< Luka 11 >

1 Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.”
It happened he was praying in a certain place, and when he stopped, one of his disciples said to him, "Master, teach us how to pray, just as Johntaught his disciples."
2 Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce, “‘Ya Uba, sunanka mai tsarki ne mulkinka ya zo.
So he said to them. "When you pray, say, "Father, hallowed be thy name; May thy kingdom come,
3 Ka ba mu kowace rana abincin yini.
"Give us day by day our bread for the coming day;
4 Ka gafarta mana zunubanmu, kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi. Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’”
"Forgive us our sins; for we also forgive everyone who has offended us; "And bring us not into temptation."
5 Sa’an nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, sa’an nan ya je wurinsa da tsakar dare ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku,
He also said to them. "Suppose you have a friend and you go to him, ‘My friend, lend me three loaves of bread,
6 domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’
"for a friend of mine is come to me from a journey, and I have nothing to set before him.’
7 Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’
"and he from indoors shall answer. ‘Do not pester me. The door is now closed, and my children are with me in bed. I cannot rise and give to you.’
8 Ina gaya muku, ko da yake ba zai so ya tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa.
"I tell you that, though he will not rise and give to him because he is his friend, yet because of his importunate persistence he will rise and give him whatever he needs.
9 “Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.
"So I say to you. "Ask, and it shall be given to you; seek, and ye shall find; knock and it shall be opened to you.
10 Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa.
"For he that asks receives, and he who seeks finds, and to him who knocks the door shall be opened.
11 “Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon,
"What father is there among you who, if his son asks for a loaf, will give him a stone? Or if he asks for a fish will give him instead a serpent?
12 ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama?
"Or if he asks for an egg, will offer him a scorpion?
13 In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba’ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”
"If you give good gifts to your children, how much more shall the Father who is in heaven give the Holy spirit to those that ask him!"
14 Sa’ad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.
Once he was casting out a dumb demon, and when the demon was gone out, the dumb man spoke, and the people wondered.
15 Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Be’elzebub, sarkin aljanu ne, yake fitar da aljanu.”
But some of them said, "It is by Beelzebub, the prince of demons, that he cast out demons."
16 Waɗansu kuma suka gwada shi, ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama.
Others, tempting him, kept seeking from him a sign from heaven.
17 Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe.
He knew their intentions and said to them. "Every kingdom divided against itself is laid waste and house falls upon house.
18 In Shaiɗan yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai tsaya? Ina faɗin haka domin kun ce, da ikon Be’elzebub nake fitar da aljanu.
"And if Satan also is divided against himself, how shall his kingdom stand?
19 In da ikon Be’elzebub nake fitar da su, to, da ikon wa masu binku suke fitar da su? Saboda haka, za su zama alƙalanku ke nan.
"Do you say that I am casting out demons by the power of Beelzebub? If I then am casting out demons by Beelzebub, by whom are your sons casting them out? They therefore shall be your judges.
20 Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.
"But if it is by the finger of God that I am casting out demons, then the kingdom of God is come upon you.
21 “Sa’ad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan.
"When the strong man fully aroused keeps guard over his homestead, his property is undisturbed;
22 Amma in wani wanda ya fi shi ƙarfi, ya faɗa masa ya kuma sha ƙarfinsa, yakan ƙwace makaman da mutumin ke dogara da su, ya kuma rarraba ganima.
"but when the stronger man attacks him, he takes away from the strong armor in which he was trusting and divides up the spoil.
23 “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi.
"He who is not for me is against me, and he who is not gathering with me is scattering.
24 “Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’
"Whenever a foul spirit is gone out of a man, it roams through waterless places, in search of rest; but when it can find none, it says, ‘I will go back to the house which I have left.’
25 Sa’ad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye.
When it comes and finds the house completely swept and garnished.
26 Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.”
"Then it goes off and fetches seven other spirits more wicked than itself, and they go in and live there. And the last state of that man is worse than the first."
27 Da Yesu yake cikin faɗin waɗannan abubuwa, sai wata mace daga cikin taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Mai albarka ce uwar da ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”
It happened while he was saying this, that a certain woman out of the crowd shouted to him, saying, "Blessed is the womb that bore you, and the breast that you have sucked."
28 Yesu ya amsa ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”
"No, rather," he answered, "blessed are those who listen to the word of God, and keep it."
29 Da taron mutane suka ƙaru, sai Yesu ya ce, “Wannan mugun zamani ne. Tana neman wani abin banmamaki, amma ba ko ɗaya da za a ba ta, sai dai ta Yunana.
When the crowd were beginning to throng about him he proceeded to say. "This is an evil generation! It seeks a sign, and there shall be no sign be given to it except the sign of Jonah;
30 Kamar yadda Yunana ya zama alama ga mutanen Ninebe, haka ma Ɗan Mutum zai zama ga zamanin nan.
"for as Jonah became a sign to the Ninevites, so shall the Son of man be to this generation.
31 A ranar shari’a, Sarauniyar Kudu za tă tashi tsaye tare da wannan zamani, ta yanke wa wannan zamani hukunci, domin ta zo daga ƙarshen duniya ta saurari hikimar Solomon, ga shi kuwa, shi wanda ya fi Solomon girma, na nan.
"The queen of the South shall rise up in Judgement with the men of this generation, and shall condemn them; because she came from the ends of the earth to listen to the wisdom of Solomon, and lo, one greater than Solomon is here!
32 A ranar shari’a, mutanen Ninebe za su tashi tsaye tare da wannan zamani, su yanke wa wannan zamani hukunci. Gama sun tuba sa’ad da Yunana ya yi musu wa’azi. Ga shi yanzu, shi wanda ya fi Yunana girma, na nan.
"The men of the Nineveh shall stand up in the judgment with his generation and shall condemn it, for they repented at the preaching of Jonah, and lo! one greater than Jonah is here!
33 “Babu wanda yakan ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta, ko ya rufe ta da murfi ba. A maimako, yakan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, don masu shiga su ga haske.
"When one lights a lamp he does not put it in a cellar nor under the bushel, but on a lamp-stand that those who enter may see the light.
34 Idonka shi ne fitilar jikinka. Sa’ad da idanunka suna da lafiya, dukan jikinka ma na cike da haske, amma sa’ad da idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma na cike da duhu.
"The lamp of the body is your eye; when your eye is single then your whole body is full of light; but when it is evil your whole body is full of darkness.
35 Ka lura fa, kada hasken da yake cikinka ya zamana duhu ne.
"Look carefully! Perhaps that very light of yours is darkness.
36 Saboda haka, in dukan jikinka yana cike da haske, ba inda ke da duhu, jikinka kuwa zai kasance da haske gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake haskaka ka.”
"If, however, your whole body is full of light, without having any part dark, it will be wholly radiant with light, as when the lamp illumines you with its bright rays."
37 Da Yesu ya gama magana, sai wani Bafarisiye ya gayyace shi cin abinci tare da shi. Sai kuwa ya shiga ya zauna a tebur.
When he had finished speaking a Pharisee asked him to dine with him; so he went in with him and reclined.
38 Amma Bafarisiyen ya lura cewa, Yesu bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba, sai mamaki ya kama shi.
And the Pharisee noticed, to his amazement, that he did not wash his hands before eating,
39 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta.
but the Lord said to him. "You Pharisee do cleanse the outside of your cup or plate, but your secret heart is full of extortion and wickedness.
40 Ku wawayen mutane! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ne kuma ya yi cikin ba?
"Foolish men! Did not He who made the outside make the inside also?
41 Ku ba matalauta abin da yake cikin kwano, kuma kome zai zama muku da tsabta.
"Better cleanse what is within, and nothing will be unclean for you.
42 “Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na na’ana’arku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.
"But woe unto you Pharisee! for you tithe mint and rue and every herb, and disregard justice and the love of God; but these you ought to have done, and not leave the other undone.
43 “Kaitonku, Farisiyawa, domin kun cika son wuraren zama masu daraja a majami’u, da kuma yawan gaisuwa a wuraren kasuwanci.
"Woe unto you Pharisee! for you delight in the best seats in the synagogue, and in the salutation in the market-places.
44 “Kaitonku, domin ku kamar kaburbura ne da ba a sa musu alama ba, waɗanda mutane suke takawa don rashin sani.”
"Woe unto you! for you are like the tombs which are hidden, and men walk over them unsuspecting."
45 Sai ɗaya daga cikin masanan dokoki ya ce wa Yesu, “Malam, in ka faɗi waɗannan abubuwa haka, kai kuma ka zage mu ke nan.”
Hereupon one of the lawyers exclaimed, "But teacher, in saying such things you are also reproaching us also."
46 Yesu ya amsa ya ce, “Ku masanan dokoki ma, kaitonku, domin kun ɗora wa mutane kaya masu nauyi waɗanda da ƙyar suke ɗaukawa, amma ku da kanku ba za ku sa ko yatsa ɗaya, don ku taimake su ba.
"Woe unto you lawyers also!" said Jesus, "for you load men with irksome burdens, and you yourselves will not touch the burdens with one of your fingers.
47 “Kaitonku, domin kun gina kaburbura saboda annabawa, nan kuwa kakannin-kakanninku ne suka kashe su.
"Woe to you! for you are building the tombs of the prophets whom you ancestors killed.
48 Wannan ya shaida cewa kun amince da abin da kakannin-kakanninku suka yi. Sun karkashe annabawa, ku kuma kun gina kaburburansu.
"So you are witnesses, and you consent to the actions of your ancestors. for they killed them, and you build their tombs.
49 Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’
"For this reason also said the Wisdom of God. ‘I will send them prophets and apostles; some of them they will kill and some they will persecute;
50 Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani,
"so that the blood of all the prophets which was shed from the foundation of the world may be required from this generation,
51 wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani.
"from the blood of Abel to the blood of Zachariah, who perished between the alter and the sanctuary; yes; I tell you, it shall be required of this generation!
52 “Kaitonku, masanan dokoki, domin kun ɗauke mabuɗin ilimi. Ku kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana wa waɗanda suke shiga, su shiga.”
"Woe to you lawyers, for you have taken away the key of knowledge!’ You yourselves have not entered, and you have hindered those who are trying to enter."
53 Da Yesu ya bar wurin, sai Farisiyawa da malaman dokoki suka fara gaba mai tsanani da shi, kuma suna tsokanansa da tambayoyi.
After he had gone away, the Scribes and the Pharisee began to set themselves vehemently against him, and to cross-question him upon many points,
54 Suna fakonsa, don su kama shi a kan wata magana da zai faɗa.
laying in wait for him, in order to catch a word from his lips.

< Luka 11 >