< Maimaitawar Shari’a 29 >

1 Waɗannan su ne sharuɗan alkawarin da Ubangiji ya umarci Musa yă yi da Isra’ilawa a Mowab, wato, ban da alkawarin da ya yi da su a Dutsen Horeb.
These are the words of the covenant which Yahweh commanded Moses to make with the children of Israel in the land of Moab, in addition to the covenant which he made with them in Horeb.
2 Sai Musa ya tara dukan Isra’ila, ya ce musu, Idanunku sun ga dukan abin da Ubangiji ya yi a Masar ga Fir’auna, ga kuma dukan shugabanninsa da kuma ga dukan ƙasarsa.
Moses called to all Israel, and said to them: Your eyes have seen all that Yahweh did in the land of Egypt to Pharaoh, and to all his servants, and to all his land;
3 Da idanunku kun ga waɗannan gwaje-gwaje, waɗannan alamu masu banmamaki, da al’ajabai masu girma.
the great trials which your eyes saw, the signs, and those great wonders.
4 Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku hankalin ganewa, ko idanun da za su gani, ko kunnuwan da za su ji ba.
But Yahweh has not given you a heart to know, eyes to see, and ears to hear, to this day.
5 Shekaru arba’in da na jagorance ku cikin hamada, tufafinku ba su yage ba, haka kuwa takalman da suke a ƙafafunku.
I have led you forty years in the wilderness. Your clothes have not grown old on you, and your sandals have not grown old on your feet.
6 Ba ku ci burodi ba, ba ku kuwa sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa jiri ba. Ya yi haka don ku san cewa shi ne Ubangiji Allahnku.
You have not eaten bread, neither have you drunk wine or strong drink, that you may know that I am Yahweh your God.
7 Sa’ad da kuka kai wannan wuri, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan, suka fito don su yi yaƙi da mu, amma muka ci su da yaƙi.
When you came to this place, Sihon the king of Heshbon and Og the king of Bashan came out against us to battle, and we struck them.
8 Muka ƙwace ƙasarsu, muka ba da ita gādo ga mutanen Ruben, mutanen Gad, da kuma rabin mutanen Manasse.
We took their land, and gave it for an inheritance to the Reubenites, and to the Gadites, and to the half-tribe of the Manassites.
9 Saboda haka sai ku kiyaye, ku bi sharuɗan wannan alkawari, don ku yi nasara a cikin kome da kuke yi.
Therefore keep the words of this covenant and do them, that you may prosper in all that you do.
10 Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabanninku da manyan mutanenku, dattawanku da hafsoshinku, da kuma dukan sauran mutanen Isra’ila,
All of you stand today in the presence of Yahweh your God: your heads, your tribes, your elders, and your officers, even all the men of Israel,
11 tare da’ya’yanku da matanku, da baƙin da suke zama sansanoninku, har ma da waɗanda suke muku faskare, da waɗanda suke ɗiba muku ruwa.
your little ones, your wives, and the foreigners who are in the middle of your camps, from the one who cuts your wood to the one who draws your water,
12 Kuna tsaye a nan don ku yi alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji yake yi ta wurin rantsuwa da ku a wannan rana,
that you may enter into the covenant of Yahweh your God, and into his oath, which Yahweh your God makes with you today,
13 don yă mai da ku jama’arsa yau, shi kuwa yă zama Allahnku kamar yadda ya yi muku alkawari, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.
that he may establish you today as his people, and that he may be your God, as he spoke to you and as he swore to your fathers, to Abraham, to Isaac, and to Jacob.
14 Ina yin wannan alkawari da rantsuwar, ba da ku kaɗai da
Neither do I make this covenant and this oath with you only,
15 kuke tsattsaye a nan tare da mu a yau a gaban Ubangiji Allahnmu ba, amma har da waɗanda ba sa nan yau.
but with those who stand here with us today before Yahweh our God, and also with those who are not here with us today
16 Ku kanku kun san yadda muka yi zama a Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al’ummai muka wuce.
(for you know how we lived in the land of Egypt, and how we came through the middle of the nations through which you passed;
17 A cikinsu, kun ga siffofi masu banƙyama da gumaka na itace da dutse, na azurfa da zinariya.
and you have seen their abominations and their idols of wood, stone, silver, and gold, which were among them);
18 Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, tă koma ga bauta wa gumakan waɗannan al’ummai. Kada a sami wani tushe mai ba da’ya’ya masu dafi, masu ɗaci a cikinku.
lest there should be among you man, woman, family, or tribe whose heart turns away today from Yahweh our God, to go to serve the gods of those nations; lest there should be among you a root that produces bitter poison;
19 Idan kuma wani mutum ya ji kalmomi na wannan rantsuwa, ya kuma sa wa kansa albarka yana tunani cewa, “Ba abin da zai same ni, ko da na nace a taurinkaina.” Wannan zai jawo lalacewar dukan Isra’ila tare da kai.
and it happen, when he hears the words of this curse, that he bless himself in his heart, saying, “I shall have peace, though I walk in the stubbornness of my heart,” to destroy the moist with the dry.
20 Ubangiji ba zai gafarce shi ba, fushinsa da kishinsa za su ƙuna a kan wannan mutum. Dukan la’anonin da aka rubuta a wannan littafi za su fāɗo a kansa, Ubangiji kuwa zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama.
Yahweh will not pardon him, but then Yahweh’s anger and his jealousy will smoke against that man, and all the curse that is written in this book will fall on him, and Yahweh will blot out his name from under the sky.
21 Ubangiji zai ware shi daga dukan kabilan Isra’ila don yă hukunta shi bisa ga dukan la’anonin alkawarin da aka rubuta a wannan Littafin Doka.
Yahweh will set him apart for evil out of all the tribes of Israel, according to all the curses of the covenant written in this book of the law.
22 Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato,’ya’yan da za su gāje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji ya buge ta da su.
The generation to come—your children who will rise up after you, and the foreigner who will come from a far land—will say, when they see the plagues of that land, and the sicknesses with which Yahweh has made it sick,
23 Ƙasar gaba ɗaya za tă zama gishiri mai ƙuna marar amfani da kuma kibiritu, babu shuki, babu abin da yake tsirowa, babu itatuwan da suke girma a cikinta. Za tă zama kamar yadda aka hallaka Sodom da Gomorra, Adma da Zeboyim, waɗanda Ubangiji ya hallaka cikin zafin fushinsa.
that all of its land is sulfur, salt, and burning, that it is not sown, doesn’t produce, nor does any grass grow in it, like the overthrow of Sodom, Gomorrah, Admah, and Zeboiim, which Yahweh overthrew in his anger, and in his wrath.
24 Dukan al’ummai za su yi tambaya su ce, “Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya jawo wannan fushi mai tsanani haka?”
Even all the nations will say, “Why has Yahweh done this to this land? What does the heat of this great anger mean?”
25 Amsar kuwa za tă zama, “Wannan ya zama haka domin wannan mutane, sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, alkawarin da ya yi da su sa’ad da ya fitar da su daga Masar.
Then men will say, “Because they abandoned the covenant of Yahweh, the God of their fathers, which he made with them when he brought them out of the land of Egypt,
26 Sun juya, suka bauta wa waɗansu alloli, suka rusuna musu, allolin da ba su sani ba, allolin da Ubangiji bai ba su ba.
and went and served other gods and worshiped them, gods that they didn’t know and that he had not given to them.
27 Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan wannan ƙasa, har ya kawo dukan la’anoni da aka rubuta a wannan littafi a kanta.
Therefore Yahweh’s anger burned against this land, to bring on it all the curses that are written in this book.
28 Cikin zafin fushi da babbar hasala Ubangiji ya tumɓuke su daga ƙasarsu, ya watsar da su cikin wata ƙasa dabam, kamar yadda suke a yau.”
Yahweh rooted them out of their land in anger, in wrath, and in great indignation, and thrust them into another land, as it is today.”
29 Ubangiji Allahnmu bai bayyana abubuwa na yanzu da na nan gaba ba, amma ya umarce mu mu kiyaye kalmomin dokar da ya ba mu, mu da kuma’ya’yanmu har abada.
The secret things belong to Yahweh our God; but the things that are revealed belong to us and to our children forever, that we may do all the words of this law.

< Maimaitawar Shari’a 29 >