< 2 Sama’ila 13 >

1 Ana nan sai Amnon ɗan Dawuda ya fara son Tamar, kyakkyawar’yar’uwar Absalom ɗan Dawuda.
大衛的兒子押沙龍有一個美貌的妹子,名叫她瑪。大衛的兒子暗嫩愛她。
2 Amnon ya matsu ƙwarai har abin ya sa shi ciwo saboda ƙanuwarsa Tamar. Ya gane zai zama da wuya yă sadu da Tamar ita kaɗai, gama ba ta taɓa kwana da namiji ba.
暗嫩為他妹子她瑪憂急成病。她瑪還是處女,暗嫩以為難向她行事。
3 To, Amnon yana da wani aboki mai suna Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda. Yonadab dai mai wayo ne ƙwarai.
暗嫩有一個朋友,名叫約拿達,是大衛長兄示米亞的兒子。這約拿達為人極其狡猾;
4 Ya tambayi Amnon ya ce, “Don me kowace safiya fuskarka a ɓace take? Kai ba yaron sarki ba ne? Faɗa mini, me ke faruwa?” Amnon ya ce masa, “Ina son Tamar ƙanuwar wan nawa Absalom ne.”
他問暗嫩說:「王的兒子啊,為何一天比一天瘦弱呢?請你告訴我。」暗嫩回答說:「我愛我兄弟押沙龍的妹子她瑪。」
5 Yonadab ya ce, “Je gado ka kwanta kamar ba ka da lafiya. Sa’ad da mahaifinka ya zo ganinka, sai ka ce masa, ‘Ina so ƙanuwata Tamar tă kawo mini wani abu in ci. Bari tă shirya abincin a gabana don in ganta, in kuma ci daga hannunta.’”
約拿達說:「你不如躺在床上裝病;你父親來看你,就對他說:『求父叫我妹子她瑪來,在我眼前預備食物,遞給我吃,使我看見,好從她手裏接過來吃。』」
6 Sai Amnon ya kwanta sai ka ce yana ciwo. Da sarki ya zo don ganinsa, sai Amnon ya ce, “Zan so ƙanuwata Tamar tă zo tă shirya mini abinci a gabana, don in ci daga hannunta.”
於是暗嫩躺臥裝病。王來看他,他對王說:「求父叫我妹子她瑪來,在我眼前為我做兩個餅,我好從她手裏接過來吃。」
7 Dawuda kuwa ya aika wa Tamar a fada, ya ce, “Ki je gidan Amnon ɗan’uwanki, ki yi masa abinci.”
大衛就打發人到宮裏,對她瑪說:「你往你哥哥暗嫩的屋裏去,為他預備食物。」
8 Saboda haka Tamar ta tafi gidan ɗan’uwanta Amnon, wanda yake kwance. Ta ɗauki fulawa, ta kwaɓa, ta yi burodi a gabansa ta toya shi.
她瑪就到她哥哥暗嫩的屋裏;暗嫩正躺臥。她瑪摶麵,在他眼前做餅,且烤熟了,
9 Sa’an nan ta juye a kasko ta ba shi burodin, amma ya ƙi ci. Amnon ya ce, “A sa kowa yă fita daga nan.” Saboda haka kowa ya fita ya bar shi.
在他面前將餅從鍋裏倒出來,他卻不肯吃,便說:「眾人離開我出去吧!」眾人就都離開他,出去了。
10 Sa’an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a nan a cikin ɗakin kwanciyata, don in ci daga hannunki.” Tamar kuwa ta ɗauki burodin da ta toya, ta kawo wa ɗan’uwanta Amnon a ciki ɗakin kwanciyarsa.
暗嫩對她瑪說:「你把食物拿進臥房,我好從你手裏接過來吃。」她瑪就把所做的餅拿進臥房,到她哥哥暗嫩那裏,
11 Amma da ta kai masa don yă ci, sai ya cafke ta ya ce, “Zo in kwana da ke,’yar’uwata.”
拿着餅上前給他吃,他便拉住她瑪,說:「我妹妹,你來與我同寢。」
12 Ta ce, “Kada ka yi wannan ɗan’uwana! Kada ka tilasta ni. Bai kamata a yi irin wannan abu a Isra’ila ba! Kada ka yi wannan mugun abu.
她瑪說:「我哥哥,不要玷辱我。以色列人中不當這樣行,你不要做這醜事;
13 Ni fa, ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuma za ka zama kamar wani mugun wawa a Isra’ila. Ina roƙonka ka yi wa sarki magana; ba zai hana ni aurenka ba.”
你玷辱了我,我何以掩蓋我的羞恥呢?你在以色列中也成了愚妄人。你可以求王,他必不禁止我歸你。」
14 Amma Amnon ya ƙi yă saurare ta, da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata fyaɗe.
但暗嫩不肯聽她的話,因比她力大,就玷辱她,與她同寢。
15 Bayan ya yi lalata da ita sai Amnon ya ƙi ta da mummunan ƙiyayya. Zahiri ya ƙi ta fiye da ya ƙaunace ta. Sai Amnon ya ce mata, “Tashi, ki fita!”
隨後,暗嫩極其恨她,那恨她的心比先前愛她的心更甚,對她說:「你起來,去吧!」
16 Ta ce, “A’a! Korina zai fi muni da abin da ka riga ka yi mini.” Amma ya ƙi yă saurare ta.
她瑪說:「不要這樣!你趕出我去的這罪比你才行的更重!」但暗嫩不肯聽她的話,
17 Sai ya kira bawansa ya ce, “Fitar da matan nan daga nan, ka rufe ƙofa.”
就叫伺候自己的僕人來,說:「將這個女子趕出去!她一出去,你就關門,上閂。」
18 Saboda haka bawansa ya fitar da ita, ya kuma sa aka rufe ƙofa. Tana sanye da doguwar riga mai kayan ado masu tsada, gama wannan ne irin kayan da budurwai’ya’yan sarki mata suke sawa.
那時她瑪穿着彩衣,因為沒有出嫁的公主都是這樣穿。暗嫩的僕人就把她趕出去,關門上閂。
19 Sai Tamar ta zuba toka a kanta, ta kuma yayyage doguwar riga mai kayan adon da take sanye da shi. Ta sa hannunta a kai, ta tafi tana kuka da ƙarfi.
她瑪把灰塵撒在頭上,撕裂所穿的彩衣,以手抱頭,一面行走,一面哭喊。
20 Absalom ɗan’uwanta ya ce mata, “Amnon, ɗan’uwanki ya ɓata ki ko? To, ki yi shiru’yar’uwata; ai, ɗan’uwanki ne. Kada wannan abu yă dame ki.” Tamar kuwa ta zauna a gidan ɗan’uwanta Absalom, zaman kaɗaici.
她胞兄押沙龍問她說:「莫非你哥哥暗嫩與你親近了嗎?我妹妹,暫且不要作聲,他是你的哥哥,不要將這事放在心上。」她瑪就孤孤單單地住在她胞兄押沙龍家裏。
21 Da Sarki Dawuda ya ji dukan abin da ya faru, sai ya husata ƙwarai.
大衛王聽見這事,就甚發怒。
22 Absalom kuwa bai yi wa Amnon wata magana ta alheri ko ta mugunta ba; ya ƙi jinin Amnon domin ya ci mutuncin ƙanuwarsa Tamar.
押沙龍並不和他哥哥暗嫩說好說歹;因為暗嫩玷辱他妹妹她瑪,所以押沙龍恨惡他。
23 Bayan shekaru biyu, sa’ad da masu askin tumakin Absalom suna Ba’al-Hazor, kusa da iyakar Efraim, sai ya gayyaci dukan’ya’yan sarki maza a can.
過了二年,在靠近以法蓮的巴力‧夏瑣有人為押沙龍剪羊毛;押沙龍請王的眾子與他同去。
24 Sai Absalom ya je wurin sarki ya ce, “Bawanka ya sa masu askin tumaki sun zo. Ko sarki da fadawansa za su zo tare da ni?”
押沙龍來見王,說:「現在有人為僕人剪羊毛,請王和王的臣僕與僕人同去。」
25 Sarki ya ce, “A’a ɗana, bai kamata dukanmu mu tafi ba; don kada nauyi yă yi maka yawa.” Absalom dai ya dāge, duk da haka sarki ya ƙi yă je, sai dai ya albarkace shi.
王對押沙龍說:「我兒,我們不必都去,恐怕使你耗費太多。」押沙龍再三請王,王仍是不肯去,只為他祝福。
26 Sa’an nan Absalom ya ce, to, “In ba za ka ba, ina roƙonka bari Amnon ɗan’uwana yă zo tare da mu.” Sarki ya ce masa, “Don me zai tafi tare da kai?”
押沙龍說:「王若不去,求王許我哥哥暗嫩同去。」王說:「何必要他去呢?」
27 Amma Absalom ya nace don sarki yă yarda, saboda haka sarki ya bar Amnon da sauran’ya’yan sarki maza su tafi tare da shi.
押沙龍再三求王,王就許暗嫩和王的眾子與他同去。
28 Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.”
押沙龍吩咐僕人說:「你們注意,看暗嫩飲酒暢快的時候,我對你們說殺暗嫩,你們便殺他,不要懼怕。這不是我吩咐你們的嗎?你們只管壯膽奮勇!」
29 Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.
押沙龍的僕人就照押沙龍所吩咐的,向暗嫩行了。王的眾子都起來,各人騎上騾子,逃跑了。
30 Yayinda suke kan hanyarsu, sai labari ya kai kunnen Dawuda cewa, “Absalom ya kashe dukan’ya’yan sarki maza; ko ɗayansu Absalom bai rage ba.”
他們還在路上,有風聲傳到大衛那裏,說:「押沙龍將王的眾子都殺了,沒有留下一個。」
31 Sai sarki ya tashi, ya yage tufafinsa, ya kuma kwanta a ƙasa; dukan bayinsa kuwa suka tsaya da rigunansu yagaggu.
王就起來,撕裂衣服,躺在地上。王的臣僕也都撕裂衣服,站在旁邊。
32 Amma Yonadab, ɗan Shimeya ɗan’uwan Dawuda ya ce, “Kada ranka yă daɗe yă yi tunani cewa an kashe dukan’ya’yan sarki maza; Amnon ne kaɗai ya mutu. Wannan ce niyyar Absalom tun lokacin da Amnon ya yi wa Tamar’yar’uwansa fyaɗe.
大衛的長兄,示米亞的兒子約拿達說:「我主,不要以為王的眾子-少年人都殺了,只有暗嫩一個人死了。自從暗嫩玷辱押沙龍妹子她瑪的那日,押沙龍就定意殺暗嫩了。
33 Kada mai girma sarki yă damu da jita-jitan nan cewa an kashe dukan’ya’yan sarki maza. Amnon ne kaɗai ya mutu.”
現在,我主我王,不要把這事放在心上,以為王的眾子都死了,只有暗嫩一個人死了。」
34 Ana cikin haka, sai Absalom ya gudu. To, mutumin da yake tsaro a wannan lokaci ya ɗaga kai sai ya ga mutane da yawa a hanya, yamma da shi, suna gangarowa daga gefen tudu. Sai mai tsaron ya je ya gaya wa sarki cewa, “Na ga mutane ta wajen Horonayim, a gefen tudu.”
押沙龍逃跑了。 守望的少年人舉目觀看,見有許多人從山坡的路上來。
35 Yonadab ya ce wa Sarki, “Duba, ga’ya’yan sarki maza sun zo; ya faru kamar dai yadda bawanka ya faɗa.”
約拿達對王說:「看哪,王的眾子都來了,果然與你僕人所說的相合。」
36 Yana gama magana, sai ga’ya’yan sarki maza suka shigo suna kuka da ƙarfi. Sarki ma da dukan bayinsa suka yi kuka mai zafi.
話才說完,王的眾子都到了,放聲大哭;王和臣僕也都哭得甚慟。
37 Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai ɗan Ammihud, sarkin Geshur. Amma Sarki Dawuda ya yi ta makokin ɗansa kowace rana.
押沙龍逃到基述王亞米忽的兒子達買那裏去了。大衛天天為他兒子悲哀。
38 Bayan Absalom ya gudu sai ya je wurin Geshur, ya zauna a can shekara uku.
押沙龍逃到基述,在那裏住了三年。
39 Sai zuciyar sarki Dawuda ya komo kan Absalom, gama an yi masa ta’aziyya game da mutuwar Amnon.
暗嫩死了以後,大衛王得了安慰,心裏切切想念押沙龍。

< 2 Sama’ila 13 >