< Irmiya 5 >

1 “Ku yi ta kai da kawowa a titunan Urushalima, ku dudduba ko’ina ku kuma lura, ku bincika cikin dandalinta. Ko za ku sami mutum guda wanda yake aikata adalci wanda yake kuma son bin gaskiya, sai in gafarta wa wannan birni.
“Run back and forth through the streets of Jerusalem, and see now, and know, and seek in its wide places, if you can find a man, if there is anyone who does justly, who seeks truth, then I will pardon her.
2 Ko da yake suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ duk da haka suna rantsuwar ƙarya.”
Though they say, ‘As Yahweh lives,’ surely they swear falsely.”
3 Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya? Ka buge su, amma ba su ji zafi ba; ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara. Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse suka ƙi su tuba.
O Yahweh, don’t your eyes look on truth? You have stricken them, but they were not grieved. You have consumed them, but they have refused to receive correction. They have made their faces harder than a rock. They have refused to return.
4 Na yi tunani, “Waɗannan ne kawai matalauta; su wawaye ne, gama ba su san hanyar Ubangiji ba, ko abubuwan da Allahnsu yake bukata ba.
Then I said, “Surely these are poor. They are foolish; for they don’t know Yahweh’s way, nor the law of their God.
5 Saboda haka zan tafi wurin shugabanni in yi musu magana; tabbatacce sun san hanyar Ubangiji, da abubuwan da Allahnsu yake bukata.” Amma da nufi guda su ma suka karye karkiyar suka tsintsinke sarƙoƙin.
I will go to the great men and will speak to them, for they know the way of Yahweh, and the law of their God.” But these with one accord have broken the yoke, and burst the bonds.
6 Saboda haka zaki daga kurmi zai fāɗa musu, kyarkeci kuma daga hamada zai cinye su, damisa za tă yi musu ƙawanya kusa da garuruwansu yă yayyage duk wanda ya kuskura ya fita, gama tawayensu da girma yake jan bayansu kuma yana da yawa.
Therefore a lion out of the forest will kill them. A wolf of the evenings will destroy them. A leopard will watch against their cities. Everyone who goes out there will be torn in pieces, because their transgressions are many and their backsliding has increased.
7 “Me zai sa in gafarta muku?’Ya’yanku sun yashe ni sun yi rantsuwa da allolin da ba alloli ba ne. Na biya musu dukan bukatunsu, duk da haka suka yi zina suka tattaru a gidajen karuwai.
“How can I pardon you? Your children have forsaken me, and sworn by what are no gods. When I had fed them to the full, they committed adultery, and assembled themselves in troops at the prostitutes’ houses.
8 An ciyar da su sosai, kamar ƙosassun ingarmu, masu jaraba, kowanne yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa.
They were as fed horses roaming at large. Everyone neighed after his neighbor’s wife.
9 Ba zan hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’ummar nan ba?
Shouldn’t I punish them for these things?” says Yahweh. “Shouldn’t my soul be avenged on such a nation as this?
10 “Ku ratsa cikin gonakin inabinta ku cinye su, amma kada ku hallaka su gaba ɗaya. Ku kakkaɓe rassanta, gama waɗannan mutane ba na Ubangiji ba ne.
“Go up on her walls, and destroy, but don’t make a full end. Take away her branches, for they are not Yahweh’s.
11 Gidan Isra’ila da gidan Yahuda sun zama marasa aminci gaba ɗaya gare ni” in ji Ubangiji.
For the house of Israel and the house of Judah have dealt very treacherously against me,” says Yahweh.
12 Sun yi ƙarya a kan Ubangiji; sun ce, “Ba zai yi kome ba! Ba wata masifar da za tă same mu; ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba.
They have denied Yahweh, and said, “It is not he. Evil won’t come on us. We won’t see sword or famine.
13 Annabawa holoƙo ne kawai maganar kuwa ba ta cikinsu; saboda haka bari abin da suke faɗi ya koma kansu.”
The prophets will become wind, and the word is not in them. Thus it will be done to them.”
14 Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Domin mutanen sun yi waɗannan maganganu, zan mai da maganata a bakinku wuta waɗannan mutane kuwa su zama itacen da za tă ci.
Therefore Yahweh, the God of Armies says, “Because you speak this word, behold, I will make my words in your mouth fire, and this people wood, and it will devour them.
15 Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.
Behold, I will bring a nation on you from far away, house of Israel,” says Yahweh. “It is a mighty nation. It is an ancient nation, a nation whose language you don’t know and don’t understand what they say.
16 Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne; dukansu jarumawa ne.
Their quiver is an open tomb. They are all mighty men.
17 Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku, za su cinye’ya’yanku maza da mata; za su cinye garkunan tumakinku da na awakinku, za su cinye’ya’yan inabinku da na ɓaurenku. Da takobi za su hallaka biranenku masu katanga.
They will eat up your harvest and your bread, which your sons and your daughters should eat. They will eat up your flocks and your herds. They will eat up your vines and your fig trees. They will beat down your fortified cities in which you trust with the sword.
18 “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki,” in ji Ubangiji, “ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba.
“But even in those days,” says Yahweh, “I will not make a full end of you.
19 Sa’ad da kuma mutanen suka yi tambaya, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi dukan wannan gare mu?’ Sai ka amsa musu, ‘Yadda kuka yashe ni kuka kuma bauta wa baƙin alloli a ƙasarku, haka yanzu za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’
It will happen when you say, ‘Why has Yahweh our God done all these things to us?’ Then you shall say to them, ‘Just as you have forsaken me and served foreign gods in your land, so you will serve strangers in a land that is not yours.’
20 “Ka sanar da wannan ga gidan Yaƙub ka yi shelarsa a Yahuda.
“Declare this in the house of Jacob, and publish it in Judah, saying,
21 Ku ji wannan, ku wawaye marasa azanci, waɗanda suke da idanu amma ba sa gani, waɗanda suke da kunnuwa amma ba sa ji.
‘Hear this now, foolish people without understanding, who have eyes, and don’t see, who have ears, and don’t hear:
22 Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba? Na sa yashi ya zama iyakar teku, madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba. Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba; za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba.
Don’t you fear me?’ says Yahweh; ‘Won’t you tremble at my presence, who have placed the sand for the bound of the sea by a perpetual decree, that it can’t pass it? Though its waves toss themselves, yet they can’t prevail. Though they roar, they still can’t pass over it.’
23 Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma’yan tawaye ne; sun kauce suka kuma rabu da ni.
“But this people has a revolting and a rebellious heart. They have revolted and gone.
24 Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu, wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara, wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’
They don’t say in their heart, ‘Let’s now fear Yahweh our God, who gives rain, both the former and the latter, in its season, who preserves to us the appointed weeks of the harvest.’
25 Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa; zunubanku sun hana ku samun alheri.
“Your iniquities have turned away these things, and your sins have withheld good from you.
26 “A cikin mutanena an sami mugaye waɗanda suke kwanton ɓauna kamar masu sa tarko wa tsuntsaye kamar waɗanda suke kafa tarko don su kama mutane.
For wicked men are found among my people. They watch, as fowlers lie in wait. They set a trap. They catch men.
27 Kamar keji cike da tsuntsaye, gidajensu sun cika da ruɗu; sun yi arziki suka kuma zama masu iko
As a cage is full of birds, so are their houses full of deceit. Therefore they have become great, and grew rich.
28 suka kuma yi ƙiba, suka yi bul-bul. Mugayen ayyukansu ba su da iyaka; ba sa wa marayu shari’ar adalci, ba sa kāre’yancin matalauta.
They have grown fat. They shine; yes, they excel in deeds of wickedness. They don’t plead the cause, the cause of the fatherless, that they may prosper; and they don’t defend the rights of the needy.
29 Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’umma kamar wannan ba?
“Shouldn’t I punish for these things?” says Yahweh. “Shouldn’t my soul be avenged on such a nation as this?
30 “Abin banmamaki da bantsoro ya faru a ƙasar.
“An astonishing and horrible thing has happened in the land.
31 Annabawa suna annabcin ƙarya, firistoci suna mulki da ikon kansu, mutanena kuma suna son haka. Amma me za ku yi a ƙarshe?
The prophets prophesy falsely, and the priests rule by their own authority; and my people love to have it so. What will you do in the end of it?

< Irmiya 5 >