< Amos 9 >
1 Na ga Ubangiji yana tsaye a gaban bagade, ya kuma ce, “Bugi kan ginshiƙan don madogaran ƙofa su girgiza. Saukar da su a kan dukan mutane; waɗanda ba su mutu ba zan kashe su da takobi. Ba mutum guda da zai tsere, babu wani da zai tsira.
2 Ko da sun tona rami kamar zurfin kabari, daga can hannuna zai fitar da su. Ko da sun hau can sama daga can zan sauko da su. (Sheol )
3 Ko da sun ɓuya a bisa Karmel, a can zan farauce su in cafko. Ko da sun ɓuya can ƙarƙashin teku, a can zan umarci maciji yă sare su.
4 Ko da abokan gābansu sun kore su zuwa zaman bauta, a can zan umarci takobi yă kashe su. “Zan sa musu ido don mugunta ba don alheri ba.”
5 Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, shi da yakan taɓa ƙasa sai ta narke, kuma dukan mazauna cikinta suna makoki, ƙasar gaba ɗaya takan hau ta kuma sauka kamar Nilu, sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar,
6 shi da ya gina kyakkyawar fadarsa a cikin sammai ya kuma kafa harsashenta a duniya, shi da yakan kira ruwan teku yă kuma kwarara su a bisa duniya, Ubangiji ne sunansa.
7 “Ku ba Isra’ilawa ba ne, daidai gare ni kamar yadda Kushawa suke?” In ji Ubangiji. “Ban fito da Isra’ila daga Masar ba, Filistiyawa kuma daga Kaftor Arameyawa kuma daga Kir ba?
8 “Tabbatacce idanun Ubangiji Mai Iko Duka suna a kan mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka shi daga fuskar duniya, duk da haka ba zan hallaka gidan Yaƙub ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji.
9 “Gama zan ba da umarni, zan kuma tankaɗe gidan Isra’ila a cikin dukan ƙasashe kamar yadda ake tankaɗe hatsi a cikin matankaɗi kuma ko ƙwaya ɗaya ba za tă fāɗi a ƙasa ba.
10 Dukan masu zunubi a cikin mutanena za su mutu ta wurin takobi, wato, su masu cewa, ‘Masifa ba za tă fāɗo ko ta same mu ba.’
11 “A wannan rana zan maido da tentin Dawuda da ya fāɗi. Zan gyaggyara wuraren da suka yayyage, in kuma maido da kufansa in gina shi kamar yadda yake a dā,
12 domin su mallaki raguwar Edom da duk al’ummai da suke amsa sunana,” in ji Ubangiji shi wanda zai yi waɗannan abubuwa.
13 “Ranaku suna zuwa, in ji Ubangiji, “sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi. Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu yă kuma kwararo daga tuddai.
14 Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta mutanena Isra’ila. “Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu; za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu.
15 Zan dasa Isra’ila a ƙasarsu, ba kuwa za a ƙara tumɓuke su daga ƙasar da na ba su ba,” in ji Ubangiji Allahnku.