< Ezekiyel 10 >

1 Na duba, sai na ga kamannin kursiyin saffaya a kan sararin da yake a bisa kawunan kerubobi.
Then I looked, and see, in the expanse that was over the head of the cherubim there appeared above them as it were a sapphire stone, as the appearance of the likeness of a throne.
2 Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da lilin, “Ka shiga cikin da’irorin da suke ƙarƙashin kerubobi. Ka cika hannuwanka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin ka kuma watsar da su a kan birnin.” Yayinda nake dubawa, sai ya shiga.
He spoke to the man clothed in linen, and said, “Go in between the whirling wheels, even under the cherub, and fill both your hands with coals of fire from between the cherubim, and scatter them over the city.” He went in as I watched.
3 Kerubobin kuwa suna tsaye a gefen kudu na haikali sa’ad da mutumin ya shiga, sai girgije ya cika filin da yake can ciki.
Now the cherubim stood on the right side of the house when the man went in; and the cloud filled the inner court.
4 Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa kerubobi ya tafi zuwa madogarar ƙofar haikali. Girgijen ya cika haikali, filin kuwa ya cika da hasken ɗaukakar Ubangiji.
Yahweh’s glory mounted up from the cherub, and stood over the threshold of the house; and the house was filled with the cloud, and the court was full of the brightness of Yahweh’s glory.
5 Sai aka ji ƙarar fikafikan kerubobin har a filin waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa’ad da ya yi magana.
The sound of the wings of the cherubim was heard even to the outer court, as the voice of God Almighty when he speaks.
6 Sa’ad da Ubangiji ya umarci mutumin da yake saye da lilin cewa, “Ka ɗibi wuta daga cikin tsakanin da’irorin, daga tsakanin kerubobin,” sai mutumin ya shiga ya tsaya kusa da da’irar.
It came to pass, when he commanded the man clothed in linen, saying, “Take fire from between the whirling wheels, from between the cherubim,” that he went in and stood beside a wheel.
7 Sa’an nan ɗaya daga cikin kerubobin ya miƙa hannu zuwa wurin wutar da take tsakaninsu. Ya ɗebo wutar daga ciki ya zuba a hannuwan mutumin da yake saye da lilin, shi kuwa ya karɓa ya fita.
The cherub stretched out his hand from between the cherubim to the fire that was between the cherubim, and took some of it, and put it into the hands of him who was clothed in linen, who took it and went out.
8 (A ƙarƙashin fikafikan kerubobin ana iya ganin abin da ya yi kamar hannuwan mutum.)
The form of a man’s hand appeared here in the cherubim under their wings.
9 Na duba, sai na ga kusa da kerubobin akwai da’irori huɗu, kowanne kusa da kerub guda; da’irorin suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja.
I looked, and behold, there were four wheels beside the cherubim, one wheel beside one cherub, and another wheel beside another cherub. The appearance of the wheels was like a beryl stone.
10 Game da kamanninsu kuwa, huɗu a cikinsu sun yi kama da juna; kowanne ya yi kamar da da’ira a cikin da’ira.
As for their appearance, the four of them had one likeness, like a wheel within a wheel.
11 Yayinda suke tafiya, sukan tafi kowane gefe huɗun da kerubobin suka nufa; da’irorin ba sa juyawa yayinda kerubobin suke tafiya. Kerubobin suka tafi kowane gefen da kan ya nufa, ba tare da juyawa ba sa’ad da suke tafiya.
When they went, they went in their four directions. They didn’t turn as they went, but to the place where the head looked they followed it. They didn’t turn as they went.
12 Jikunansu gaba ɗaya, har da bayansu, hannuwansu da fikafikansu, sun cika gaba ɗaya da idanu, kamar yadda suke a da’irori huɗun.
Their whole body, including their backs, their hands, their wings, and the wheels, were full of eyes all around, even the wheels that the four of them had.
13 Na ji ana kiran da’irorin “da’irorin guguwa.”
As for the wheels, they were called in my hearing, “the whirling wheels”.
14 Kowane daga kerubobin yana da fuskoki huɗu. Fuska ɗaya na kerub ne, na biyun fuskar mutum ne, na ukun fuskar zaki ne, na huɗun kuwa fuskar gaggafa ce.
Every one of them had four faces. The first face was the face of the cherub. The second face was the face of a man. The third face was the face of a lion. The fourth was the face of an eagle.
15 Sai kerubobin suka tashi sama. Waɗannan ne halittu masu ran da na gani kusa da Kogin Kebar.
The cherubim mounted up. This is the living creature that I saw by the river Chebar.
16 Sa’ad da kerubobin suka motsa, sai da’irorin da suke kusa da su su motsa; kuma sa’ad da kerubobin suka buɗe fikafikansu don su tashi daga ƙasa, da’irorin ba sa barin wurarensu.
When the cherubim went, the wheels went beside them; and when the cherubim lifted up their wings to mount up from the earth, the wheels also didn’t turn from beside them.
17 Sa’ad da kerubobin suka tsaya cik, su ma sukan tsaya cik; kuma sa’ad da kerubobin suka tashi, sai su ma su tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun yana a cikinsu.
When they stood, these stood. When they mounted up, these mounted up with them; for the spirit of the living creature was in them.
18 Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa madogarar ƙofar haikali ya kuma tsaya a bisa kerubobi.
Yahweh’s glory went out from over the threshold of the house and stood over the cherubim.
19 Yayinda nake duba, kerubobin suka buɗe fikafikansu suka kuma tashi daga ƙasa, yayinda suka tafi kuwa, da’irorin suka tafi tare da su. Suka tsaya a mashigin ƙofar gabas na gidan Ubangiji, ɗaukakar Allah na Isra’ila kuwa yana a kansu.
The cherubim lifted up their wings and mounted up from the earth in my sight when they went out, with the wheels beside them. Then they stood at the door of the east gate of Yahweh’s house; and the glory of the God of Israel was over them above.
20 Waɗannan ne rayayyun halittun da na gani a ƙarƙashin Allah na Isra’ila kusa da Kogin Kebar, na kuma gane cewa su kerubobi ne.
This is the living creature that I saw under the God of Israel by the river Chebar; and I knew that they were cherubim.
21 Kowanne yana da fuskoki huɗu da fikafikai huɗu, a ƙarƙashin kuwa akwai wani abin da ya yi kamar hannuwan mutum.
Every one had four faces, and every one four wings. The likeness of the hands of a man was under their wings.
22 Fuskokinsu suna da kamanni ɗaya da waɗanda na gani kusa da Kogin Kebar. Kowanne ya tafi kai tsaye sosai.
As for the likeness of their faces, they were the faces which I saw by the river Chebar, their appearances and themselves. They each went straight forward.

< Ezekiyel 10 >