certificate of divorce.’
32 Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.
But I tell you that any man who divorces his wife except for sexual immorality causes her to commit adultery, and whoever marries a divorced woman commits adultery.
33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’
And again, you've heard that the law said to the people of long ago, ‘You shall not perjure yourself. Instead make sure you keep the oaths you swear to the Lord.’
34 Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne;
But I tell you, don't swear at all. Don't swear by heaven, because it's the throne of God.
35 ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne.
Don't swear by the earth, because it's God's footstool. Don't swear by Jerusalem, because it's the city of the great King.
36 Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba.
Don't even swear by your head, because you're not able to make a single hair white or black.
37 Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.
Simply say yes or no—more than this comes from the evil one.
38 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’
You've heard that the law said, ‘An eye for an eye, and a tooth for a tooth.’
39 Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma.
But I tell you, don't resist someone who is evil. If someone slaps you on the right cheek, turn the other cheek to them as well.
40 In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma.
If someone wants to sue you in court and takes your shirt, give them your coat too.
41 In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu.
If someone demands that you go one mile, go with them two.
42 Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.
Give to those who ask you, and don't turn away those who want to borrow from you.
43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’
You've heard that the law said, ‘Love your neighbor and hate your enemy.’
44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābankukuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,
But I tell you, love your enemies and pray for those who persecute you,
45 don ku zama’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.
so you may become children of your heavenly Father. For his sun shines on both the good and the bad; and he makes the rain fall on both those who do right and those who do wrong.
46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?
For if you only love those who love you, what reward do you have? Don't even the tax-collectors do that?
47 In kuwa kuna gai da’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba?
If you only speak kindly to your family, what more are you doing than anyone else? Even the heathen do that!
48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.
Grow up and become completely trustworthy, just as your heavenly Father is trustworthy.

< Mattiyu 5 >