< Luka 3 >

1 A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline. 2 A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada. 3 Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 4 Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa. 5 Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul. 6 Dukan’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’” 7 Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yă yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8 Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da’ya’ya wa Ibrahim. 9 An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.” 10 Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?” 11 Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.” 12 Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?” 13 Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.” 14 Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.” 15 Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa. 16 Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma. 17 Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.” 18 Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara. 19 Amma da Yohanna ya tsawata wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi, 20 Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku. 21 Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe, 22 Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.” 23 To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa sa’ad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne, ɗan Heli, 24 ɗan Mattat, ɗan Lawi, ɗan Melki, ɗan Yannai, ɗan Yusuf, 25 ɗan Mattatiyas, ɗan Amos, ɗan Nahum, ɗan Esli, ɗan Naggai, 26 ɗan Ma’at, ɗan Mattatiyas, ɗan Semeyin, ɗan Yosek, ɗan Yoda, 27 ɗan Yowanan, ɗan Resa, ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel, ɗan Neri, 28 ɗan Melki, ɗan Addi, ɗan Kosam, ɗan Elmadam, ɗan Er, 29 ɗan Yoshuwa, ɗan Eliyezer, ɗan Yorim, ɗan Mattat, ɗan Lawi, 30 ɗan Simeyon, ɗan Yahuda, ɗan Yusuf, ɗan Yonam, ɗan Eliyakim, 31 ɗan Meleya, ɗan Menna, ɗan Mattata, ɗan Natan, ɗan Dawuda, 32 ɗan Yesse, ɗan Obed, ɗan Bowaz, ɗan Salmon, ɗan Nashon, 33 ɗan Amminadab, ɗan Ram, ɗan Hezron, ɗan Ferez, ɗan Yahuda, 34 ɗan Yaƙub, ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim, ɗan Tera, ɗan Nahor, 35 ɗan Serug, ɗan Reyu, ɗan Feleg, ɗan Eber, ɗan Sala, 36 ɗan Kainan, ɗan Arfakshad, ɗan Shem, ɗan Nuhu, ɗan Lamek, 37 ɗan Metusela, ɗan Enok, ɗan Yared, ɗan Mahalalel, ɗan Kainan, 38 ɗan Enosh, ɗan Shitu, ɗan Adamu, ɗan Allah.

< Luka 3 >