< Farawa 46 >

1 Saboda haka Isra’ila ya kama hanya da dukan abin da yake nasa, sa’ad da ya kai Beyersheba, sai ya miƙa hadayu ga Allah na Ishaku, mahaifinsa.
Israel made his journey with all that he had and went to Beersheba. There he offered sacrifices to the God of his father Isaac.
2 Allah kuwa ya yi magana ga Isra’ila a wahayi da dare ya ce, “Yaƙub! Yaƙub!” Yaƙub kuwa ya amsa ya ce, “Ga ni.”
God spoke to Israel in a vision at night, saying, “Jacob, Jacob.” He said, “Here I am.”
3 Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama zan mai da kai al’umma mai girma a can.
He said, “I am God, the God of your father. Do not fear to go down to Egypt, for there I will make you a great nation.
4 Zan gangara zuwa Masar tare da kai, tabbatacce zan sāke dawo da kai. Kuma hannun Yusuf zai rufe idanunka.”
I will go down with you into Egypt, and I will surely bring you up again and Joseph will close your eyes with his own hand.”
5 Sa’an nan Yaƙub ya bar Beyersheba,’ya’yan Isra’ila maza, suka ɗauki mahaifinsu Yaƙub da’ya’yansu da matansu a cikin wagonun da Fir’auna ya aika don a kawo shi.
Jacob rose up from Beersheba. The sons of Israel transported Jacob their father, their children, and their wives, in the carts that Pharaoh had sent to carry him.
6 Suka kuma ɗauki dabbobinsu da mallakarsu, da suka samu a Kan’ana, Yaƙub kuwa da dukan zuriyarsa suka tafi Masar.
They took their livestock and their possessions that they had accumulated in the land of Canaan. They came into Egypt, Jacob and all his descendants with him.
7 Ya ɗauki’ya’yansa maza da jikokinsa da’ya’yansa mata da jikokinsa mata, dukan zuriyarsa zuwa Masar.
He brought with him to Egypt his sons and his sons' sons, his daughters and his sons' daughters, and all his descendants.
8 Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Isra’ila maza (Yaƙub da zuriyarsa) waɗanda suka tafi Masar, Ruben ɗan farin Yaƙub.
These were the names of the children of Israel who came to Egypt: Jacob and his sons, Reuben, Jacob's firstborn;
9 ’Ya’yan Ruben maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
the sons of Reuben, Hanok, Pallu, Hezron, and Karmi;
10 ’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana.
the sons of Simeon, Jemuel, Jamin, Ohad, Jakin, Zohar, and Shaul, the son of a Canaanite woman;
11 ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.
and the sons of Levi, Gershon, Kohath, and Merari.
12 ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana).’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.
The sons of Judah were Er, Onan, Shelah, Perez, and Zerah, (but Er and Onan had died in the land of Canaan). The sons of Perez were Hezron and Hamul.
13 ’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yoshub da Shimron.
The sons of Issachar were Tola, Puah, Lob, and Shimron;
14 ’Ya’yan Zebulun maza su ne, Sered, Elon da Yaleyel.
The sons of Zebulun were Sered, Elon, and Jahleel
15 Waɗannan su ne’ya’yan Liyatu maza da ta haifa wa Yaƙub a Faddan Aram, ban da’yarsa Dina.’Ya’yansa maza da mata duka, mutum talatin da uku ne.
These were the sons of Leah whom she bore to Jacob in Paddan Aram, along with his daughter Dinah. His sons and his daughters numbered thirty-three.
16 ’Ya’yan Gad maza su ne, Zafon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi da Areli.
The sons of Gad were Zephon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi, and Areli.
17 ’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishbi da Beriya.’Yar’uwarsu ita ce Sera.’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel.
The sons of Asher were Imnah, Ishvah, Ishvi, and Beriah; and Serah was their sister. The sons of Beriah were Heber and Malkiel
18 Waɗannan su ne’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa’yarsa Liyatu.’Ya’yan duka, su sha shida ne.
These were the sons of Zilpah, whom Laban had given to Leah his daughter. These sons she bore to Jacob—sixteen in all.
19 ’Ya’yan Yaƙub maza waɗanda Rahila ta haifa su ne, Yusuf da Benyamin.
The sons of Jacob's wife Rachel were Joseph and Benjamin.
20 A Masar, Asenat’yar Fotifera, firist na On ta haifi Manasse da Efraim wa Yusuf.
In Egypt Manasseh and Ephraim were born to Joseph by Asenath, the daughter of Potiphera priest of On.
21 ’Ya’yan Benyamin maza su ne, Bela, Beker, Ashbel, Gera, Na’aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim da Ard.
The sons of Benjamin were Bela, Beker, Ashbel, Gera, Naaman, Ehi, Rosh, Muppim, Huppim, and Ard.
22 Waɗannan su ne’ya’yan Rahila maza waɗanda ta haifa wa Yaƙub, dukansu mutum goma sha huɗu ne.
These were the sons of Rachel who were born to Jacob—fourteen in all.
23 Yaron Dan shi ne, Hushim.
The son of Dan was Hushim.
24 ’Ya’yan Naftali maza su ne, Yazeyel, Guni, Yezer da Shillem.
The sons of Naphtali were Jahziel, Guni, Jezer, and Shillem.
25 Waɗannan su ne’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa’yarsa Rahila.’Ya’yan suka su bakwai ne.
These were the sons born to Jacob by Bilhah, whom Laban gave to Rachel his daughter—seven in all.
26 Dukan waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub, waɗanda suke zuriyarsa kai tsaye ban da matan’ya’yansa maza, su mutum sittin da shida ne.
All those who went to Egypt with Jacob, who were his descendants, not counting Jacob's sons' wives, were sixty-six in all.
27 In aka haɗa da’ya’yan nan maza guda biyu waɗanda aka haifa wa Yusuf a Masar, membobin iyalin Yaƙub, waɗanda suka tafi Masar, duka su saba’in ne.
With the two sons of Joseph who were born to him in Egypt, the members of his family who went to Egypt were seventy in all.
28 To, Yaƙub ya aiki Yahuda yă yi gaba yă sadu da Yusuf, don yă nuna musu hanyar da za su bi zuwa yankin Goshen. Da suka isa yankin Goshen,
Jacob sent Judah ahead of him to Joseph to show the way before him to Goshen, and they came to the land of Goshen.
29 sai Yusuf ya kintsa keken yaƙinsa ya haura zuwa Goshen don yă taryi mahaifinsa, Isra’ila. Nan da nan da isowar Yusuf a wurin mahaifinsa, sai ya rungumi mahaifinsa, ya yi kuka na dogon lokaci.
Joseph prepared his chariot and went up to meet Israel his father in Goshen. He saw him, hugged his neck, and wept on his neck a long time.
30 Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Yanzu ina a shirye in mutu, da yake na gani da kaina cewa har yanzu kana da rai.”
Israel said to Joseph, “Now let me die, since I have seen your face, that you are still alive.”
31 Sa’an nan Yusuf ya ce wa’yan’uwansa da gidan mahaifinsa, “Zan haura in yi magana da Fir’auna, zan kuwa ce masa, ‘’Yan’uwana da gidan mahaifina, waɗanda suke zaune a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina.
Joseph said to his brothers and to his father's house, “I will go up and tell Pharaoh, saying, 'My brothers and my father's house, who were in the land of Canaan, have come to me.
32 Mutanen fa, makiyaya ne; suna kiwon dabbobi, sun kuma zo tare da garkunansu da shanunsa da kuma kome da suka mallaka.’
The men are shepherds, for they have been keepers of livestock. They have brought their flocks, their herds, and all that they have.'
33 Sa’ad da Fir’auna ya kira ku ciki, ya yi tambaya, ‘Mece ce sana’arku?’
It will come about, when Pharaoh calls you and asks, 'What is your occupation?'
34 Ku amsa, ‘Bayinka suna kiwon dabbobi ne, tun muna samari har zuwa yanzu, kamar yadda kakanninmu suka yi.’ Ta haka za a bar ku ku zauna a yankin Goshen, gama Masarawa suna ƙyamar makiyaya.”
that you should say, 'Your servants have been keepers of livestock from our youth until now, both we, and our forefathers.' Do this so that you may live in the land of Goshen, for every shepherd is an abomination to the Egyptians.”

< Farawa 46 >