< Irmiya 47 >

1 Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza. 2 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa; za su zama kogi mai rigyawa. Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta, garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu. Mutane za su yi kuka; dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa 3 da jin motsin takawar kofatan dawakai, da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba da motsin ƙafafunsu. Ubanni ba za su juye don su taimaki’ya’yansu ba; hannuwansu za su yi laƙwas. 4 Gama rana ta zo da za a hallaka Filistiyawa a kuma datse dukan waɗanda suka ragu waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon. Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa, raguwa daga bakin tekun Kaftor. 5 Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki; Ashkelon zai yi shiru. Ya raguwar da suke zama a fili, har yaushe za ku tsattsage kanku? 6 “Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji sai yaushe za ka huta? Ka koma kubenka; ka huta, ka yi shiru.’ 7 Amma ta yaya zai huta sa’ad da Ubangiji ya umarta, sa’ad da ya umarta shi don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?”

< Irmiya 47 >