< Mai Hadishi 7 >

1 Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.
A good name is better than fine perfume; and the day of death better than the day of one’s birth.
2 Gara a tafi gidan makoki da a je gidan biki, gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum; ya kamata masu rai su lura da haka.
It is better to go to the house of mourning than to go to the house of feasting; for that is the end of all men, and the living should take this to heart.
3 Baƙin ciki ya fi dariya, gama baƙin ciki yakan kawo gyara.
Sorrow is better than laughter; for by the sadness of the face the heart is made good.
4 Zuciyar masu hikima tana a gidan makoki, amma zuciya wawaye tana a gidan shagali.
The heart of the wise is in the house of mourning; but the heart of fools is in the house of mirth.
5 Gara ka saurari tsawatawar mai hikima da ka saurari waƙar wawaye.
It is better to hear the rebuke of the wise than for a man to hear the song of fools.
6 Kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya, haka dariyar wawaye take. Wannan ma ba shi da amfani.
For as the crackling of thorns under a pot, so is the laughter of the fool. This also is vanity.
7 Zalunci yakan mai da mutum mai hikima wawa, cin hanci kuma yakan lalace hali.
Surely extortion makes the wise man foolish; and a bribe destroys the understanding.
8 Ƙarshen abu ya fi farkonsa, haƙuri kuma ya fi girman kai.
Better is the end of a thing than its beginning. The patient in spirit is better than the proud in spirit.
9 Kada ranka yă yi saurin tashi, gama fushi yana zama a cinyar wawaye.
Don’t be hasty in your spirit to be angry, for anger rests in the bosom of fools.
10 Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi waɗannan?” Gama ba daidai ba ne a yi irin waɗannan tambayoyi.
Don’t say, “Why were the former days better than these?” For you do not ask wisely about this.
11 Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana.
Wisdom is as good as an inheritance. Yes, it is more excellent for those who see the sun.
12 Hikima mafaka ce takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi. Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita ita ce amfanin ilimi.
For wisdom is a defense, even as money is a defense; but the excellency of knowledge is that wisdom preserves the life of him who has it.
13 Ku lura da abin da Allah ya yi. Wa zai iya miƙe abin da ya tanƙware?
Consider the work of God, for who can make that straight which he has made crooked?
14 Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki, amma sa’ad da suka lalace, ka tuna, Allah ne ya yi wancan shi ne kuma ya yi wannan. Saboda haka, mutum ba zai san wani abu game da nan gabansa ba.
In the day of prosperity be joyful, and in the day of adversity consider; yes, God has made the one side by side with the other, to the end that man should not find out anything after him.
15 A cikin rayuwan nan ta rashin amfani nawa, na lura da waɗannan abubuwa biyu, mai adalci yana hallakawa cikin adalcinsa, mai mugunta kuma yana tsawon rai cikin muguntarsa.
All this I have seen in my days of vanity: there is a righteous man who perishes in his righteousness, and there is a wicked man who lives long in his evildoing.
16 Kada ka cika yin adalci, fiye da kima, kada kuma ka cika yin hikima, don me za ka hallaka kanka!
Don’t be overly righteous, neither make yourself overly wise. Why should you destroy yourself?
17 Kada ka cika yin mugunta, kada kuma ka cika yin wauta, don me za ka mutu kafin lokacinka?
Don’t be too wicked, neither be foolish. Why should you die before your time?
18 Yana da kyau ka kama ɗaya ba tare da ka saki wancan ba. Mai tsoron Allah zai guji wuce gona da iri.
It is good that you should take hold of this. Yes, also don’t withdraw your hand from that; for he who fears God will come out of them all.
19 Hikima takan sa mutum guda mai hikima yă yi ƙarfi fiye da masu mulki goma a cikin birni.
Wisdom is a strength to the wise man more than ten rulers who are in a city.
20 Babu mai adalci a duniya wanda yake yin abin da yake daidai da bai taɓa yin zunubi ba.
Surely there is not a righteous man on earth who does good and doesn’t sin.
21 Kada ka mai da hankali ga dukan abin da mutane suke faɗi, in ba haka ba wata rana za ka ji bayinka suna zaginka.
Also don’t take heed to all words that are spoken, lest you hear your servant curse you;
22 Gama kai kanka ka sani cewa sau da yawa ka zagi waɗansu.
for often your own heart knows that you yourself have likewise cursed others.
23 Dukan waɗannan na gwada su ta wurin hikima na kuma ce, “Na ƙudurta in zama mai hikima,” amma abin ya fi ƙarfina.
All this I have proved in wisdom. I said, “I will be wise;” but it was far from me.
24 Ko da me hikima take, Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa, wa zai iya gane shi?
That which is, is far off and exceedingly deep. Who can find it out?
25 Saboda haka na mai da hankalina ga fahimi, don in bincika in nemi hikima da yadda aka tsara abubuwa, in kuma fahimci wawancin mugunta da haukar wauta.
I turned around, and my heart sought to know and to search out, and to seek wisdom and the scheme of things, and to know that wickedness is stupidity, and that foolishness is madness.
26 Sai na iske wani abin da ya fi mutuwa ɗaci mace wadda take tarko ne, wadda zuciyarta tarko ne wadda kuma hannuwanta sarƙa ne. Mutumin da ya gamshi Allah zai tsere mata, amma za tă kama mai zunubi.
I find more bitter than death the woman whose heart is snares and traps, whose hands are chains. Whoever pleases God shall escape from her; but the sinner will be ensnared by her.
27 Malami ya ce, “Duba, abin da na gane ke nan. “Na tara abu guda da wani, don in gane tsarin abubuwa,
“Behold, I have found this,” says the Preacher, “to one another, to find an explanation
28 yayinda nake cikin nema amma ban samu ba, sai na sami adali guda cikin dubu, amma ba mace mai adalci guda a cikinsu duka.
which my soul still seeks, but I have not found. I have found one man among a thousand, but I have not found a woman among all those.
29 Wannan ne kaɗai abin da na gane. Allah ya yi mutum tsab amma sai muka rikitar da kanmu.”
Behold, I have only found this: that God made mankind upright; but they search for many inventions.”

< Mai Hadishi 7 >