< Fitowa 11 >

1 To, fa, sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan ƙara kawo annoba guda a kan Fir’auna da kan Masar. Bayan haka, zai bar ku, ku fita daga nan. Sa’ad da ya yi haka kuwa, zai kore ku gaba ɗaya. 2 Ka faɗa wa mutane cewa dukan maza da mata, su roƙi maƙwabtansu kayan azurfa da na zinariya.” 3 (Ubangiji ya sa mutane suka sami tagomashi a idon Masarawa, Musa kuwa ya sami girma sosai a cikin ƙasar Masar a gaban fadawan Fir’auna da kuma a gaban jama’ar.) 4 Saboda haka Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Wajen tsakar dare, zan ratsa dukan Masar. 5 Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan’yan farin shanu. 6 Za a yi kuka mai zafi ko’ina a Masar, irin wadda ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a ƙara yi ba. 7 Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila. 8 Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace. 9 Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir’auna zai ƙi kasa kunne gare ka, sai na ƙara aikata waɗansu mu’ujizai cikin Masar.” 10 Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu’ujizai a gaban Fir’auna, amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa ba.

< Fitowa 11 >