< Farawa 26 >

1 Aka yi yunwa a ƙasar; ban da yunwar da aka yi da fari a zamanin Ibrahim, sai Ishaku ya tafi wurin Abimelek sarkin Filistiyawa a Gerar.
There was a famine in the land, besides the first famine that was in the days of Abraham. Isaac went to Abimelech king of the Philistines, to Gerar.
2 Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ishaku ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar; ka yi zauna a ƙasar da zan faɗa maka.
And God appeared to him, and said, "Do not go down into Egypt. Live in the land I will tell you about.
3 Ka zauna a wannan ƙasa na ɗan lokaci, zan kuwa kasance tare da kai, zan kuma albarkace ka. Gama zan ba da waɗannan ƙasashe gare ka da kuma zuriyarka. Zan kuma cika rantsuwar da na yi wa mahaifinka Ibrahim.
Sojourn in this land, and I will be with you, and will bless you. For to you, and to your descendants, I will give all these lands, and I will establish the oath which I swore to Abraham your father.
4 Zan sa zuriyarka ta yi yawa kamar taurari a sararin sama zan kuwa ba su dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin’ya’yanka kuma za a albarkaci dukan al’umman duniya,
I will multiply your descendants as the stars of the sky, and will give to your descendants all these lands, and by your descendants will all the nations of the earth be blessed,
5 domin Ibrahim ya yi mini biyayya ya kuma kiyaye umarnaina, ƙa’idodina da kuma dokokina.”
because Abraham obeyed my voice, and kept my requirements, my commandments, my statutes, and my laws."
6 Sai Ishaku ya zauna a Gerar.
So Isaac settled in Gerar.
7 Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, “’Yar’uwata ce,” gama yana tsoro yă ce, “Ita matata ce.” Ya yi tunani, “Mutane wannan wuri za su kashe ni ta dalili Rebeka, domin kyakkyawa ce.”
The men of the place asked him about his wife. He said, "She is my sister," for he was afraid to say, "My wife," lest, he thought, "the men of the place might kill me for Rebekah, because she is beautiful to look at."
8 Sa’ad da Ishaku ya daɗe a can, sai Abimelek sarkin Filistiyawa ya duba daga taga ya ga Ishaku yana rungumar matarsa Rebeka.
It happened, when he had been there a long time, that Abimelech king of the Philistines looked out at a window, and saw, and look, Isaac was caressing Rebekah, his wife.
9 Saboda haka Abimelek ya aika Ishaku yă je, sa’an nan ya ce, “Tabbatacce ita matarka ce! Me ya sa ka ce, ‘Ita’yar’uwata ce?’” Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”
Abimelech called Isaac, and said, "Look, surely she is your wife. Why did you say, 'She is my sister?'" Isaac said to him, "Because I thought, 'Lest I die because of her.'"
10 Sa’an nan Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Da a ce wani daga mazanmu ya kwana da matarka, ai, da ka jawo laifi a kanmu.”
Abimelech said, "What is this you have done to us? One of the people might easily have slept with your wife, and you would have brought guilt on us."
11 Saboda haka Abimelek ya yi umarni ga dukan mutane. “Duk wanda ya fitine wannan mutum ko matarsa, tabbatacce za a kashe shi.”
Abimelech commanded all the people, saying, "He who touches this man or his wife will surely be put to death."
12 Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi.
Isaac sowed in that land, and reaped in the same year one hundred times what he planted. And God blessed him.
13 Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.
The man became wealthy, and prospered more and more until he became very wealthy.
14 Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa.
He had possessions of flocks, possessions of herds, and a great household. The Philistines envied him.
15 Saboda haka dukan rijiyoyin da bayin mahaifinsa suka haƙa a kwanakin da mahaifinsa Ibrahim yake da rai, Filistiyawa sun toshe su, suka kuma ciccike su da ƙasa.
Now all the wells which his father's servants had dug in the days of Abraham his father, the Philistines had stopped, and filled with earth.
16 Sai Abimelek ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu; ka fi ƙarfinmu.”
Abimelech said to Isaac, "Go from us, for you are much mightier than we."
17 Saboda haka Ishaku ya fita daga can, ya yi sansani a Kwarin Gerar, ya kuma zauna a can.
Isaac departed from there, camped in the valley of Gerar, and lived there.
18 Ishaku ya sāke tona rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa suka tattoshe bayan mutuwar Ibrahim, ya kuma sa musu sunayen da mahaifinsa ya ba su.
Isaac dug again the wells which the servants of his father Abraham had dug. For the Philistines had stopped them after the death of Abraham. And he called their names after the names by which his father had called them.
19 Barorin Ishaku suka haƙa cikin kwarin suka kuwa sami rijiya mai ruwa mai kyau a can.
Isaac's servants dug in the valley, and found there a well of flowing water.
20 Amma makiyayan Gerar suka yi faɗa da na Ishaku suka ce, “Ruwan namu ne!” Saboda haka Ishaku ya ba wa rijiyar suna Esek, domin sun yi faɗa da shi.
The herdsmen of Gerar argued with Isaac's herdsmen, saying, "The water is ours." He called the name of the well Esek, because they contended with him.
21 Sai suka haƙa wata rijiya, amma suka yi faɗa a kanta ita ma, saboda haka ya ce da ita Sitna.
They dug another well, and they argued over that, also. He called its name Sitnah.
22 Sai Ishaku ya matsa daga can ya sāke haƙa wata rijiyar, babu wani kuma da yi faɗa a kanta. Sai ya ba ta suna Rehobot, yana cewa, “Yanzu Ubangiji ya ba mu wuri, za mu kuwa yi ta haihuwa a ƙasar.”
He left that place, and dug another well. They did not argue over that one. He called it Rehoboth. He said, "For now God has made room for us, and we will be fruitful in the land."
23 Daga can ya haura zuwa Beyersheba.
He went up from there to Beersheba.
24 A wannan dare Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka Ibrahim. Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan albarkace ka, zan kuma ƙara yawan zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”
And God appeared to him the same night, and said, "I am the God of Abraham your father. Do not be afraid, for I am with you, and will bless you, and multiply your descendants for my servant Abraham's sake."
25 Sai Ishaku ya gina bagade a can, ya kuma kira bisa sunan Ubangiji. A can ya kafa tentinsa, a can kuma bayinsa suka haƙa wata rijiya.
He built an altar there, and called on the name of YHWH, and pitched his tent there. There Isaac's servants dug a well.
26 Ana cikin haka, sai Abimelek ya zo wurinsa daga Gerar, tare da Ahuzzat mai ba shi shawara da Fikol shugaban mayaƙansa.
Then Abimelech went to him from Gerar, and Ahuzzath his friend, and Phicol the commander of his army.
27 Ishaku ya tambaye su, “Me ya kawo ku gare ni, da yake kun yi gāba da ni, kuka kuma kore ni?”
Isaac said to them, "Why have you come to me, since you hate me, and have sent me away from you?"
28 Suka amsa, “Mun ga a zahiri cewa Ubangiji yana tare da kai; saboda haka muka ce, ‘Dole rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai.’ Bari mu yi yarjejjeniya da kai
They said, "We saw plainly that God was with you. We said, 'Let there now be an oath between us, even between us and you, and let us make a covenant with you,
29 cewa ba za ka cuce mu ba, kamar yadda ba mu fitine ka ba, amma muka yi maka kirki, muka kuma sallame ka cikin salama. Yanzu kuwa kai albarkatacce ne na Ubangiji.”
that you will do us no harm, as we have not touched you, and as we have done to you nothing but good, and have sent you away in peace.' You are now the blessed of God."
30 Sai Ishaku ya shirya musu liyafa, suka ci suka kuma sha.
He made them a feast, and they ate and drank.
31 Kashegari da sassafe sai mutanen suka yi wa juna rantsuwa. Sa’an nan Ishaku ya sallame su, suka kuwa tafi cikin salama.
They rose up some time in the morning, and swore an oath to each other. Isaac sent them away, and they departed from him in peace.
32 A wannan rana bayin Ishaku suka zo suka faɗa masa game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, “Mun sami ruwa!”
It happened the same day, that Isaac's servants came, and told him concerning the well which they had dug, and said to him, "We have found water."
33 Sai ya kira ta Shiba, don haka har wa yau ana kira garin Beyersheba.
He called it Shibah. Therefore the name of the city is Beersheba to this day.
34 Sa’ad da Yaƙub ya kai shekaru arba’in da haihuwa, sai ya auri Yudit’yar Beyeri mutumin Hitti, da kuma Basemat’yar Elon mutumin Hitti.
When Esau was forty years old, he married Judith, the daughter of Beeri the Hethite, and Basemath, the daughter of Elon the Hethite.
35 Su ne suka zama sanadin baƙin ciki ga Ishaku da Rebeka.
They brought grief to Isaac and Rebekah.

< Farawa 26 >