< Mahukunta 2 >

1 Mala’ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim ya ce, “Na hauro da ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba wa kakanninku. Na ce, ‘Ba zan taɓa tā da yarjejjeniyata da ku ba,
And an angel of the LORD came up from Gilgal to Bochim, and said, I made you to depart from Egypt, and have brought you to the land which I swore to your fathers; and I said, I will never break my covenant with you.
2 ku kuma kada ku shiga wata yarjejjeniya da mazaunan ƙasan nan, sai dai za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya mini ba. Me ya sa kuka yi haka?
And ye shall make no league with the inhabitants of this land; ye shall throw down their altars: but ye have not obeyed my voice: why have ye done this?
3 Saboda haka ina gaya muku cewa ba zan kore su a gabanku ba; za su zama muku ƙaya, gumakansu kuma za su zama muku tarko.”
Therefore I also said, I will not drive them out from before you; but they shall be as thorns in your sides, and their gods shall be a snare to you.
4 Da mala’ikan Ubangiji ya faɗa wa dukan Isra’ilawa waɗannan abubuwa, sai mutane suka yi kuka mai zafi,
And it came to pass, when the angel of the LORD spoke these words to all the children of Israel, that the people lifted up their voice, and wept.
5 sai suka sa wa wannan wuri suna, Bokim. A nan suka miƙa hadaya a gaban Ubangiji.
And they called the name of that place Bochim: and they sacrificed there to the LORD.
6 Bayan Yoshuwa ya sallami Isra’ilawa, sai suka tafi don su mallaki ƙasar, kowa da nasa gādon.
And when Joshua had let the people go, the children of Israel went every man to his inheritance to possess the land.
7 Mutane suka bauta wa Ubangiji duk tsawon kwanakin Yoshuwa da na dattawan da suka rayu bayansa waɗanda suka ga manyan abubuwan da Ubangiji ya yi wa Isra’ila.
And the people served the LORD all the days of Joshua, and all the days of the elders that outlived Joshua, who had seen all the great works of the LORD, that he did for Israel.
8 Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekara ɗari da goma.
And Joshua the son of Nun, the servant of the LORD, died, being an hundred and ten years old.
9 Aka binne shi a ƙasar gādonsa, a Timnat Heres a ƙasar tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash.
And they buried him in the border of his inheritance in Timnathheres, in the mount of Ephraim, on the north side of the hill Gaash.
10 Bayan tsaran nan duka suka rasu, sai wata tsara ta taso wadda ba tă san Ubangiji ko abin da ya yi wa Isra’ila ba.
And also all that generation were gathered to their fathers: and there arose another generation after them, which knew not the LORD, nor yet the works which he had done for Israel.
11 Sai Isra’ilawa suka yi mugaye abubuwa a gaban Ubangiji suka kuma bauta Ba’al.
And the children of Israel did evil in the sight of the LORD, and served Baalim:
12 Suka yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar. Suka bi suka kuma bauta alloli dabam-dabam na mutanen da suke kewaye da su. Suka tsokani Ubangiji ya yi fushi
And they forsook the LORD God of their fathers, who brought them out of the land of Egypt, and followed other gods, of the gods of the people that were around them, and bowed themselves to them, and provoked the LORD to anger.
13 domin sun bar shi suka bauta wa Ba’al da Ashtarot.
And they forsook the LORD, and served Baal and Ashtaroth.
14 Cikin fushinsa a kan Isra’ila Ubangiji ya ba da su ga hannun waɗanda suka kawo musu hari suka washe su. Ya sayar da su ga abokan gābansu da suke kewaye da su, waɗanda ba za su iya yin tsayayya da su ba.
And the anger of the LORD was hot against Israel, and he delivered them into the hands of spoilers that spoiled them, and he sold them into the hands of their enemies around them, so that they could not any longer stand before their enemies.
15 Duk sa’ad da Isra’ila suka fita yaƙi, Ubangiji yakan yi gāba da su don a ci su a yaƙi, kamar dai yadda ya rantse musu. Suka kuwa shiga wahala ƙwarai.
Wherever they went out, the hand of the LORD was against them for evil, as the LORD had said, and as the LORD had sworn to them: and they were greatly distressed.
16 Sa’an nan Ubangiji ya naɗa mahukunta, waɗanda suka cece su daga hannun waɗannan musu hari.
Nevertheless the LORD raised up judges, who delivered them out of the hand of those that spoiled them.
17 Duk da haka ba su saurari mahukuntansu ba amma sai suka shiga ha’inci da waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Ba kamar kakanninsu ba, nan da nan suka kauce daga hanyar da kakanninsu suka bi, hanyar biyayya ga umarnan Ubangiji.
And yet they would not hearken to their judges, but they played the harlot with other gods, and bowed themselves to them: they turned quickly out of the way which their fathers walked in, obeying the commandments of the LORD; but they did not so.
18 Duk sa’ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan kasance tare da mahukuncin, yă kuma cece su daga hannun abokan gāba, muddin mahukuncin yana a raye; gama Ubangiji yakan ji tausayinsu yayinda suke gunaguni ƙarƙashin waɗanda suka danne su suke kuma gasa musu azaba.
And when the LORD raised up judges for them, then the LORD was with the judge, and delivered them out of the hand of their enemies all the days of the judge: for the LORD repented because of their groanings by reason of them that oppressed them and burdened them.
19 Amma sa’ad da mahukuncin ya mutu, mutanen suka koma hanyar da ta fi ta kakanninsu muni, sukan bi waɗansu alloli suna bauta musu. Suka ƙi barin mugun ayyukansu da taurin zuciyarsu.
And it came to pass, when the judge was dead, that they returned, and corrupted themselves more than their fathers, in following other gods to serve them, and to bow down to them; they ceased not from their own doings, nor from their stubborn way.
20 Saboda haka sai Ubangiji ya fusata da Isra’ila ya ce, “Domin wannan al’umma ta tā da yarjejjeniyar da na yi da kakanninsu ba su kuwa saurare ni ba,
And the anger of the LORD was hot against Israel; and he said, Because that this people hath transgressed my covenant which I commanded their fathers, and have not hearkened to my voice;
21 ba zan ƙara kori wata al’ummar da Yoshuwa ya bari sa’ad da ya rasu ba.
I also will not henceforth drive out from before them any of the nations which Joshua left when he died:
22 Zan yi amfani da su in gwada Isra’ila in ga ko za su bi hanyar Ubangiji su kuma yi tafiya a cikinta kamar yadda kakanninsu suka yi.”
That through them I may test Israel, whether they will keep the way of the LORD to walk in it, as their fathers kept it, or not.
23 Ubangiji ya bar waɗannan al’ummai su kasance; bai kore su nan take ta wurin ba da su a hannun Yoshuwa ba.
Therefore the LORD left those nations, without driving them out speedily; neither did he deliver them into the hand of Joshua.

< Mahukunta 2 >