< Luka 3 >

1 A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.
Ἐν ἔτει δὲ πεντεκαιδεκάτῳ τῆς ἡγεμονίας Τιβερίου Καίσαρος, ἡγεμονεύοντος Ποντίου Πιλάτου τῆς Ἰουδαίας, καὶ τετραρχοῦντος τῆς Γαλιλαίας Ἡρῴδου, Φιλίππου δὲ τοῦ ἀδελφοῦ αὐτοῦ τετραρχοῦντος τῆς Ἰτουραίας καὶ Τραχωνίτιδος χώρας, καὶ Λυσανίου τῆς Ἀβιληνῆς τετραρχοῦντος,
2 A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.
ἐπ᾿ ἀρχιερέων Ἄννα καὶ Καϊάφα, ἐγένετο ῥῆμα Θεοῦ ἐπὶ Ἰωάννην τὸν τοῦ Ζαχαρίου υἱὸν ἐν τῇ ἐρήμῳ.
3 Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.
Καὶ ἦλθεν εἰς πᾶσαν τὴν περίχωρον τοῦ Ἰορδάνου, κηρύσσων βάπτισμα μετανοίας εἰς ἄφεσιν ἁμαρτιῶν·
4 Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.
ὡς γέγραπται ἐν βίβλῳ λόγων Ἠσαΐου τοῦ προφήτου, λέγοντος, Φωνὴ βοῶντος ἐν τῇ ἐρήμῳ, Ἑτοιμάσατε τὴν ὁδὸν Κυρίου· εὐθείας ποιεῖτε τὰς τρίβους αὐτοῦ.
5 Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.
Πᾶσα φάραγξ πληρωθήσεται, καὶ πᾶν ὄρος καὶ βουνὸς ταπεινωθήσεται· καὶ ἔσται τὰ σκολιὰ εἰς εὐθεῖαν, καὶ αἱ τραχεῖαι εἰς ὁδοὺς λείας·
6 Dukan’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’”
καὶ ὄψεται πᾶσα σὰρξ τὸ σωτήριον τοῦ Θεοῦ.
7 Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yă yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?
Ἔλεγεν οὖν τοῖς ἐκπορευομένοις ὄχλοις βαπτισθῆναι ὑπ᾿ αὐτοῦ, Γεννήματα ἐχιδνῶν, τίς ὑπέδειξεν ὑμῖν φυγεῖν ἀπὸ τῆς μελλούσης ὀργῆς;
8 Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da’ya’ya wa Ibrahim.
Ποιήσατε οὖν καρποὺς ἀξίους τῆς μετανοίας· καὶ μὴ ἄρξησθε λέγειν ἐν ἑαυτοῖς, Πατέρα ἔχομεν τὸν Ἀβραάμ· λέγω γὰρ ὑμῖν ὅτι δύναται ὁ Θεὸς ἐκ τῶν λίθων τούτων ἐγεῖραι τέκνα τῷ Ἀβραάμ.
9 An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.”
Ἤδη δὲ καὶ ἡ ἀξίνη πρὸς τὴν ῥίζαν τῶν δένδρων κεῖται· πᾶν οὖν δένδρον μὴ ποιοῦν καρπὸν καλὸν ἐκκόπτεται καὶ εἰς πῦρ βάλλεται.
10 Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?”
Καὶ ἐπηρώτων αὐτὸν οἱ ὄχλοι λέγοντες, Τί οὖν ποιήσομεν;
11 Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.”
Ἀποκριθεὶς δὲ λέγει αὐτοῖς, Ὁ ἔχων δύο χιτῶνας μεταδότω τῷ μὴ ἔχοντι· καὶ ὁ ἔχων βρώματα ὁμοίως ποιείτω.
12 Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?”
Ἦλθον δὲ καὶ τελῶναι βαπτισθῆναι, καὶ εἶπον πρὸς αὐτόν, Διδάσκαλε, τί ποιήσομεν;
13 Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”
Ὁ δὲ εἶπε πρὸς αὐτούς, Μηδὲν πλέον παρὰ τὸ διατεταγμένον ὑμῖν πράσσετε.
14 Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”
Ἐπηρώτων δὲ αὐτὸν καὶ στρατευόμενοι, λέγοντες, Καὶ ἡμεῖς τί ποιήσομεν; Καὶ εἶπε πρὸς αὐτούς, Μηδένα διασείσητε, μηδὲ συκοφαντήσητε· καὶ ἀρκεῖσθε τοῖς ὀψωνίοις ὑμῶν.
15 Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa.
Προσδοκῶντος δὲ τοῦ λαοῦ, καὶ διαλογιζομένων πάντων ἐν ταῖς καρδίαις αὐτῶν περὶ τοῦ Ἰωάννου, μήποτε αὐτὸς εἴη ὁ Χριστός,
16 Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma.
ἀπεκρίνατο ὁ Ἰωάννης, ἅπασι λέγων, Ἐγὼ μὲν ὕδατι βαπτίζω ὑμᾶς· ἔρχεται δὲ ὁ ἰσχυρότερός μου, οὗ οὐκ εἰμὶ ἱκανὸς λῦσαι τὸν ἱμάντα τῶν ὑποδημάτων αὐτοῦ· αὐτὸς ὑμᾶς βαπτίσει ἐν πνεύματι ἁγίῳ καὶ πυρί·
17 Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
οὗ τὸ πτύον ἐν τῇ χειρὶ αὐτοῦ, καὶ διακαθαριεῖ τὴν ἅλωνα αὐτοῦ, καὶ συνάξει τὸν σῖτον εἰς τὴν ἀποθήκην αὐτοῦ, τὸ δὲ ἄχυρον κατακαύσει πυρὶ ἀσβέστῳ.
18 Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara.
Πολλὰ μὲν οὖν καὶ ἕτερα παρακαλῶν εὐηγγελίζετο τὸν λαόν·
19 Amma da Yohanna ya tsawata wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi,
ὁ δὲ Ἡρῴδης ὁ τετράρχης, ἐλεγχόμενος ὑπ᾿ αὐτοῦ περὶ Ἡρῳδιάδος τῆς γυναικὸς Φιλίππου τοῦ ἀδελφοῦ αὐτοῦ, καὶ περὶ πάντων ὧν ἐποίησε πονηρῶν ὁ Ἡρῴδης,
20 Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku.
προσέθηκε καὶ τοῦτο ἐπὶ πᾶσι, καὶ κατέκλεισε τὸν Ἰωάννην ἐν τῇ φυλακῇ.
21 Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe,
Ἐγένετο δὲ ἐν τῷ βαπτισθῆναι ἅπαντα τὸν λαόν, καὶ Ἰησοῦ βαπτισθέντος καὶ προσευχομένου, ἀνεῳχθῆναι τὸν οὐρανόν,
22 Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”
καὶ καταβῆναι τὸ πνεῦμα τὸ ἅγιον σωματικῷ εἴδει ὡσεὶ περιστερὰν ἐπ᾿ αὐτόν, καὶ φωνὴν ἐξ οὐρανοῦ γενέσθαι, λέγουσαν, Σὺ εἶ ὁ υἱός μου ὁ ἀγαπητός, ἐν σοὶ ηὐδόκησα.
23 To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa sa’ad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne, ɗan Heli,
Καὶ αὐτὸς ἦν ὁ Ἰησοῦς ὡσεὶ ἐτῶν τριάκοντα ἀρχόμενος, ὢν — ὡς ἐνομίζετο — υἱὸς Ἰωσήφ, τοῦ Ἡλί,
24 ɗan Mattat, ɗan Lawi, ɗan Melki, ɗan Yannai, ɗan Yusuf,
τοῦ Ματθάτ, τοῦ Λευΐ, τοῦ Μελχί, τοῦ Ἰαννά, τοῦ Ἰωσήφ,
25 ɗan Mattatiyas, ɗan Amos, ɗan Nahum, ɗan Esli, ɗan Naggai,
τοῦ Ματταθίου, τοῦ Ἀμώς, τοῦ Ναούμ, τοῦ Ἐσλί, τοῦ Ναγγαί,
26 ɗan Ma’at, ɗan Mattatiyas, ɗan Semeyin, ɗan Yosek, ɗan Yoda,
τοῦ Μαάθ, τοῦ Ματταθίου, τοῦ Σεμεΐ, τοῦ Ἰωσήφ, τοῦ Ἰούδα,
27 ɗan Yowanan, ɗan Resa, ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel, ɗan Neri,
τοῦ Ἰωαννᾶ, τοῦ Ῥησά, τοῦ Ζοροβάβελ, τοῦ Σαλαθιήλ, τοῦ Νηρί,
28 ɗan Melki, ɗan Addi, ɗan Kosam, ɗan Elmadam, ɗan Er,
τοῦ Μελχί, τοῦ Ἀδδί, τοῦ Κωσάμ, τοῦ Ἐλμωδάμ, τοῦ Ἤρ,
29 ɗan Yoshuwa, ɗan Eliyezer, ɗan Yorim, ɗan Mattat, ɗan Lawi,
τοῦ Ἰωσή, τοῦ Ἐλιέζερ, τοῦ Ἰωρείμ, τοῦ Ματθάτ, τοῦ Λευΐ,
30 ɗan Simeyon, ɗan Yahuda, ɗan Yusuf, ɗan Yonam, ɗan Eliyakim,
τοῦ Συμεών, τοῦ Ἰούδα, τοῦ Ἰωσήφ, τοῦ Ἰωνάν, τοῦ Ἐλιακείμ,
31 ɗan Meleya, ɗan Menna, ɗan Mattata, ɗan Natan, ɗan Dawuda,
τοῦ Μελεᾶ, τοῦ Μαϊνάν, τοῦ Ματταθά, τοῦ Ναθάν, τοῦ Δαβίδ,
32 ɗan Yesse, ɗan Obed, ɗan Bowaz, ɗan Salmon, ɗan Nashon,
τοῦ Ἰεσσαί, τοῦ Ὠβήδ, τοῦ Βοόζ, τοῦ Σαλμών, τοῦ Ναασσών,
33 ɗan Amminadab, ɗan Ram, ɗan Hezron, ɗan Ferez, ɗan Yahuda,
τοῦ Ἀμιναδάβ, τοῦ Ἀράμ, τοῦ Ἑσρώμ, τοῦ Φαρές, τοῦ Ἰούδα,
34 ɗan Yaƙub, ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim, ɗan Tera, ɗan Nahor,
τοῦ Ἰακώβ, τοῦ Ἰσαάκ, τοῦ Ἀβραάμ, τοῦ Θάρα, τοῦ Ναχώρ,
35 ɗan Serug, ɗan Reyu, ɗan Feleg, ɗan Eber, ɗan Sala,
τοῦ Σαρούχ, τοῦ Ῥαγαῦ, τοῦ Φαλέκ, τοῦ Ἑβέρ, τοῦ Σαλά,
36 ɗan Kainan, ɗan Arfakshad, ɗan Shem, ɗan Nuhu, ɗan Lamek,
τοῦ Καϊνάν, τοῦ Ἀρφαξάδ, τοῦ Σήμ, τοῦ Νῶε, τοῦ Λάμεχ,
37 ɗan Metusela, ɗan Enok, ɗan Yared, ɗan Mahalalel, ɗan Kainan,
τοῦ Μαθουσάλα, τοῦ Ἐνώχ, τοῦ Ἰαρέδ, τοῦ Μαλελεήλ, τοῦ Καϊνάν,
38 ɗan Enosh, ɗan Shitu, ɗan Adamu, ɗan Allah.
τοῦ Ἐνώς, τοῦ Σήθ, τοῦ Ἀδάμ, τοῦ Θεοῦ.

< Luka 3 >