< Ayuba 5 >

1 “Ka yi kira in kana so, amma wa zai amsa maka? Wurin waɗanne tsarkaka za ka juya?
“Call now; is there any who will answer you? To which of the holy ones will you turn?
2 Fushi yana kashe wawa, ƙyashi kuma yana kashe marar azanci.
For resentment kills the foolish man, and jealousy kills the simple.
3 Ni ma na ga wawa yana cin gaba, amma nan da nan gidansa ya zama la’ananne.
I have seen the foolish taking root, but suddenly I cursed his habitation.
4 ’Ya’yansa suna cikin hatsari, ba wanda zai tsaya musu a gaban alƙali,
His children are far from safety. They are crushed in the gate. Neither is there any to deliver them,
5 mayunwata sun kwashe girbinsa, har abubuwan da suke cikin ƙaya, masu jin ƙishirwa kuma suna zuba ido ga dukiyarsa.
whose harvest the hungry eat up, and take it even out of the thorns. The snare gapes for their substance.
6 Gama ba daga cikin ƙasa wahala take fitowa ba, ko kuma bala’i daga ƙasa.
For affliction doesn’t come out of the dust, neither does trouble spring out of the ground;
7 Duk da haka an haifi mutum don wahala ne, kamar yadda ba shakka tartsatsin wuta yake tashi.
but man is born to trouble, as the sparks fly upward.
8 “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata.
“But as for me, I would seek God. I would commit my cause to God,
9 Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa.
who does great things that can’t be fathomed, marvelous things without number;
10 Yana zuba ruwan sama a ƙasa; yana zuba ruwa a gonaki.
who gives rain on the earth, and sends waters on the fields;
11 Yana ɗaukaka masu sauƙinkai, yana kāre waɗanda suke makoki.
so that he sets up on high those who are low, those who mourn are exalted to safety.
12 Yana dagula shirye-shiryen masu wayo don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi.
He frustrates the plans of the crafty, so that their hands can’t perform their enterprise.
13 Yana kama masu wayo cikin wayonsu, yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba.
He takes the wise in their own craftiness; the counsel of the cunning is carried headlong.
14 Da rana sukan yi karo da duhu; da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke.
They meet with darkness in the day time, and grope at noonday as in the night.
15 Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.
But he saves from the sword of their mouth, even the needy from the hand of the mighty.
16 Saboda haka matalauta suna da bege, rashin gaskiya kuma ta yi shiru.
So the poor has hope, and injustice shuts her mouth.
17 “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.
“Behold, happy is the man whom God corrects. Therefore do not despise the chastening of the Almighty.
18 Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.
For he wounds and binds up. He injures and his hands make whole.
19 Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka.
He will deliver you in six troubles; yes, in seven no evil will touch you.
20 Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.
In famine he will redeem you from death; in war, from the power of the sword.
21 Zai kāre ka daga ɓata suna, kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo.
You will be hidden from the scourge of the tongue, neither will you be afraid of destruction when it comes.
22 Za ka yi wa hallaka da yunwa dariya; kuma ba ka bukata ka ji tsoron manyan namun jeji.
You will laugh at destruction and famine, neither will you be afraid of the animals of the earth.
23 Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki, kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai.
For you will be allied with the stones of the field. The animals of the field will be at peace with you.
24 Za ka zauna lafiya a cikin tenti naka, za ka ƙirga kayanka za ka samu kome na nan.
You will know that your tent is in peace. You will visit your fold, and will miss nothing.
25 Za ka san cewa’ya’yanka za su zama da yawa, zuriyarka kuma kamar ciyawa a ƙasa.
You will know also that your offspring will be great, your offspring as the grass of the earth.
26 Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu, kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi.
You will come to your grave in a full age, like a shock of grain comes in its season.
27 “Mun yi nazarin wannan, kuma gaskiya ne. Saboda haka ka ji, ka kuma yi amfani da shi.”
Behold, we have researched it. It is so. Hear it, and know it for your good.”

< Ayuba 5 >