< Ishaya 21 >

1 Abin da Allah ya faɗa game da Hamada da take kusa da Teku. Kamar guguwa mai share cikin ƙasar kudu, mai hari ya zo daga hamada, daga ƙasar mai banrazana.
The burden of the desert of the sea. As whirlwinds in the south pass through; [so] it cometh from the desert, from a terrible land.
2 An nuna mini mugun wahayi, mai bashewa ya bashe, mai washewa ya washe. Elam, ki yi yaƙi! Mediya, ki yi kwanto! Zan kawo ƙarshen dukan nishe-nishen da ta jawo.
A grievous vision is declared to me; the treacherous dealer dealeth treacherously, and the spoiler plundereth. Go up, O Elam: besiege, O Media; all her sighing have I made to cease.
3 Game da wannan jikina yana ciwo, zafi ya kama ni, kamar na mace mai naƙuda; na razana game da abin da na ji, na yi mamakin abin da na gani.
Therefore are my loins filled with pain: pangs have taken hold upon me, as the pangs of a woman that travaileth: I was bowed down at the hearing [of it]; I was dismayed at the seeing [of it].
4 Gabana tana ta fāɗuwa, tsoro ya sa ina rawan jiki; hasken da nake marmari ya zo da razana gare ni.
My heart panted, fearfulness affrighted me: the night of my pleasure hath he turned into fear to me.
5 Sun shirya teburori, sun shimfiɗa dardumai, sun ci, sun sha! Tashi, ku hafsoshi, sa mai a garkuwoyi!
Prepare the table, watch in the watch-tower, eat, drink: arise, ye princes, [and] anoint the shield.
6 Ga abin da mai girma ya ce mini, “Tafi, ka sa mai tsaro ka kuma sa ya ba da rahoton abin da ya gani.
For thus hath the LORD said to me, Go, set a watchman, let him declare what he seeth.
7 Sa’ad da ya ga kekunan yaƙi tare da ƙungiyoyin dawakai, mahaya a kan jakuna, ko mahaya a kan raƙuma, to, fa ya zauna a faɗake, ya kintsa sosai.”
And he saw a chariot [with] a couple of horsemen, a chariot of asses, [and] a chariot of camels; and he hearkened diligently with much heed:
8 Mai tsaron kuma ya yi ihu, “Kowace rana, ranka yă daɗe, nakan tsaya a hasumiyar tsaro; kowane dare nakan tsaya a wurin aikina.
And he cried, a lion: My lord, I stand continually upon the watch-tower in the day time, and I am set in my ward whole nights.
9 Duba, ga wani mutum tafe a keken yaƙin tare da ƙungiyar dawakai. Ya kuma mayar da amsa, ‘Babilon ta fāɗi, ta fāɗi! Dukan siffofin allolinta kwance a ragargaje a ƙasa!’”
And behold, here cometh a chariot of men, [with] a couple of horsemen. And he answered and said, Babylon is fallen, is fallen; and all the graven images of her gods he hath broken to the ground.
10 Ya mutanena, an ragargaje ku a masussuka, na faɗa muku abin da na ji daga Ubangiji Maɗaukaki, daga Allah na Isra’ila.
O my threshing, and the corn of my floor; that which I have heard from the LORD of hosts, the God of Israel, have I declared to you.
11 Abin da Allah ya faɗa game da Duma, Wani ya kira ni daga Seyir, “Mai tsaro, me ya rage a daren? Mai tsaro, me ya rage a daren?”
The burden of Dumah. He calleth to me out of Seir, Watchman, what of the night? Watchman, what of the night?
12 Mai tsaro ya amsa, “Safiya ta gabato, haka kuma dare. In za ka yi tambaya, to, yi tambaya; sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”
The watchman said, The morning cometh, and also the night: if ye will inquire, inquire ye: return, come.
13 Abin da Allah ya faɗa game da Arabiya. Ku ayarin Dedanawa, ku da kuka sauka a jejin Arabiya,
The burden upon Arabia. In the forest in Arabia shall ye lodge, O ye traveling companies of Dedanim.
14 ku kawo ruwa don ƙishirwa; ku da kuke zama a Tema, ku kawo abinci don masu gudun hijira.
The inhabitants of the land of Tema brought water to him that was thirsty, they met with their bread him that fled.
15 Sun gudu daga takobi, daga takobin da aka janye, daga bakan da aka tanƙware da kuma daga zafin yaƙi.
For they fled from the swords, from the drawn sword, and from the bent bow, and from the grievousness of war.
16 Ga abin da mai girma ya ce mini, “Cikin shekara ɗaya, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, dukan sojojin Kedar za su zo ga ƙarshe.
For thus hath the LORD said to me, Within a year, according to the years of a hireling, and all the glory of Kedar shall fail:
17 Waɗanda suka yi rai na maharba, jarumawan Kedar, za su zama kaɗan.” Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa.
And the residue of the number of archers, the mighty men of the children of Kedar, shall be diminished: for the LORD God of Israel hath spoken [it].

< Ishaya 21 >