< Irmiya 10 >

1 Ku ji abin da Ubangiji yana ce muku, ya gidan Isra’ila.
Hear the word which Yahweh speaks to you, house of Israel!
2 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ku koyi hanyoyin al’ummai ko ku razana game da alamun sararin sama, ko da yake al’ummai sun razana saboda su.
Yahweh says, “Don’t learn the way of the nations, and don’t be dismayed at the signs of the sky; for the nations are dismayed at them.
3 Gama al’adun mutane banza ne; sukan yanke itace daga kurmi, sai mai sassaƙa yă sassaƙa shi da gizago.
For the customs of the peoples are vanity; for one cuts a tree out of the forest, the work of the hands of the workman with the ax.
4 Sukan yi masa ado da azurfa da kuma zinariya; sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi, don kada yă fāɗi.
They deck it with silver and with gold. They fasten it with nails and with hammers, so that it can’t move.
5 Kamar dodon gona cikin gonar kabewa, haka gumakansu ba sa iya magana; dole a yi ta ɗaukansu domin ba za su iya tafiya ba. Kada ku ji tsoronsu; ba za su iya yi wa wani lahani ba ba sa iya yin wani abin kirki.”
They are like a palm tree, of turned work, and don’t speak. They must be carried, because they can’t move. Don’t be afraid of them; for they can’t do evil, neither is it in them to do good.”
6 Babu wani kamar ka, ya Ubangiji; kai mai girma ne, kuma sunanka yana da girma da kuma iko.
There is no one like you, Yahweh. You are great, and your name is great in might.
7 Wane ne ba zai girmama ka ba, Ya Sarkin al’ummai? Tsoronka wajibi ne. A cikin dukan masu hikima na al’ummai kuma cikin dukan mulkokinsu, babu kamar ka.
Who shouldn’t fear you, King of the nations? For it belongs to you. Because among all the wise men of the nations, and in all their royal estate, there is no one like you.
8 Dukansu marasa azanci ne wawaye; gumakan itacen banza ne suke koya musu.
But they are together brutish and foolish, instructed by idols! It is just wood.
9 An kawo ƙeraren azurfa daga Tarshish zinariya kuma daga Ufaz. Abin da gwani da maƙerin zinariya suka yi sa’an nan aka yi masa ado da mulufi da shunayya dukan aikin gwanaye.
There is silver beaten into plates, which is brought from Tarshish, and gold from Uphaz, the work of the engraver and of the hands of the goldsmith. Their clothing is blue and purple. They are all the work of skillful men.
10 Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya; shi ne Allah mai rai, madawwamin sarki. Sa’ad da ya yi fushi, ƙasa takan girgiza; al’ummai ba sa iya jure da hasalarsa.
But Yahweh is the true God. He is the living God, and an everlasting King. At his wrath, the earth trembles. The nations aren’t able to withstand his indignation.
11 “Ka faɗa musu wannan, ‘Waɗannan alloli, waɗanda ba su yi sammai da ƙasa ba, za su hallaka daga duniya da kuma daga ƙarƙashin sammai.’”
“You shall say this to them: ‘The gods that have not made the heavens and the earth will perish from the earth, and from under the heavens.’”
12 Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
God has made the earth by his power. He has established the world by his wisdom, and by his understanding has he stretched out the heavens.
13 Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi; yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya. Yakan aiki walƙiya da ruwan sama ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.
When he utters his voice, the waters in the heavens roar, and he causes the vapors to ascend from the ends of the earth. He makes lightnings for the rain, and brings the wind out of his treasuries.
14 Kowa marar azanci ne, marar ilimi; kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa. Siffofinsa ƙarya ne; ba su da numfashi a cikinsu.
Every man has become brutish and without knowledge. Every goldsmith is disappointed by his engraved image; for his molten image is falsehood, and there is no breath in them.
15 Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne; Sa’ad da hukuncinsu ya yi za su lalace.
They are vanity, a work of delusion. In the time of their visitation they will perish.
16 Shi da yake Rabon Yaƙub ba kamar waɗannan yake ba, gama shi ne Mahaliccin abubuwa duka, har da Isra’ila, kabilar gādonsa Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
The portion of Jacob is not like these; for he is the maker of all things; and Israel is the tribe of his inheritance. Yahweh of Armies is his name.
17 Ku tattara kayayyakinku don ku bar ƙasar, ku da kuke zaune a wurin da aka kewaye da yaƙi.
Gather up your wares out of the land, you who live under siege.
18 Gama haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan lokaci zan jefar da waɗanda suke zaune a ƙasar; zan kawo damuwa a kansu domin a kama su.”
For Yahweh says, “Behold, I will sling out the inhabitants of the land at this time, and will distress them, that they may feel it.”
19 Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini! Raunina ba mai warkewa ba ne! Duk da haka na ce wa kaina, “Wannan ciwona ne, dole kuma in jure da shi.”
Woe is me because of my injury! My wound is serious; but I said, “Truly this is my grief, and I must bear it.”
20 An lalatar da tentina; dukan igiyoyinsa sun tsintsinke.’Ya’yana maza sun bar ni ba sa nan; ba wanda aka bari da zai kafa tentina ko ya kafa mini mafaka.
My tent has been destroyed, and all my cords are broken. My children have gone away from me, and they are no more. There is no one to spread my tent any more, to set up my curtains.
21 Makiyaya marasa azanci ne kuma ba sa neman nufin Ubangiji; saboda haka ba sa nasara dukan garkensu kuwa ya watse.
For the shepherds have become brutish, and have not inquired of Yahweh. Therefore they have not prospered, and all their flocks have scattered.
22 Ku saurara! Rahoto yana zuwa babban hargitsi daga ƙasar arewa! Zai mai da garuruwan Yahuda kufai, mazaunin diloli.
The voice of news, behold, it comes, and a great commotion out of the north country, to make the cities of Judah a desolation, a dwelling place of jackals.
23 Na sani, ya Ubangiji, cewa ran mutum ba nasa ba ne; ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba.
Yahweh, I know that the way of man is not in himself. It is not in man who walks to direct his steps.
24 Ka yi mini gyara, Ubangiji, amma fa da adalci kaɗai ba cikin fushinka ba, don kada ka wofinta ni.
Yahweh, correct me, but gently; not in your anger, lest you reduce me to nothing.
25 Ka zuba hasalarka a kan al’umman da ba su san ka ba, a kan mutanen da ba sa kira bisa sunanka. Gama sun cinye Yaƙub; sun cinye shi gaba ɗaya suka kuma lalace wurin zamansa.
Pour out your wrath on the nations that don’t know you, and on the families that don’t call on your name; for they have devoured Jacob. Yes, they have devoured him, consumed him, and have laid waste his habitation.

< Irmiya 10 >