< Ayuba 1 >

1 A ƙasar Uz akwai wani mutum mai suna Ayuba. Mutum ne marar laifi kuma mai adalci; yana tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.
There was a man in the land of Uz whose name was Job; and Job was blameless and upright, one who feared God and turned from evil.
2 Yana da’ya’ya maza bakwai da’yan mata uku,
There were born to him seven sons and three daughters.
3 yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa.
He possessed seven thousand sheep, three thousand camels, five hundred pairs of oxen, and five hundred donkeys and a great many servants. He was the man who was the greatest of all the people of the East.
4 ’Ya’yansa maza sukan yi biki a gidajensu, wannan yă yi yă ba wancan, sai su kira’yan’uwansu mata ukun su ci, su sha tare.
On each son's assigned day, he would give a feast in his house. They would send and call for their three sisters to eat and drink with them.
5 Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi.
When the days of the feast were over, Job would send for them and he would consecrate them. He would rise early in the morning and offer burnt offerings for each of his children, for he would say, “It may be that my children have sinned and cursed God in their hearts.” Job always did this.
6 Wata rana mala’iku suka kawo kansu gaban Ubangiji, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su.
Then it was the day when the sons of God came to present themselves before Yahweh. Satan also came with them.
7 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”
Yahweh said to Satan, “From where have you come?” Then Satan answered Yahweh and said, “From wandering on the earth, from going back and forth on it.”
8 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.”
Yahweh said to Satan, “Have you considered my servant Job? For there is no one like him on the earth, a blameless and upright man, one who fears God and turns from evil.”
9 Sai Shaiɗan ya amsa ya ce, “Haka kawai Ayuba yake tsoron Allah?
Then Satan answered Yahweh and said, “Does Job fear God without reason?
10 Ba ka kāre shi da iyalinsa gaba ɗaya da duk mallakarsa ba? Ka Albarkaci ayyukan hannunsa yadda dabbobinsa duk sun cika ko’ina.
Have you not put a barrier around him, around his house, and around all that is his from every side? You have blessed the deeds of his hands, and his cattle have burst forth in the land.
11 Ka ɗan miƙa hannunka ka raba shi da duk abin da yake da shi, ba shakka zai la’anta ka kana ji, kana gani.”
But now stretch out your hand and touch all that he has, and see if he does not curse you to your face.”
12 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.” Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji.
Yahweh said to Satan, “Behold, all that he has is in your hand. Only against him himself do not stretch out your hand.” Then Satan went away from the presence of Yahweh.
13 Wata rana lokacin da’ya’yan Ayuba suke cikin biki a gidan babban ɗansa,
It came about that on a certain day, his sons and his daughters were eating and drinking wine in their oldest brother's house.
14 sai ɗan aika ya zo wurin Ayuba ya ce masa, “Shanu suna huɗa, jakuna kuma suna kiwo nan kusa,
A messenger came to Job and said, “The oxen were plowing and the donkeys were feeding beside them.
15 sai Sabenawa suka auka musu suka kwashe su suka tafi, suka karkashe masu yi maka aiki duka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
Then the Sabeans fell on them and took them away. As for the servants, they have struck them with the edge of the sword. I alone have escaped to tell you.”
16 Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Wutar Allah ta sauko daga sama ta ƙona dukan tumaki da masu lura da su, wato, bayinka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
While he was still speaking, another also came and said, “The fire of God fell from the heavens and burned up the sheep and the servants. I alone have escaped to tell you.”
17 Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa sun auka wa raƙumanka sun kwashe su duka, suka kuma karkashe masu yi maka aiki, ni kaɗai ne na tsira na zo in gaya maka!”
While he was still speaking, another also came and said, “The Chaldeans formed three groups, attacked the camels, and have taken them away. As for the servants, they have struck them with the edge of the sword. I alone have escaped to tell you.”
18 Yana cikin magana, sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “’Ya’yanka maza da mata suna biki, suna ci suna sha a gidan babban ɗanka,
While he was yet speaking, another also came and said, “Your sons and your daughters were eating and drinking wine in their oldest brother's house.
19 sai wata iska mai ƙarfi daga hamada ta auka ta rushe gidan, gidan kuwa ya fāɗi a kan’ya’yanka ya kashe su, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
A strong wind came from the wilderness and struck the four corners of the house. It fell on the young people, and they died. I alone have escaped to tell you.”
20 Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada
Then Job rose, tore his robe, shaved his head, lay facedown on the ground, and worshiped God.
21 ya ce, “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata, tsirara kuma zan koma. Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa; yabo ya tabbata ga Ubangiji.”
He said, “I was naked when I came out of my mother's womb, and I will be naked when I will return there. It is Yahweh who gave, and it is Yahweh who has taken away. May the name of Yahweh be blessed.”
22 Cikin wannan duka Ayuba bai yi wa Allah zunubi ta wurin ba shi laifi ba.
In all this matter, Job did not sin, nor did he accuse God of wrongdoing.

< Ayuba 1 >