< Ishaya 25 >

1 Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka, gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki, abubuwan da aka shirya tun da. 2 Ka mai da birnin tsibin tarkace, ka lalatar da gari mai katanga, birnin baƙi mai ƙarfi, ta ɓace; ba za a ƙara gina ta ba. 3 Saboda haka mutane masu ƙarfi za su girmama ka; biranen mugayen al’ummai za su ji tsoronka. 4 Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa, wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana. Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango 5 kuma kamar zafin hamada. Ka kwantar da hayaniyar baƙi; kamar yadda inuwar girgije kan rage zafin rana, haka ake kwantar da waƙar mugaye. 6 A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane, liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau. 7 A wannan dutse zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane, ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai; 8 zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa. 9 A wannan rana za su ce, “Tabbatacce wannan shi ne Allah; mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu. Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi; bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.” 10 Hannun Ubangiji zai zauna a kan wannan dutse; amma za a tattake Mowab a ƙarƙashinsa kamar yadda ake tattaka kara a cikin taki. 11 Za su buɗe hannuwansa a cikinsa, yadda mai iyo kan buɗe hannuwansa don yă yi iyo. Allah ya ƙasƙantar da girmankansu duk da wayon hannuwansu. 12 Zai rurrushe manyan katangar kagaru ya kuma ƙasƙantar da su; zai rushe su har ƙasa, su zama ƙura.

< Ishaya 25 >