< Firistoci 8 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
Yahweh spoke to Moses, saying,
2 “Kawo Haruna da’ya’yansa maza, ka ɗauki rigunansu, man keɓewa, bijimi domin hadaya don zunubi,’yan raguna biyu da kuma kwandon da yake da burodi marar yisti,
“Take Aaron and his sons with him, and the garments, and the anointing oil, and the bull of the sin offering, and the two rams, and the basket of unleavened bread;
3 ka kuma tara dukan jama’a a ƙofar Tentin Sujada.”
and assemble all the congregation at the door of the Tent of Meeting.”
4 Sai Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi, jama’a kuwa suka taru a ƙofar Tentin Sujada.
Moses did as Yahweh commanded him; and the congregation was assembled at the door of the Tent of Meeting.
5 Sai Musa ya ce wa jama’ar, “Ga abin da Ubangiji ya umarta a yi.”
Moses said to the congregation, “This is the thing which Yahweh has commanded to be done.”
6 Sa’an nan Musa ya kawo Haruna da’ya’yansa maza gaba, ya kuma wanke su da ruwa.
Moses brought Aaron and his sons, and washed them with water.
7 Ya sa wa Haruna taguwa, ya ɗaura igiya kewaye da shi, ya sa masa riga, ya sa masa efod. Ya kuma ɗaura masa efod wanda aka yi masa saƙar gwaninta.
He put the tunic on him, tied the sash on him, clothed him with the robe, put the ephod on him, and he tied the skillfully woven band of the ephod on him and fastened it to him with it.
8 Ya sa masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirjin.
He placed the breastplate on him. He put the Urim and Thummim in the breastplate.
9 Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
He set the turban on his head. He set the golden plate, the holy crown, on the front of the turban, as Yahweh commanded Moses.
10 Sa’an nan Musa ya ɗauki man keɓewa ya keɓe tabanakul da kuma kowane abin da yake cikinsa, ta haka ya tsarkake su.
Moses took the anointing oil, and anointed the tabernacle and all that was in it, and sanctified them.
11 Ya yayyafa mai a kan bagade sau bakwai, yana keɓe bagade da dukan kayayyaki, da daro, da abin da yake tsaya a kai, don yă tsarkake su.
He sprinkled it on the altar seven times, and anointed the altar and all its vessels, and the basin and its base, to sanctify them.
12 Ya zuba man keɓewa a kan Haruna, ya kuma keɓe shi don yă tsarkake shi.
He poured some of the anointing oil on Aaron’s head, and anointed him, to sanctify him.
13 Sa’an nan ya kawo’ya’yan Haruna maza, ya sa musu taguwoyi, ya ɗaɗɗaura igiyoyi kewaye da su, ya kuma sa musu huluna yadda Ubangiji ya umarce shi.
Moses brought Aaron’s sons, and clothed them with tunics, and tied sashes on them, and put headbands on them, as Yahweh commanded Moses.
14 Sa’an nan ya miƙa bijimi domin hadaya don zunubi, sai Haruna da’ya’yansa suka ɗibiya hannuwansu a bijimin.
He brought the bull of the sin offering, and Aaron and his sons laid their hands on the head of the bull of the sin offering.
15 Musa ya yanka bijimin ya ɗauki jinin, ya sa yatsarsa ya zuba a dukan ƙahonin bagade don yă tsarkake bagaden. Ya zuba sauran jinin a gindin bagade. Ta haka ya tsarkake shi don yă yi kafara dominsa.
He killed it; and Moses took the blood, and put it around on the horns of the altar with his finger, and purified the altar, and poured out the blood at the base of the altar, and sanctified it, to make atonement for it.
16 Musa ya ɗebo dukan kitsen da yake kewaye da kayan ciki, da kuma wanda ya rufe hanta, da ƙodojin, da kuma kitsensu, ya kuma ƙone su a kan bagade.
He took all the fat that was on the innards, and the cover of the liver, and the two kidneys, and their fat; and Moses burned it on the altar.
17 Amma bijimin da fatarsa da namansa da kuma ƙashinsa ya ƙone su a bayan sansani, yadda Ubangiji ya umarce shi.
But the bull, and its skin, and its meat, and its dung, he burned with fire outside the camp, as Yahweh commanded Moses.
18 Sa’an nan ya miƙa ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, sai Haruna da’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan rago.
He presented the ram of the burnt offering. Aaron and his sons laid their hands on the head of the ram.
19 Sa’an nan Musa ya yanka ɗan ragon, ya kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagaden.
He killed it; and Moses sprinkled the blood around on the altar.
20 Ya yanka ragon gunduwa-gunduwa ya ƙone kan, ya kuma ƙone gunduwa-gunduwan da kitsen.
He cut the ram into its pieces; and Moses burned the head, and the pieces, and the fat.
21 Ya wanke kayan cikin da ƙafafun a ruwa, ya kuma ƙone dukan ragon a bisa bagade kamar hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
He washed the innards and the legs with water; and Moses burned the whole ram on the altar. It was a burnt offering for a pleasant aroma. It was an offering made by fire to Yahweh, as Yahweh commanded Moses.
22 Sai ya miƙa ɗayan ɗan ragon, ɗan ragon naɗin, sai Haruna da’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan ragon.
He presented the other ram, the ram of consecration. Aaron and his sons laid their hands on the head of the ram.
23 Musa kuwa ya yanka ɗan ragon ya ɗibi jinin ya sa leɓatun kunnen dama na Haruna, ya kuma sa a babbar yatsarsa ta hannun dama da kuma a babbar yatsar ƙafarsa ta dama.
He killed it; and Moses took some of its blood, and put it on the tip of Aaron’s right ear, and on the thumb of his right hand, and on the great toe of his right foot.
24 Musa ya kuma kawo’ya’yan Haruna gaba, ya sa jini a leɓatun kunnuwansu na dama, ya kuma sa a manyan yatsotsinsu na hannun dama da kuma a manyan yatsotsinsu na ƙafafunsu na dama. Sa’an nan ya yayyafa jinin a kowane gefen bagade.
He brought Aaron’s sons; and Moses put some of the blood on the tip of their right ear, and on the thumb of their right hand, and on the great toe of their right foot; and Moses sprinkled the blood around on the altar.
25 Ya ɗibi kitsen, da wutsiya mai kitse, da kuma dukan kitsen da ke kewaye da kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, ƙodoji biyu da kitsensu da kuma cinya ta dama.
He took the fat, the fat tail, all the fat that was on the innards, the cover of the liver, the two kidneys and their fat, and the right thigh;
26 Sa’an nan daga cikin kwandon burodi marar yisti wanda yake a gaban Ubangiji, ya ɗauko dunƙulen burodi, da kuma guda da aka yi da mai, da kuma ƙosai; ya sa waɗannan a sassan kitsen, da kuma a cinya ta dama.
and out of the basket of unleavened bread that was before Yahweh, he took one unleavened cake, one cake of oiled bread, and one wafer, and placed them on the fat and on the right thigh.
27 Ya sa waɗannan a hannuwan Haruna da’ya’yansa, suka kuma kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.
He put all these in Aaron’s hands and in his sons’ hands, and waved them for a wave offering before Yahweh.
28 Sa’an nan Musa ya karɓe su daga hannuwansu ya ƙone a bagade a bisa hadaya ta ƙonawa a matsayin hadaya ta naɗi, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
Moses took them from their hands, and burned them on the altar on the burnt offering. They were a consecration offering for a pleasant aroma. It was an offering made by fire to Yahweh.
29 Ya kuma ɗauki ƙirjin; rabon Musa na ɗan ragon naɗi, ya kaɗa shi a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Moses took the breast, and waved it for a wave offering before Yahweh. It was Moses’ portion of the ram of consecration, as Yahweh commanded Moses.
30 Sai Musa ya ɗibi man keɓewa da jini daga bagade, ya yayyafa su a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan’ya’yansa da rigunansu, don yă tsarkake Haruna da rigunansa da kuma’ya’yansa da rigunansu.
Moses took some of the anointing oil, and some of the blood which was on the altar, and sprinkled it on Aaron, on his garments, and on his sons, and on his sons’ garments with him, and sanctified Aaron, his garments, and his sons, and his sons’ garments with him.
31 Sai Musa ya ce wa Haruna da’ya’yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar Tentin Sujada, ku kuma ci shi a can tare da burodi daga kwandon naɗi, yadda na umarta, cewa, ‘Haruna da’ya’yansa maza za su ci shi.’
Moses said to Aaron and to his sons, “Boil the meat at the door of the Tent of Meeting, and there eat it and the bread that is in the basket of consecration, as I commanded, saying, ‘Aaron and his sons shall eat it.’
32 Sa’an nan ku ƙone sauran naman da kuma burodin.
What remains of the meat and of the bread you shall burn with fire.
33 Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada har kwana bakwai, sai ranakun naɗi suka cika, gama naɗinku zai ɗauki kwana bakwai.
You shall not go out from the door of the Tent of Meeting for seven days, until the days of your consecration are fulfilled: for he shall consecrate you seven days.
34 Abin da aka yi a yau umarni ne daga Ubangiji don yin kafara saboda ku.
What has been done today, so Yahweh has commanded to do, to make atonement for you.
35 Dole ku kasance a ƙofar Tentin Sujada dare da rana har kwana bakwai, ku kuma yi abin da Ubangiji yake bukata, don kada ku mutu; gama abin da aka umarce ni ke nan.”
You shall stay at the door of the Tent of Meeting day and night seven days, and keep Yahweh’s command, that you don’t die: for so I am commanded.”
36 Saboda haka Haruna da’ya’yansa maza suka yi kome da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.
Aaron and his sons did all the things which Yahweh commanded by Moses.

< Firistoci 8 >