< Luka 5 >

1 Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah,
Now it happened, while the crowd pressed on him and heard the word of God, that he was standing by the lake of Gennesaret.
2 sai ya hangi jiragen ruwa biyu a bakin tafkin, waɗanda masu kamun kifi suka bari suna wankin abin kamun kifinsu.
He saw two boats standing by the lake, but the fishermen had gone out of them, and were washing their nets.
3 Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki.
He entered into one of the boats, which was Shimon's, and asked him to put out a little from the land. He sat down and taught the crowds from the boat.
4 Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.”
When he had finished speaking, he said to Shimon, "Put out into the deep, and let down your nets for a catch."
5 Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.”
Shimon answered him, "Master, we worked all night, and took nothing; but at your word I will let down the nets."
6 Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har abin kamun kifinsu suka fara tsintsinkewa.
When they had done this, they caught a great multitude of fish, and their net was breaking.
7 Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa.
They beckoned to their partners in the other boat, that they should come and help them. They came, and filled both boats, so that they began to sink.
8 Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!”
But Shimon Kipha, when he saw it, fell down at Yeshua's knees, saying, "Depart from me, for I am a sinful man, Lord."
9 Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama.
For he was amazed, and all who were with him, at the catch of fish which they had caught;
10 Yaƙub da Yohanna,’ya’yan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.”
and so also were Yaquv and Yukhanan, sons of Zabedai, who were partners with Shimon. Yeshua said to Shimon, "Do not be afraid. From now on you will be catching people."
11 Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi.
When they had brought their boats to land, they left everything, and followed him.
12 Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni.”
It happened, while he was in one of the cities, look, there was a man full of leprosy. When he saw Yeshua, he fell on his face, and begged him, saying, "Lord, if you want to, you can make me clean."
13 Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.
And he stretched out his hand, and touched him, saying, "I am willing. Be cleansed." Immediately the leprosy left him.
14 Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.”
And he commanded him, "Do not tell anyone, but go your way, and show yourself to the priest, and offer for your cleansing according to what Mushe commanded, for a testimony to them."
15 Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu.
But the report concerning him spread much more, and large crowds came together to hear, and to be healed of their infirmities.
16 Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yă yi addu’a.
But he withdrew himself into the desert, and prayed.
17 Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yă warkar da masu ciwo.
It happened on one of those days, that he was teaching; and there were Pharisees and teachers of the Law sitting by, who had come out of every village of Galila, Yehuda, and Urishlim. The power of the Lord was with him to heal.
18 Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu.
And look, men brought a paralyzed man on a cot, and they sought to bring him in to lay before him.
19 Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.
Not finding a way to bring him in because of the crowd, they went up to the housetop, and let him down through the tiles with his cot into the midst before Yeshua.
20 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Saurayi, an gafarta maka zunubanka.”
Seeing their faith, he said, "Man, your sins are forgiven you."
21 Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”
The scribes and the Pharisees began to reason, saying, "Who is this that speaks blasphemies? Who can forgive sins, but God alone?"
22 Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku?
But Yeshua, perceiving their thoughts, answered them, "Why are you reasoning so in your hearts?
23 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?
Which is easier to say, 'Your sins are forgiven you;' or to say, 'Arise and walk?'
24 Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”
But that you may know that the Son of Man has authority on earth to forgive sins" (he said to the paralyzed man), "I tell you, arise, and take up your cot, and go to your house."
25 Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.
Immediately he rose up before them, and took up that which he was laying on, and departed to his house, glorifying God.
26 Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”
Amazement took hold on all, and they glorified God. They were filled with fear, saying, "We have seen remarkable things today."
27 Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.”
After these things he went out, and saw a tax collector named Lewi sitting at the tax office, and said to him, "Follow me."
28 Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi.
He left everything, and rose up and followed him.
29 Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su.
Lewi made a great feast for him in his house. There was a large crowd of tax collectors and others who were reclining with them.
30 Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”
The Pharisees and their scribes grumbled at his disciples, saying, "Why do you eat and drink with the tax collectors and sinners?"
31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
Yeshua answered them, "Those who are healthy have no need for a physician, but those who are sick do.
32 Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”
I have not come to call the righteous, but sinners to repentance."
33 Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da addu’a, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.”
They said to him, "The disciples of Yukhanan often fast and pray, likewise also the disciples of the Pharisees, but yours eat and drink."
34 Yesu ya amsa ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su?
He said to them, "Can you make the friends of the bridegroom fast, while the bridegroom is with them?
35 Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.”
But the days will come when the bridegroom will be taken away from them. Then they will fast in those days."
36 Sai ya faɗa musu wannan misali ya ce, “Ba wanda yakan yage ƙyalle daga sabuwar riga ya yi wa tsohuwar riga faci. In ya yi haka, zai yage sabuwar rigar, kuma facin daga sabuwar ba zai dace da tsohuwar rigar ba.
He also told a parable to them. "No one having torn a piece from a new garment puts it on an old garment, or else he will tear the new, and also the piece from the new will not match the old.
37 Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yă zube, salkunan kuma su lalace.
And no one puts new wine into old wineskins, or else the new wine will burst the skins, and it will be spilled, and the skins will be destroyed.
38 A’a, sai dai a zuba sabon ruwan inabi a sababbin salkuna.
But new wine must be put into fresh wineskins.
39 Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’”
No one having drunk old wine desires new, for he says, 'The old is good.'"

< Luka 5 >