< Farawa 18 >

1 Ubangiji ya bayyana ga Ibrahim kusa da manyan itatuwan Mamre yayinda yake zaune a mashigin tentinsa da tsakar rana.
Yahweh appeared to him by the oaks of Mamre, as he sat in the tent door in the heat of the day.
2 Da Ibrahim ya ɗaga ido, sai ya ga mutum uku suna tsaye kusa da shi. Sa’ad da ya gan su, sai ya tashi nan da nan daga mashigin tentinsa, ya tarye su, ya rusuna har ƙasa.
He lifted up his eyes and looked, and saw that three men stood near him. When he saw them, he ran to meet them from the tent door, and bowed himself to the earth,
3 Ya ce, “Ranka yă daɗe, in na sami tagomashi daga gare ku kada ku wuce bawanku.
and said, “My lord, if now I have found favor in your sight, please don’t go away from your servant.
4 Bari a kawo ruwa ku wanke ƙafafunku, ku huta a ƙarƙashin wannan itace.
Now let a little water be fetched, wash your feet, and rest yourselves under the tree.
5 Bari in samo muku wani abu ku ci don ku wartsake, sa’an nan ku ci gaba da tafiyarku; da yake kun biyo wurin bawanku.” Suka ce, “To, sai ka yi abin da ka ce.”
I will get a piece of bread so you can refresh your heart. After that you may go your way, now that you have come to your servant.” They said, “Very well, do as you have said.”
6 Saboda haka Ibrahim ya ruga zuwa wurin Saratu a cikin tenti ya ce, “Yi sauri, ki shirya mudu uku na gari mai laushi, ki cuɗa shi, ki yi burodi.”
Abraham hurried into the tent to Sarah, and said, “Quickly prepare three seahs of fine meal, knead it, and make cakes.”
7 Sa’an nan Ibrahim ya yi gudu zuwa garkensa, ya zaɓi ɗan maraƙi ya ba wa bawansa, bawansa kuma ya yi sauri ya gyara shi.
Abraham ran to the herd, and fetched a tender and good calf, and gave it to the servant. He hurried to dress it.
8 Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.
He took butter, milk, and the calf which he had dressed, and set it before them. He stood by them under the tree, and they ate.
9 Sai suka ce masa, “Ina Saratu matarka?” Ibrahim ya ce, “Tana can cikin tenti.”
They asked him, “Where is Sarah, your wife?” He said, “There, in the tent.”
10 Sa’an nan ɗayansu ya ce, “Lalle zan komo wurinka war haka shekara mai zuwa. Saratu matarka kuwa za tă haifi ɗa.” Saratu kuwa tana a bayansu tana ji daga mashigin tenti.
He said, “I will certainly return to you at about this time next year; and behold, Sarah your wife will have a son.” Sarah heard in the tent door, which was behind him.
11 Ibrahim da Saratu dai sun riga sun tsufa sosai. Saratu kuma ta wuce shekarun haihuwa.
Now Abraham and Sarah were old, well advanced in age. Sarah had passed the age of childbearing.
12 Saboda haka Saratu ta yi dariya da ta yi tunani a zuci tana cewa, “Bayan ƙarfina ya ƙare, maigidana kuma ya tsufa, yanzu zan sami wannan jin daɗi?”
Sarah laughed within herself, saying, “After I have grown old will I have pleasure, my lord being old also?”
13 Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’
Yahweh said to Abraham, “Why did Sarah laugh, saying, ‘Will I really bear a child when I am old?’
14 Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.”
Is anything too hard for Yahweh? At the set time I will return to you, when the season comes around, and Sarah will have a son.”
15 Saratu ta ji tsoro, don haka sai ta yi ƙarya ta ce, “Ban yi dariya ba.” Ya ce, “A’a, kin yi dariya.”
Then Sarah denied it, saying, “I didn’t laugh,” for she was afraid. He said, “No, but you did laugh.”
16 Sai mutanen suka tashi suka nufi Sodom, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya, ya yi bankwana da su.
The men rose up from there, and looked toward Sodom. Abraham went with them to see them on their way.
17 Sai Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin yi?
Yahweh said, “Will I hide from Abraham what I do,
18 Lalle Ibrahim zai zama al’umma mai girma da kuma mai iko, kuma ta wurinsa dukan al’umman duniya za su sami albarka.
since Abraham will surely become a great and mighty nation, and all the nations of the earth will be blessed in him?
19 Saboda na zaɓe shi don yă umarci’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.”
For I have known him, to the end that he may command his children and his household after him, that they may keep the way of Yahweh, to do righteousness and justice; to the end that Yahweh may bring on Abraham that which he has spoken of him.”
20 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai,
Yahweh said, “Because the cry of Sodom and Gomorrah is great, and because their sin is very grievous,
21 zan gangara in ga ko abin da suka yi ya yi muni kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”
I will go down now, and see whether their deeds are as bad as the reports which have come to me. If not, I will know.”
22 Sai mutanen suka juya suka nufi wajen Sodom amma Ibrahim ya ci gaba da kasance a gaban Ubangiji.
The men turned from there, and went toward Sodom, but Abraham stood yet before Yahweh.
23 Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta?
Abraham came near, and said, “Will you consume the righteous with the wicked?
24 Me zai faru in akwai mutum hamshin masu adalci a cikin birnin? Ashe, za ka hallaka shi, ba za ka cece wurin saboda mutane hamsin nan masu adalcin da suke a cikinsa ba?
What if there are fifty righteous within the city? Will you consume and not spare the place for the fifty righteous who are in it?
25 Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?”
May it be far from you to do things like that, to kill the righteous with the wicked, so that the righteous should be like the wicked. May that be far from you. Shouldn’t the Judge of all the earth do right?”
26 Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.”
Yahweh said, “If I find in Sodom fifty righteous within the city, then I will spare the whole place for their sake.”
27 Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka,
Abraham answered, “See now, I have taken it on myself to speak to the Lord, although I am dust and ashes.
28 in yawan masu adalci sun kāsa hamshin da mutum biyar fa? Za ka hallaka dukan birnin saboda rashin mutum biyar ɗin?” Ya ce, “In na sami mutum arba’in da biyar a wurin, ba zan hallaka shi ba.”
What if there will lack five of the fifty righteous? Will you destroy all the city for lack of five?” He said, “I will not destroy it if I find forty-five there.”
29 Ya sāke cewa, “In mutum arba’in kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda mutum arba’in ɗin, ba zan aikata ba.”
He spoke to him yet again, and said, “What if there are forty found there?” He said, “I will not do it for the forty’s sake.”
30 Sai ya ce, “Kada Ubangiji ya yi fushi, amma bari in ƙara magana. A ce mutum talatin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Ba zan aikata ba, in na sami mutum talatin a can.”
He said, “Oh don’t let the Lord be angry, and I will speak. What if there are thirty found there?” He said, “I will not do it if I find thirty there.”
31 Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda ashirin ɗin, ba zan hallaka shi ba.”
He said, “See now, I have taken it on myself to speak to the Lord. What if there are twenty found there?” He said, “I will not destroy it for the twenty’s sake.”
32 Sa’an nan Ibrahim ya ce, “Kada Ubangiji yă yi fushi, amma bari in ƙara magana sau ɗaya tak. In aka sami mutum goma kaɗai a can fa?” Ubangiji ya ce, “Saboda goma nan, ba zan hallaka shi ba.”
He said, “Oh don’t let the Lord be angry, and I will speak just once more. What if ten are found there?” He said, “I will not destroy it for the ten’s sake.”
33 Sa’ad da Ubangiji ya gama magana da Ibrahim, ya tafi, Ibrahim kuma ya koma gida.
Yahweh went his way as soon as he had finished communing with Abraham, and Abraham returned to his place.

< Farawa 18 >