< Ayuba 16 >

1 Sai Ayuba ya amsa,
Then Job answered,
2 “Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan; dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!
“I have heard many such things. You are all miserable comforters!
3 Dogayen surutanku ba sa ƙare ne? Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?
Shall vain words have an end? Or what provokes you that you answer?
4 Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi in da kuna cikin halin da nake; zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi, in kaɗa muku kaina.
I also could speak as you do. If your soul were in my soul’s place, I could join words together against you, and shake my head at you,
5 Amma bakina zai ƙarfafa ku; ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku.
but I would strengthen you with my mouth. The solace of my lips would relieve you.
6 “Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi; in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.
“Though I speak, my grief is not subsided. Though I forbear, what am I eased?
7 Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni; ka ɓata gidana gaba ɗaya.
But now, God, you have surely worn me out. You have made all my company desolate.
8 Ka daure ni, ya kuma zama shaida; yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.
You have shriveled me up. This is a witness against me. My leanness rises up against me. It testifies to my face.
9 Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni; ya zura mini ido.
He has torn me in his wrath and persecuted me. He has gnashed on me with his teeth. My adversary sharpens his eyes on me.
10 Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni; suka yi mini ba’a suka haɗu suka tayar mini.
They have gaped on me with their mouth. They have struck me on the cheek reproachfully. They gather themselves together against me.
11 Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefa ni hannun mugaye.
God delivers me to the ungodly, and casts me into the hands of the wicked.
12 Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai; amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya; ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;
I was at ease, and he broke me apart. Yes, he has taken me by the neck, and dashed me to pieces. He has also set me up for his target.
13 maharbansa sun kewaye ni. Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata har jini ya zuba a ƙasa.
His archers surround me. He splits my kidneys apart, and does not spare. He pours out my bile on the ground.
14 Ya ji mini rauni a kai a kai ya auko mini kamar mai yaƙi.
He breaks me with breach on breach. He runs at me like a giant.
15 “Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura.
I have sewed sackcloth on my skin, and have thrust my horn in the dust.
16 Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura;
My face is red with weeping. Deep darkness is on my eyelids,
17 duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba kuma addu’ata mai tsabta ce.
although there is no violence in my hands, and my prayer is pure.
18 “Ya duniya, kada ki ɓoye jinina; bari yă yi kuka a madadina!
“Earth, don’t cover my blood. Let my cry have no place to rest.
19 Ko yanzu haka shaidata tana sama; wanda zai tsaya mini yana sama.
Even now, behold, my witness is in heaven. He who vouches for me is on high.
20 Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne yayinda nake kuka ga Allah;
My friends scoff at me. My eyes pour out tears to God,
21 a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
that he would maintain the right of a man with God, of a son of man with his neighbor!
22 “Shekaru kaɗan suka rage in kama hanyar da ba a komawa.
For when a few years have come, I will go the way of no return.

< Ayuba 16 >