< Ayuba 38 >

1 Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce, 2 “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata da surutan wofi? 3 Ka sha ɗamara kamar namiji; zan yi maka tambaya, za ka kuwa amsa mini. 4 “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya? Gaya mini, in ka sani. 5 Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani! Wane ne ya ja layin aunawa a kanta? 6 A kan me aka kafa tushenta, ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta, 7 yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki. 8 “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki. 9 Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai, 10 sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa. 11 Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya? 12 “Ko ka taɓa ba safiya umarni ko kuma ka sa asuba ta fito, 13 don ta kama gefen duniya ta kakkaɓe mugaye daga cikinta? 14 Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga. 15 An hana mugaye haskensu, hannun da suka ɗaga an karya shi. 16 “Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku, ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku? 17 Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa? Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa? 18 Ko ka gane fāɗin duniya? Gaya mini, in ka san wannan duka. 19 “Ina ne hanyar zuwa gidan haske? Kuma a ina duhu yake zama? 20 Ko za ka iya kai su wurarensu? Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama? 21 Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin! Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa. 22 “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara 23 waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala, domin kwanakin yaƙi da faɗa? 24 Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya, ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya? 25 Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa, da kuma hanyar walƙiyar tsawa 26 don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin jeji inda ba mai zama ciki 27 don a ƙosar da wurin da ya bushe a sa ciyawa ta tsiro a can? 28 Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya zama mahaifin raɓa? 29 Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara? Wane ne ya haifi jaura daga sammai 30 lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse, lokacin da saman ruwa ya daskare? 31 “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo? 32 Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da’ya’yanta zuwa waje? 33 Ka san dokokin sammai? Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya? 34 “Za ka iya tsawata wa gizagizai ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa? 35 Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa? Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’ 36 Wane ne yake cika zuciya da hikima ko kuma yake ba zuciya ganewa? 37 Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai? Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai 38 sa’ad da ƙura ta yi yawa ta daskare a wuri ɗaya? 39 “Za ka iya farauto wa zakanya nama, ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu. 40 Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu, ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu? 41 Wane ne yake ba hankaka abinci lokacin da’ya’yansa suke kuka ga Allah, kuma suna yawo don rashin abinci?

< Ayuba 38 >