< Hosiya 6 >

1 “Ku zo, mu koma ga Ubangiji. Ya yayyage mu kucu-kucu amma zai warkar da mu; ya ji mana ciwo amma zai daure mana miyakunmu.
“Come! Let’s return to Yahweh; for he has torn us to pieces, and he will heal us; he has injured us, and he will bind up our wounds.
2 Bayan kwana biyu zai rayar da mu, a rana ta uku zai tashe mu, don mu rayu a gabansa.
After two days he will revive us. On the third day he will raise us up, and we will live before him.
3 Bari mu yarda da Ubangiji; bari mu nace gaba don mu yarda da shi. Muddin rana tana fitowa, zai bayyana; zai zo mana kamar ruwan bazara, kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”
Let’s acknowledge Yahweh. Let’s press on to know Yahweh. As surely as the sun rises, Yahweh will appear. He will come to us like the rain, like the spring rain that waters the earth.”
4 “Me zan yi da kai Efraim? Me zan yi da kai Yahuda? Ƙaunarku tana kamar hazon safiya, kamar raɓar safiya da takan ɓace.
“Ephraim, what shall I do to you? Judah, what shall I do to you? For your love is like a morning cloud, and like the dew that disappears early.
5 Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana, na kashe ku da kalmomin bakina; hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku.
Therefore I have cut them to pieces with the prophets; I killed them with the words of my mouth. Your judgments are like a flash of lightning.
6 Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba, ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.
For I desire mercy, and not sacrifice; and the knowledge of God more than burnt offerings.
7 Kamar Adamu, sun tā da alkawari, sun yi mini rashin aminci a can.
But they, like Adam, have broken the covenant. They were unfaithful to me there.
8 Gileyad birni ce ta mugayen mutane, da tabon alamun jini.
Gilead is a city of those who work iniquity; it is stained with blood.
9 Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum, haka ƙungiyoyin firistoci suke; suna kisa a hanya zuwa Shekem, suna aikata laifofi bankunya.
As gangs of robbers wait to ambush a man, so the company of priests murder on the path toward Shechem, committing shameful crimes.
10 Na ga wani abu mai bantsoro a gidan Isra’ila. A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci Isra’ila kuma ta ƙazantu.
In the house of Israel I have seen a horrible thing. There is prostitution in Ephraim. Israel is defiled.
11 “Ku kuma, ya mutanen Yahuda, na shirya muku ranar girbi. “A duk sa’ad da zan mayar da dukiya wa mutanena,
“Also, Judah, there is a harvest appointed for you, when I restore the fortunes of my people.

< Hosiya 6 >