< Luka 17 >

1 Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa.
Jesus said to His disciples, "It is inevitable that causes of stumbling should come; but alas for him through whom they come!
2 Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi.
It would be well for him if, with a millstone round his neck, he were lying at the bottom of the sea, rather than that he should cause even one of these little ones to fall.
3 Saboda haka, ku lura da kanku. “In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa.
Be on your guard. "If your brother acts wrongly, reprove him; and if he is sorry, forgive him;
4 In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.”
and if seven times in a day he acts wrongly towards you, and seven times turns again to you and says, 'I am sorry,' you must forgive him."
5 Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!”
And the Apostles said to the Lord, "Give us faith."
6 Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.
"If your faith," replied the Lord, "is like a mustard seed, you might command this black-mulberry-tree, 'Tear up your roots and plant yourself in the sea,' and instantly it would obey you.
7 “In ɗaya a cikinku yana da bawa, wanda yake masa noma, ko kiwon tumaki, da dawowar bawan daga gonar, ai, ba zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna, ka ci abinci ba’?
But which of you who has a servant ploughing, or tending sheep, will say to him when he comes in from the farm, 'Come at once and take your place at table,'
8 Ashe, ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma, ka shirya ka yi mini hidima domin in ci in sha, bayan haka kana iya ci, ka kuma sha ba’?
and will not rather say to him, 'Get my dinner ready, make yourself tidy, and wait upon me till I have finished my dinner, and then you shall have yours'?
9 Shin, zai gode wa bawan don yă yi aikin da aka ce ya yi ne?
Does he thank the servant for obeying his orders?
10 Haka ku ma, bayan kun yi duk abin da aka ce muku ku yi, ya kamata ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta, mun dai yi aikinmu ne kaɗai.’”
So you also, when you have obeyed all the orders given you, must say, "'There is no merit in our service: what we have done is only what we were in duty bound to do.'"
11 Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili.
As they pursued their journey to Jerusalem, He passed through Samaria and Galilee.
12 Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa,
And as He entered a certain village, ten men met Him who were lepers and stood at a distance.
13 suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”
In loud voices they cried out, "Jesus, Rabbi, take pity on us."
14 Da ya gan su sai ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.
Perceiving this, He said to them, "Go and show yourselves to the Priests." And while on their way to do this they were made clean.
15 Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya.
One of them, seeing that he was cured, came back, adoring and praising God in a loud voice,
16 Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.
and he threw himself at the feet of Jesus, thanking Him. He was a Samaritan.
17 Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran?
"Were not all ten made clean?" Jesus asked; "but where are the nine?
18 Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?”
Have none been found to come back and give glory to God except this foreigner?"
19 Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.”
And He said to him, "Rise and go: your faith has cured you."
20 Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin kallon ku ba.
Being asked by the Pharisees when the Kingdom of God was coming, He answered, "The Kingdom of God does not so come that you can stealthily watch for it.
21 Mutane kuma ba za su ce, ‘Ga shi nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can’ ba, domin mulkin Allah yana cikinku ne.”
Nor will they say, 'See here!' or 'See there!' --for the Kingdom of God is within you."
22 Sai ya ce wa almajiransa, “Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin rana ɗaya cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba.
Then, turning to His disciples, He said, "There will come a time when you will wish you could see a single one of the days of the Son of Man, but will not see one.
23 Mutane za su ce muku, ‘Ga shi can!’ Ko kuma, ‘Ga shi nan!’ Kada ku yi hanzarin binsu.
And they will say to you, 'See there!' 'See here!' Do not start off and go in pursuit.
24 Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa.
For just as the lightning, when it flashes, shines from one part of the horizon to the opposite part, so will the Son of Man be on His day.
25 Amma da fari, dole yă sha wahaloli masu yawa, kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi.
But first He must endure much suffering, and be rejected by the present generation.
26 “Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum.
"And as it was in the time of Noah, so will it also be in the time of the Son of Man.
27 Mutane suna ci, suna sha, suna aurayya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Sa’an nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka.
Men were eating and drinking, taking wives and giving wives, up to the very day on which Noah entered the Ark, and the Deluge came and destroyed them all.
28 “Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine.
The same was true in the time of Lot: they were eating and drinking, buying and selling, planting and building;
29 Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka.
but on the day that Lot left Sodom, God rained fire and brimstone from the sky and destroyed them all.
30 “Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana.
Exactly so will it be on the day that the veil is lifted from the Son of Man.
31 A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don yă kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada yă koma don wani abu.
"On that day, if a man is on the roof and his property indoors, let him not go down to fetch it; and, in the same way, he who is in the field, let him not turn back.
32 Ku tuna fa da matar Lot!
Remember Lot's wife.
33 Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi.
Any man who makes it his object to keep his own life safe, will lose it; but whoever loses his life will preserve it.
34 Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.
On that night, I tell you, there will be two men in one bed: one will be taken away and the other left behind.
35 Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.”
There will be two women turning the mill together: one will be taken away and the other left behind."
37 Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.”
"Where, Master?" they inquired. "Where the dead body is," He replied, "there also will the vultures flock together."

< Luka 17 >