< Ishaya 27 >

1 A wannan rana, Ubangiji zai yi hukunci da takobi, takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna, zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe, dodon ruwa macijin nan mai murɗewa; zai kashe dodon nan na teku.
In that day, the LORD with his fierce and great and mighty sword will punish leviathan, the fleeing serpent, and leviathan the twisted serpent; and he will kill the serpent that is in the sea.
2 A wannan rana, “Ku rera game da gonar inabi mai ba da’ya’ya ku ce
In that day, sing to her, "A pleasant vineyard.
3 Ni, Ubangiji na lura da ita; na yi ta yin mata banruwa. Na yi tsaronta dare da rana don kada wani yă yi mata ɓarna.
I, the LORD, am its keeper. I will water it every moment. Lest anyone damage it, I will keep it night and day.
4 Ban yi fushi ba. Da a ce ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suke kalubalanta na mana! Zan fita in yi yaƙi da su; da na sa musu wuta duka.
Wrath is not in me, but if I should find briers and thorns, I would do battle. I would march on them and I would burn them together.
5 Ko kuma bari su zo wurina don mafaka; bari su yi sulhu da ni, I, bari su yi sulhu da ni.”
Or else let him take hold of my strength, that he may make peace with me. Let him make peace with me."
6 A kwanaki masu zuwa Yaƙub zai yi saiwa, Isra’ila zai yi toho ya kuma yi fure ya cika dukan duniya da’ya’ya.
In days to come, Jacob will take root. Israel will blossom and bud. They will fill the surface of the world with fruit.
7 Ubangiji ya buge shi kamar yadda ya bugi waɗanda suka buge shi? An kashe shi kamar yadda aka kashe waɗanda suka kashe shi?
Has he struck them as he struck those who struck them? Or have they been killed as their killers were killed?
8 Ta wurin yaƙi da zaman bauta ka hukunta shi, da tsananin tsawa kuma ka kore shi, kamar a ranar da iskar gabas ta hura.
In measure, when you send them away, you contend with them. He has removed them with his rough blast in the day of the east wind.
9 A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub, wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa. Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu, har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare da za a bari a tsaye.
Therefore, by this the iniquity of Jacob will be forgiven, and this is all the fruit of taking away his sin: that he makes all the stones of the altar as chalk stones that are beaten in pieces, so that the Asherim and the incense altars shall rise no more.
10 Birni mai katanga ya zama kufai, yasasshen mazauni, an yashe shi kamar hamada; a can’yan maruƙa suke kiwo, a can suke kwance; sun kakkaɓe rassanta ƙaf.
For the fortified city is solitary, a habitation deserted and forsaken, like the wilderness. The calf will feed there, and there he will lie down, and consume its branches.
11 Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su mata kuma su zo su yi itacen wuta da su. Gama mutane ne marar azanci; saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba, Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba.
When its boughs are withered, they will be broken off. The women will come and set them on fire, for they are a people of no understanding. Therefore he who made them will not have compassion on them, and he who formed them will show them no favor.
12 A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya.
It will happen in that day, that the LORD will thresh from the flowing stream of the Perath to the Wadi of Egypt; and you will be gathered one by one, children of Israel.
13 Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima.
It will happen in that day that a great trumpet will be blown; and those who were ready to perish in the land of Assyria, and those who were outcasts in the land of Egypt, shall come; and they will worship the LORD in the holy mountain at Jerusalem.

< Ishaya 27 >