< Farawa 40 >

1 Bayan ɗan lokaci, sai mai riƙon kwaf da mai tuyan sarkin Masar suka yi wa maigidansu, sarkin Masar laifi.
ἐγένετο δὲ μετὰ τὰ ῥήματα ταῦτα ἥμαρτεν ὁ ἀρχιοινοχόος τοῦ βασιλέως Αἰγύπτου καὶ ὁ ἀρχισιτοποιὸς τῷ κυρίῳ αὐτῶν βασιλεῖ Αἰγύπτου
2 Fir’auna ya yi fushi da hafsoshin nan nasa guda biyu, shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya,
καὶ ὠργίσθη Φαραω ἐπὶ τοῖς δυσὶν εὐνούχοις αὐτοῦ ἐπὶ τῷ ἀρχιοινοχόῳ καὶ ἐπὶ τῷ ἀρχισιτοποιῷ
3 ya kuma sa su a kurkuku a cikin gidan shugaban masu tsaro, a wannan kurkukun da aka sa Yusuf.
καὶ ἔθετο αὐτοὺς ἐν φυλακῇ παρὰ τῷ δεσμοφύλακι εἰς τὸ δεσμωτήριον εἰς τὸν τόπον οὗ Ιωσηφ ἀπῆκτο ἐκεῖ
4 Sai shugaban masu tsaro ya danƙa su a hannun Yusuf, ya kuwa yi musu hidima. Bayan sun jima cikin kurkuku,
καὶ συνέστησεν ὁ ἀρχιδεσμώτης τῷ Ιωσηφ αὐτούς καὶ παρέστη αὐτοῖς ἦσαν δὲ ἡμέρας ἐν τῇ φυλακῇ
5 sai kowanne a cikin mutum biyun nan, mai riƙon kwaf da mai tuya na sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, suka yi mafarki a dare ɗaya, kuma kowane mafarki ya kasance da fassara irin tasa.
καὶ εἶδον ἀμφότεροι ἐνύπνιον ἑκάτερος ἐνύπνιον ἐν μιᾷ νυκτὶ ὅρασις τοῦ ἐνυπνίου αὐτοῦ ὁ ἀρχιοινοχόος καὶ ὁ ἀρχισιτοποιός οἳ ἦσαν τῷ βασιλεῖ Αἰγύπτου οἱ ὄντες ἐν τῷ δεσμωτηρίῳ
6 Sa’ad da Yusuf ya zo wurinsu kashegari, sai ya ga duk sun damu.
εἰσῆλθεν δὲ πρὸς αὐτοὺς Ιωσηφ τὸ πρωὶ καὶ εἶδεν αὐτούς καὶ ἦσαν τεταραγμένοι
7 Saboda haka ya tambayi hafsoshin Fir’auna, waɗanda suke a kurkuku tare da shi, a gidan maigidansa ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a ɓace haka?”
καὶ ἠρώτα τοὺς εὐνούχους Φαραω οἳ ἦσαν μετ’ αὐτοῦ ἐν τῇ φυλακῇ παρὰ τῷ κυρίῳ αὐτοῦ λέγων τί ὅτι τὰ πρόσωπα ὑμῶν σκυθρωπὰ σήμερον
8 Sai suka amsa, “Mu biyu, mun yi mafarki, amma babu wani da zai fassara mana su.” Sa’an nan Yusuf ya ce musu, “Fassara ba daga Allah take zuwa ba? Ku faɗa mini mafarkanku.”
οἱ δὲ εἶπαν αὐτῷ ἐνύπνιον εἴδομεν καὶ ὁ συγκρίνων οὐκ ἔστιν αὐτό εἶπεν δὲ αὐτοῖς Ιωσηφ οὐχὶ διὰ τοῦ θεοῦ ἡ διασάφησις αὐτῶν ἐστιν διηγήσασθε οὖν μοι
9 Sai shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusuf mafarkinsa. Ya ce masa, “A cikin mafarkina, na ga kuringa a gabana,
καὶ διηγήσατο ὁ ἀρχιοινοχόος τὸ ἐνύπνιον αὐτοῦ τῷ Ιωσηφ καὶ εἶπεν ἐν τῷ ὕπνῳ μου ἦν ἄμπελος ἐναντίον μου
10 kuma a kuringar, akwai rassa uku. Nan da nan kuringar ta yi toho, ta huda, ta kuma yi nonna har suka nuna, suka zama inabi.
ἐν δὲ τῇ ἀμπέλῳ τρεῖς πυθμένες καὶ αὐτὴ θάλλουσα ἀνενηνοχυῖα βλαστούς πέπειροι οἱ βότρυες σταφυλῆς
11 Kwaf Fir’auna kuwa yana a hannuna, na kuma ɗiba inabin na matse su cikin kwaf Fir’auna, na kuma sa kwaf ɗin a hannunsa.”
καὶ τὸ ποτήριον Φαραω ἐν τῇ χειρί μου καὶ ἔλαβον τὴν σταφυλὴν καὶ ἐξέθλιψα αὐτὴν εἰς τὸ ποτήριον καὶ ἔδωκα τὸ ποτήριον εἰς τὰς χεῖρας Φαραω
12 Yusuf ya ce masa, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Rassan nan uku, kwana uku ne.
καὶ εἶπεν αὐτῷ Ιωσηφ τοῦτο ἡ σύγκρισις αὐτοῦ οἱ τρεῖς πυθμένες τρεῖς ἡμέραι εἰσίν
13 Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa.
ἔτι τρεῖς ἡμέραι καὶ μνησθήσεται Φαραω τῆς ἀρχῆς σου καὶ ἀποκαταστήσει σε ἐπὶ τὴν ἀρχιοινοχοΐαν σου καὶ δώσεις τὸ ποτήριον Φαραω εἰς τὴν χεῖρα αὐτοῦ κατὰ τὴν ἀρχήν σου τὴν προτέραν ὡς ἦσθα οἰνοχοῶν
14 Amma fa, sa’ad da kome ya zama maka da kyau, ka tuna da ni, ka kuma yi mini alheri, ka ambace ni wa Fir’auna, ka fid da ni daga wannan kurkuku.
ἀλλὰ μνήσθητί μου διὰ σεαυτοῦ ὅταν εὖ σοι γένηται καὶ ποιήσεις ἐν ἐμοὶ ἔλεος καὶ μνησθήσῃ περὶ ἐμοῦ Φαραω καὶ ἐξάξεις με ἐκ τοῦ ὀχυρώματος τούτου
15 Gama da ƙarfi ne aka ɗauke ni daga ƙasar Ibraniyawa, ko a nan ma ban yi wani abin da ya cancanci a sa ni cikin kurkuku ba.’”
ὅτι κλοπῇ ἐκλάπην ἐκ γῆς Εβραίων καὶ ὧδε οὐκ ἐποίησα οὐδέν ἀλλ’ ἐνέβαλόν με εἰς τὸν λάκκον τοῦτον
16 Sa’ad da shugaban masu tuya ya ga cewa Yusuf ya ba da fassara mai gamsarwa, sai ya ce, wa Yusuf, “Ni ma na yi mafarki. A kaina, akwai kwanduna uku na burodi.
καὶ εἶδεν ὁ ἀρχισιτοποιὸς ὅτι ὀρθῶς συνέκρινεν καὶ εἶπεν τῷ Ιωσηφ κἀγὼ εἶδον ἐνύπνιον καὶ ᾤμην τρία κανᾶ χονδριτῶν αἴρειν ἐπὶ τῆς κεφαλῆς μου
17 A kwandon na bisa, akwai kayan iri-iri da aka toya, masu kyau domin Fir’auna, amma tsuntsaye suka ci su a kwandon da yake kaina.”
ἐν δὲ τῷ κανῷ τῷ ἐπάνω ἀπὸ πάντων τῶν γενῶν ὧν ὁ βασιλεὺς Φαραω ἐσθίει ἔργον σιτοποιοῦ καὶ τὰ πετεινὰ τοῦ οὐρανοῦ κατήσθιεν αὐτὰ ἀπὸ τοῦ κανοῦ τοῦ ἐπάνω τῆς κεφαλῆς μου
18 Yusuf ya ce, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Kwanduna uku, kwanaki uku ne.
ἀποκριθεὶς δὲ Ιωσηφ εἶπεν αὐτῷ αὕτη ἡ σύγκρισις αὐτοῦ τὰ τρία κανᾶ τρεῖς ἡμέραι εἰσίν
19 Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’”
ἔτι τριῶν ἡμερῶν ἀφελεῖ Φαραω τὴν κεφαλήν σου ἀπὸ σοῦ καὶ κρεμάσει σε ἐπὶ ξύλου καὶ φάγεται τὰ ὄρνεα τοῦ οὐρανοῦ τὰς σάρκας σου ἀπὸ σοῦ
20 To, a rana ta uku ne, ranar tunawa da haihuwar Fir’auna, ya kuwa yi biki wa dukan hafsoshinsa. Ya fid da shugaban masu shayarwa da kuma shugaban masu tuya a gaban hafsoshinsa.
ἐγένετο δὲ ἐν τῇ ἡμέρᾳ τῇ τρίτῃ ἡμέρα γενέσεως ἦν Φαραω καὶ ἐποίει πότον πᾶσι τοῖς παισὶν αὐτοῦ καὶ ἐμνήσθη τῆς ἀρχῆς τοῦ ἀρχιοινοχόου καὶ τῆς ἀρχῆς τοῦ ἀρχισιτοποιοῦ ἐν μέσῳ τῶν παίδων αὐτοῦ
21 Ya mai da shugaban masu shayarwa a matsayinsa, saboda haka shugaban masu shayarwa ya sāke sa kwaf a hannun Fir’auna,
καὶ ἀπεκατέστησεν τὸν ἀρχιοινοχόον ἐπὶ τὴν ἀρχὴν αὐτοῦ καὶ ἔδωκεν τὸ ποτήριον εἰς τὴν χεῖρα Φαραω
22 amma ya rataye shugaban masu tuya, kamar dai yadda Yusuf ya faɗa musu a fassarar mafarkan da suka yi.
τὸν δὲ ἀρχισιτοποιὸν ἐκρέμασεν καθὰ συνέκρινεν αὐτοῖς Ιωσηφ
23 Shugaban masu shayarwa fa, bai tuna da Yusuf ba; ya mance da shi.
οὐκ ἐμνήσθη δὲ ὁ ἀρχιοινοχόος τοῦ Ιωσηφ ἀλλὰ ἐπελάθετο αὐτοῦ

< Farawa 40 >