< Daniyel 12 >

1 “A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi. 2 Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. 3 Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin. 4 Amma kai, Daniyel, ka rufe zancen nan ka kuma liƙe kalmomin littafin nan har sai ƙarshe. Mutane da yawa za su yi ta kai komo don neman sani.” 5 Sa’an nan ni, Daniyel, na duba, a gabana kuwa ga waɗansu mutum biyu tsaye, ɗaya a wannan hayen kogi ɗaya kuma a ƙetaren kogin. 6 Ɗayansu ya ce wa mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, “Har yaushe waɗannan abubuwan banmamakin za su cika?” 7 Mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, ya ɗaga hannun damansa da kuma na hagunsa sama, sai na ji yana rantsuwa da wannan da yake raye har abada, yana cewa, “Zai kasance na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa’ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.” 8 Na kuma ji, amma ban fahimta ba. Don haka sai na yi tambaya, “Ranka yă daɗe, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?” 9 Sai ya amsa ya ce, “Ka kama hanyarka, Daniyel, domin a rufe kalmomin aka kuma liƙe su har sai ƙarshen lokaci. 10 Za a tsarkake mutane da yawa, za a maishe su marasa aibi a kuma tace su; amma mugaye za su ci gaba da mugunta. Babu wani mugun da zai fahimta, amma waɗanda za su zama masu hikima za su fahimta. 11 “Daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kuma kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana 1,290. 12 Mai albarka ne wanda ya jira har yă zuwa ƙarshen kwanakin nan 1,335. 13 “Gare ka dai, ka yi tafiyarka har zuwa ƙarshe. Za ka huta, sa’an nan a ƙarshen kwanaki za ka tashi don karɓi sashen gadon da aka ba ka.”

< Daniyel 12 >