< Firistoci 27 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
Yahweh spoke to Moses, saying,
2 “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Duk sa’ad da mutum ya yi rantsuwa ta musamman zai keɓe wani ga Ubangiji, ta wurin biyan kuɗaɗen fansa,
“Speak to the children of Israel, and say to them, ‘When a man consecrates a person to Yahweh in a vow, according to your valuation,
3 ga yadda ma’aunin biyan zai kasance, mutum mai shekara tsakanin ashirin da sittin, za a biya azurfa hamsin.
your valuation of a male from twenty years old to sixty years old shall be fifty shekels of silver, according to the shekel of the sanctuary.
4 Mace kuma za a biya azurfa talatin.
If she is a female, then your valuation shall be thirty shekels.
5 Saurayi mai shekara tsakanin biyar da ashirin, za a biya azurfa ashirin, yarinya kuma azurfa goma.
If the person is from five years old to twenty years old, then your valuation shall be for a male twenty shekels, and for a female ten shekels.
6 Yaro mai shekara tsakanin wata ɗaya da shekara biyar, za a biya azurfa biyar,’yar yarinya kuma azurfa uku.
If the person is from a month old to five years old, then your valuation shall be for a male five shekels of silver, and for a female your valuation shall be three shekels of silver.
7 Namijin da ya fi shekara sittin, za a biya azurfa goma sha biyar, mace kuma azurfa goma.
If the person is from sixty years old and upward; if he is a male, then your valuation shall be fifteen shekels, and for a female ten shekels.
8 In mai alkawarin matalauci ne da ba zai iya biyan ƙayyadadden abin da aka tsara ba, sai yă tafi wurin firist, shi firist kuma yă duba yadda mutumin da ya yi alkawarin zai iya biya. Sa’an nan mutumin zai biya abin da firist ya faɗa.
But if he is poorer than your valuation, then he shall be set before the priest, and the priest shall assign a value to him. The priest shall assign a value according to his ability to pay.
9 “‘In abin da ya yi alkawarin yardajje ne a matsayin hadaya ga Ubangiji, wannan dabbar da aka bayar ga Ubangiji, za tă zama mai tsarki.
“‘If it is an animal of which men offer an offering to Yahweh, all that any man gives of such to Yahweh becomes holy.
10 Kada yă yi musayarta ko yă yi musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau; in lalle ne yă yi musayar dabbar da wata, to, duk wannan da kuma wanda zai yi musayar da ita za su zama masu tsarki.
He shall not alter it, nor exchange it, a good for a bad, or a bad for a good. If he shall at all exchange animal for animal, then both it and that for which it is exchanged shall be holy.
11 In abin da ya yi alkawari dabba ce marar tsarki, wadda ba yardajje ba ce, a matsayin hadaya ga Ubangiji, dole a kai dabbar wa firist,
If it is any unclean animal, of which they do not offer as an offering to Yahweh, then he shall set the animal before the priest;
12 wanda zai yanke hukunci dacewarta, ko mai kyau ce, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.
and the priest shall evaluate it, whether it is good or bad. As the priest evaluates it, so it shall be.
13 In mai shi yana so yă fanshi dabbar, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta.
But if he will indeed redeem it, then he shall add the fifth part of it to its valuation.
14 “‘In mutum ya miƙa gidansa a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji, firist zai daidaita dacewar ko mai kyau ne, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.
“‘When a man dedicates his house to be holy to Yahweh, then the priest shall evaluate it, whether it is good or bad. As the priest evaluates it, so it shall stand.
15 In mutumin da ya keɓe gidansa ya fanshe shi, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar, gidan kuma zai zama nasa.
If he who dedicates it will redeem his house, then he shall add the fifth part of the money of your valuation to it, and it shall be his.
16 “‘In wani ya keɓe wa Ubangiji wani sashe daga cikin gonarsa ta gādo, sai yă kimanta kuɗin gonar daidai da yawan irin da za a iya shuka a gonar. Za a kimanta kuɗin a kan shekel hamsin na irin sha’ir.
“‘If a man dedicates to Yahweh part of the field of his possession, then your valuation shall be according to the seed for it. The sowing of a homer of barley shall be valued at fifty shekels of silver.
17 In ya keɓe gonarsa a Shekara ta Murna, darajar da aka kimanta za tă zauna.
If he dedicates his field from the Year of Jubilee, according to your valuation it shall stand.
18 Amma in ya keɓe gonar bayan Shekara ta Murnan, firist zai kimanta darajar bisa ga yawan shekarun da suka rage har zuwa Shekara ta Murna mai zuwa, sai a rage darajar da aka kimanta a kanta.
But if he dedicates his field after the Jubilee, then the priest shall reckon to him the money according to the years that remain to the Year of Jubilee; and an abatement shall be made from your valuation.
19 In mutumin da ya keɓe gonar, yana so yă fanshe ta, to, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta, gonar kuwa tă zama nasa.
If he who dedicated the field will indeed redeem it, then he shall add the fifth part of the money of your valuation to it, and it shall remain his.
20 In kuma bai fanshe gonar ba, ko kuwa in ya sayar wa wani dabam, ba za a taɓa fanshe ta ba.
If he will not redeem the field, or if he has sold the field to another man, it shall not be redeemed any more;
21 Sa’ad da aka saki gonar a Shekara ta Murna, za tă zama mai tsarki, a matsayin gonar da aka miƙa ga Ubangiji, za tă zama mallakar firistoci.
but the field, when it goes out in the Jubilee, shall be holy to Yahweh, as a devoted field. It shall be owned by the priests.
22 “‘In mutum ya keɓe gonar da ya saya, wadda take ba sashe na gonar iyali ba, ga Ubangiji,
“‘If he dedicates a field to Yahweh which he has bought, which is not of the field of his possession,
23 firist zai kimanta darajarta har Shekara ta Murna, dole kuma mutumin yă biya darajarta a ranar, a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji.
then the priest shall reckon to him the worth of your valuation up to the Year of Jubilee; and he shall give your valuation on that day, as a holy thing to Yahweh.
24 A Shekara ta Murna ɗin, gonar za tă dawo ga mutumin da aka saye ta daga wurinsa, wanda yake mai gonar.
In the Year of Jubilee the field shall return to him from whom it was bought, even to him to whom the possession of the land belongs.
25 A kimanta kowace daraja bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, gera ashirin ga shekel.
All your valuations shall be according to the shekel of the sanctuary: twenty gerahs to the shekel.
26 “‘Ba wani da zai iya keɓe ɗan farin dabba, da yake ɗan fari ya riga ya zama na Ubangiji, ko na saniya, ko na tunkiya, na Ubangiji ne.
“‘However the firstborn among animals, which belongs to Yahweh as a firstborn, no man may dedicate, whether an ox or a sheep. It is Yahweh’s.
27 In tana cikin dabbobin da suke marasa tsarki, zai iya saye ta a darajar da aka kimanta, yă ƙara da kashi ɗaya bisa biyar na darajarta. In bai fanshe ta ba, sai a sayar da ita a darajar da aka kimanta.
If it is an unclean animal, then he shall buy it back according to your valuation, and shall add to it the fifth part of it; or if it isn’t redeemed, then it shall be sold according to your valuation.
28 “‘Amma babu abin da mutum ya mallaka, ya kuma keɓe ga Ubangiji, ko mutum ne, ko dabba, ko ganar iyali da za a sayar, ko a fansa; kome da aka keɓe a wannan hanya, mafi tsarki ne ga Ubangiji.
“‘Notwithstanding, no devoted thing that a man devotes to Yahweh of all that he has, whether of man or animal, or of the field of his possession, shall be sold or redeemed. Everything that is permanently devoted is most holy to Yahweh.
29 “‘Babu wani da aka keɓe don hallaka da za a fansa; dole a kashe shi.
“‘No one devoted to destruction, who shall be devoted from among men, shall be ransomed. He shall surely be put to death.
30 “‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji.
“‘All the tithe of the land, whether of the seed of the land or of the fruit of the trees, is Yahweh’s. It is holy to Yahweh.
31 In mutum ya fanshi wani zakansa, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar.
If a man redeems anything of his tithe, he shall add a fifth part to it.
32 Ushirin gaba ɗaya na garken shanu, da na tumaki, kowane kashi ɗaya bisa goma na dabbar da ta wuce ƙarƙashin sandan mai kiwo, za tă zama mai tsarki ga Ubangiji.
All the tithe of the herds or the flocks, whatever passes under the rod, the tenth shall be holy to Yahweh.
33 Kada kuwa ya zaɓa mai kyau daga marar kyau, ko yă yi musaya. In ya yi musaya kuwa, dabbar da wadda ya musayar, za su zama masu tsarki, ba kuma za a fanshe su ba.’”
He shall not examine whether it is good or bad, neither shall he exchange it. If he exchanges it at all, then both it and that for which it is exchanged shall be holy. It shall not be redeemed.’”
34 Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai saboda Isra’ilawa.
These are the commandments which Yahweh commanded Moses for the children of Israel on Mount Sinai.

< Firistoci 27 >