< Luka 19 >

1 Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta.
He entered and was passing through Jericho.
2 Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma.
There was a man named Zacchaeus. He was a chief tax collector, and he was rich.
3 Ya so yă ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne.
He was trying to see who Yeshua was, and couldn’t because of the crowd, because he was short.
4 Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don yă gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne.
He ran on ahead and climbed up into a sycamore tree to see him, for he was going to pass that way.
5 Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.”
When Yeshua came to the place, he looked up and saw him, and said to him, “Zacchaeus, hurry and come down, for today I must stay at your house.”
6 Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna.
He hurried, came down, and received him joyfully.
7 Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’”
When they saw it, they all murmured, saying, “He has gone in to lodge with a man who is a sinner.”
8 Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”
Zacchaeus stood and said to the Lord, “Behold, Lord, half of my goods I give to the poor. If I have wrongfully exacted anything of anyone, I restore four times as much.”
9 Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne.
Yeshua said to him, “Today, salvation has come to this house, because he also is a son of Abraham.
10 Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”
For the Son of Man came to seek and to save that which was lost.”
11 Yayinda suna cikin sauraron wannan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, kuma mutanen suna tsammani mulkin Allah zai bayyana, nan da nan.
As they heard these things, he went on and told a parable, because he was near Jerusalem, and they supposed that God’s Kingdom would be revealed immediately.
12 Ya ce, “Wani mutum mai martaba ya tafi wata ƙasa mai nisa don a naɗa shi sarki sa’an nan ya dawo.
He said therefore, “A certain nobleman went into a far country to receive for himself a kingdom and to return.
13 Saboda haka ya kira bayinsa goma ya ba su mina goma. Ya ce, ‘Ku yi kasuwanci da kuɗin nan, sai na dawo.’
He called ten servants of his and gave them ten mina coins, and told them, ‘Conduct business until I come.’
14 “Amma talakawansa suka ƙi shi, sai suka aikar da wakilai bayansa, domin su ce, ‘Ba mu son wannan mutum ya zama sarkinmu.’
But his citizens hated him, and sent an envoy after him, saying, ‘We don’t want this man to reign over us.’
15 “Duk da haka, aka naɗa shi sarki, sa’an nan ya dawo gida. Sai ya aika aka kira bayin da ya ba su kuɗin, don yă san ribar da suka samu.
“When he had come back again, having received the kingdom, he commanded these servants, to whom he had given the money, to be called to him, that he might know what they had gained by conducting business.
16 “Na fari ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar goma.’
The first came before him, saying, ‘Lord, your mina has made ten more minas.’
17 “Maigidan ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawana mai kirki! Tun da ka yi aminci a kan abu ƙanƙani, ka yi riƙon birane goma.’
“He said to him, ‘Well done, you good servant! Because you were found faithful with very little, you shall have authority over ten cities.’
18 “Na biyun ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar biyar.’
“The second came, saying, ‘Your mina, Lord, has made five minas.’
19 “Maigidansa ya ce, ‘Kai ka yi riƙon birane biyar.’
“So he said to him, ‘And you are to be over five cities.’
20 “Sai wani bawan ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ga minarka. Na ɓoye shi a wani ɗan tsumma.
Another came, saying, ‘Lord, behold, your mina, which I kept laid away in a handkerchief,
21 Na ji tsoronka, don kai mai wuyan sha’ani ne. Kakan ɗauki abin da ba ka ajiye ba, kakan kuma yi girbin abin da ba ka shuka ba.’
for I feared you, because you are an exacting man. You take up that which you didn’t lay down, and reap that which you didn’t sow.’
22 “Sai maigidansa, ya amsa ya ce, ‘Zan hukunta ka a kan kalmominka, kai mugun bawa! Ashe, ka san cewa ni mai wuyan sha’ani ne, nakan ɗauka abin da ban ajiye ba, ina kuma girbin abin da ban shuka ba?
“He said to him, ‘Out of your own mouth I will judge you, you wicked servant! You knew that I am an exacting man, taking up that which I didn’t lay down and reaping that which I didn’t sow.
23 Don me ba ka sa kuɗina a wajen ajiya, don in na dawo, in sami riba a kai ba?’
Then why didn’t you deposit my money in the bank, and at my coming, I might have earned interest on it?’
24 “Sai ya ce wa waɗanda suke tsaye a wajen, ‘Ku karɓi minarsa ku ba wa wanda yake da mina goma.’
He said to those who stood by, ‘Take the mina away from him and give it to him who has the ten minas.’
25 “Suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ai, yana da guda goma ko!’
“They said to him, ‘Lord, he has ten minas!’
26 “Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da shi kuwa, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe.
‘For I tell you that to everyone who has, will more be given; but from him who doesn’t have, even that which he has will be taken away from him.
27 Amma waɗannan abokan gābana, waɗanda ba su so in zama sarkinsu ba, ku kawo su nan, ku karkashe su, a gabana.’”
But bring those enemies of mine who didn’t want me to reign over them here, and kill them before me.’”
28 Bayan Yesu ya yi wannan magana, sai ya yi gaba zuwa Urushalima.
Having said these things, he went on ahead, going up to Jerusalem.
29 Da ya kai kusa da Betfaji da Betani, a tudun da ake kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, ya ce musu,
When he came near to Bethsphage and Bethany, at the mountain that is called Olivet, he sent two of his disciples,
30 “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a daure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan.
saying, “Go your way into the village on the other side, in which, as you enter, you will find a colt tied, which no man has ever sat upon. Untie it and bring it.
31 In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke kunce shi?’ Ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatarsa.’”
If anyone asks you, ‘Why are you untying it?’ say to him: ‘The Lord needs it.’”
32 Waɗanda aka aika su yi gaba suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya gaya musu.
Those who were sent went away and found things just as he had told them.
33 Suna cikin kunce ɗan jakin, sai masu ɗan jakin suka ce musu, “Don me kuke kunce shi?”
As they were untying the colt, its owners said to them, “Why are you untying the colt?”
34 Suka amsa suka ce, “Ubangiji ne na bukatarsa.”
They said, “The Lord needs it.”
35 Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, sa’an nan suka sa Yesu a kai.
Then they brought it to Yeshua. They threw their cloaks on the colt and sat Yeshua on them.
36 Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya.
As he went, they spread their cloaks on the road.
37 Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,
As he was now getting near, at the descent of the Mount of Olives, the whole multitude of the disciples began to rejoice and praise God with a loud voice for all the mighty works which they had seen,
38 “Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”
saying, “Blessed is the King who comes in the name of the Lord! Peace in heaven, and glory in the highest!”
39 Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!”
Some of the Pharisees from the multitude said to him, “Rabbi, rebuke your disciples!”
40 Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.”
He answered them, “I tell you that if these were silent, the stones would cry out.”
41 Da ya yi kusa da Urushalima, ya kuma ga birnin, sai ya yi kuka a kanta,
When he came near, he saw the city and wept over it,
42 kuma ya ce, “In ke, ko ke ɗin ma, dā ma kin san abin da zai kawo miki salama a wannan rana, amma yanzu an ɓoye shi daga idanunki.
saying, “If you, even you, had known today the things which belong to your peace! But now, they are hidden from your eyes.
43 Ranakun za su auko miki, a lokacin da abokan gābanki za su gina bango gāba da ke, su kuma kewaye inda kike, za su kuma tsare kowane gefenki, su sa ke a tsakiya.
For the days will come on you when your enemies will throw up a barricade against you, surround you, hem you in on every side,
44 Za su fyaɗa ke a ƙasa, ke da’ya’yan da suke cikin katanganki. Ba za su bar wani dutse a kan wani ba, saboda ba ki gane da lokacin da Allah zai ziyarce ki ba.”
and will dash you and your children within you to the ground. They will not leave in you one stone on another, because you didn’t know the time of your visitation.”
45 Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya.
He entered into the temple and began to drive out those who bought and sold in it,
46 Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’amma ga shi kun mai da shi ‘kogon’yan fashi.’”
saying to them, “It is written, ‘My house is a house of prayer,’ but you have made it a ‘den of robbers’!”
47 Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi.
He was teaching daily in the temple, but the chief priests, the scribes, and the leading men amongst the people sought to destroy him.
48 Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen.
They couldn’t find what they might do, for all the people hung on to every word that he said.

< Luka 19 >