< 2 Sarakuna 10 >

1 To, akwai’ya’ya maza saba’in na gidan Ahab a Samariya. Saboda haka Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika su Samariya, zuwa ga shugabannin Yezireyel, da kuma ga masu lura da’ya’yan Ahab. Ya ce,
Now Ahab had seventy sons in Samaria. Jehu wrote letters and sent them to Samaria, to the rulers of Jezreel, even the elders, and to those who brought up Ahab’s sons, saying,
2 “Da zarar wasiƙan nan ta sadu da ku, da yake’ya’yan maigidanku suna tare da ku, kuna kuma da kekunan yaƙi da dawakai, da birni mai katanga da makamai,
“Now as soon as this letter comes to you, since your master’s sons are with you, and you have chariots and horses, a fortified city also, and armor,
3 sai ku zaɓi mafi cancanta a cikin’ya’yan maigidanku ku sa shi a kan kursiyin mahaifinsa. Sa’an nan ku yi yaƙi don gidan maigidanku.”
select the best and fittest of your master’s sons, set him on his father’s throne, and fight for your master’s house.”
4 Amma suka razana suka ce, “Idan sarakuna biyu ba su iya yin tsayayya da shi ba, wane mu?”
But they were exceedingly afraid, and said, “Behold, the two kings didn’t stand before him! How then shall we stand?”
5 Saboda haka sarkin fada, da gwamnan birnin, da dattawa, da kuma masu lura da’ya’yan suka aika da saƙo ga Yehu, cewa, “Mu bayinka ne, za mu kuma yi duk abin da ka ce. Ba za mu naɗa kowa sarki ba; sai ka yi abin da ka ga ya fi kyau.”
He who was over the household, and he who was over the city, the elders also, and those who raised the children, sent to Jehu, saying, “We are your servants, and will do all that you ask us. We will not make any man king. You do that which is good in your eyes.”
6 Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To,’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su.
Then he wrote a letter the second time to them, saying, “If you are on my side, and if you will listen to my voice, take the heads of the men who are your master’s sons, and come to me to Jezreel by tomorrow this time.” Now the king’s sons, being seventy persons, were with the great men of the city, who brought them up.
7 Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel.
When the letter came to them, they took the king’s sons and killed them, even seventy people, and put their heads in baskets, and sent them to him to Jezreel.
8 Da ɗan saƙon ya iso, sai aka ce wa Yehu, “Sun kawo kawunan’ya’yan sarki.” Sai Yehu ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar gari har safiya.”
A messenger came and told him, “They have brought the heads of the king’s sons.” He said, “Lay them in two heaps at the entrance of the gate until the morning.”
9 Da gari ya waye, sai Yehu ya fita ya tsaya a gaban dukan jama’a ya ce, “Ba ku da laifi. Ni ne na ƙulla wa maigidana maƙarƙashiya, na kuma kashe shi, amma wa ya karkashe dukan waɗannan?
In the morning, he went out and stood, and said to all the people, “You are righteous. Behold, I conspired against my master and killed him, but who killed all these?
10 Ku sani fa, ba kalmar da Ubangiji ya faɗa game da gidan Ahab da ba za tă cika ba. Ubangiji ya yi abin da ya alkawarta ta bakin bawansa Iliya.”
Know now that nothing will fall to the earth of Yahweh’s word, which Yahweh spoke concerning Ahab’s house. For Yahweh has done that which he spoke by his servant Elijah.”
11 Saboda haka Yehu ya kashe duk waɗanda suka rage na iyalin Ahab a Yezireyel, tare da dukan fadawansa da aminansa da firistocinsa, ba a bar masa kowa ba.
So Jehu struck all that remained of Ahab’s house in Jezreel, with all his great men, his familiar friends, and his priests, until he left him no one remaining.
12 Sa’an nan Yehu ya nufi Samariya. Da ya kai Bet-Eked na Makiyaya,
He arose and departed, and went to Samaria. As he was at the shearing house of the shepherds on the way,
13 sai ya gamu da waɗansu daga dangin Ahaziya sarkin Yahuda, sai ya tambaye su, ya ce, “Ku, su wane ne?” Suka ce, “Mu dangin Ahaziya ne, mun kuma zo ne mu gai da iyalan sarki da kuma mahaifiyar sarauniya.”
Jehu met with the brothers of Ahaziah king of Judah, and said, “Who are you?” They answered, “We are the brothers of Ahaziah. We are going down to greet the children of the king and the children of the queen.”
14 Sai ya umarta ya ce, “A kama su da rai!” Aka kuwa kama su aka yayyanka kusa da rijiyar Bet-Eked, su arba’in da biyu. Ba a bar wani da rai ba.
He said, “Take them alive!” They took them alive, and killed them at the pit of the shearing house, even forty-two men. He didn’t leave any of them.
15 Bayan ya bar wurin, sai ya gamu da Yehonadab ɗan Rekab wanda yake kan hanyarsa don yă sadu da shi. Sai Yehu ya gaishe shi, ya ce, “Ka amince da ni yadda na amince da kai?” Yehonadab ya ce, “I.” Yehu ya ce, “To, in haka ne ka ba ni hannunka.” Sai ya miƙa masa, Yehu kuwa ya ja shi cikin keken yaƙin.
When he had departed from there, he met Jehonadab the son of Rechab coming to meet him. He greeted him, and said to him, “Is your heart right, as my heart is with your heart?” Jehonadab answered, “It is.” “If it is, give me your hand.” He gave him his hand; and he took him up to him into the chariot.
16 Yehu ya ce, “Zo tare da ni ka ga himmata saboda Ubangiji.” Sa’an nan ya sa suka tafi tare cikin keken yaƙinsa.
He said, “Come with me, and see my zeal for Yahweh.” So they made him ride in his chariot.
17 Da Yehu ya isa Samariya, sai ya karkashe dukan sauran iyalin Ahab, ya hallaka su, bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.
When he came to Samaria, he struck all who remained to Ahab in Samaria, until he had destroyed them, according to Yahweh’s word which he spoke to Elijah.
18 Sa’an nan Yehu ya tattara dukan jama’a ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba’al kaɗan ne kawai; amma Yehu zai bauta masa sosai.
Jehu gathered all the people together, and said to them, “Ahab served Baal a little, but Jehu will serve him much.
19 Yanzu sai ku kira dukan annabawan Ba’al, dukan masu yin masa hidima da kuma dukan firistocinsa. Ku tabbata ba a manta da wani ba, gama zan yi wa Ba’al babbar hadaya. Duk wanda bai zo ba, a bakin ransa.” Amma Yehu yana wayo ne domin yă hallaka masu yi wa Ba’al sujada.
Now therefore call to me all the prophets of Baal, all of his worshipers, and all of his priests. Let no one be absent, for I have a great sacrifice to Baal. Whoever is absent, he shall not live.” But Jehu did deceptively, intending to destroy the worshipers of Baal.
20 Yehu ya ce, “Ku kira jama’a don a girmama Ba’al.” Saboda haka suka yi shela.
Jehu said, “Sanctify a solemn assembly for Baal!” So they proclaimed it.
21 Sa’an nan ya aika saƙo ko’ina a Isra’ila, dukan masu yi wa Ba’al hidima kuwa suka tattaru, ba mutumin da bai zo ba. Suka yi cincirindo a haikalin Ba’al har sai da ya cika makil.
Jehu sent through all Israel; and all the worshipers of Baal came, so that there was not a man left that didn’t come. They came into the house of Baal; and the house of Baal was filled from one end to another.
22 Sai Yehu ya ce wa mai ajiyar tufafi, “Ka kawo riguna domin dukan masu yi wa Ba’al hidima.” Sai ya fito musu da riguna.
He said to him who kept the wardrobe, “Bring out robes for all the worshipers of Baal!” So he brought robes out to them.
23 Sa’an nan Yehu da Yehonadab ɗan Rekab, suka shiga haikalin Ba’al. Yehu ya ce wa masu yi wa Ba’al sujada, “Ku dudduba ku tabbatar cewa babu wani bawan Ubangiji a nan tare da ku, sai masu hidimar Ba’al kawai.”
Jehu went with Jehonadab the son of Rechab into the house of Baal. Then he said to the worshipers of Baal, “Search, and see that none of the servants of Yahweh are here with you, but only the worshipers of Baal.”
24 Saboda haka suka shiga don su miƙa hadayu da kuma hadaya ta ƙonawa. To, Yehu ya riga ya ba wa mutane takwas wannan kashedi a waje cewa, “In waninku ya bar ɗaya daga cikin mutanen nan da nake danƙa a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”
So they went in to offer sacrifices and burnt offerings. Now Jehu had appointed for himself eighty men outside, and said, “If any of the men whom I bring into your hands escape, he who lets him go, his life shall be for the life of him.”
25 Nan da nan sa’ad da Yehu ya gama yin hadayar, sai ya umarci masu gadin da hafsoshi, “Ku shiga ku karkashe su; kada ku bar wani yă tsere.” Saboda haka suka karkashe su da takobi. Masu gadin da hafsoshin suka wuwwurga gawawwakinsu waje, suka kuma shiga ciki cikin haikalin Ba’al ɗin,
As soon as he had finished offering the burnt offering, Jehu said to the guard and to the captains, “Go in and kill them! Let no one escape.” So they struck them with the edge of the sword. The guard and the captains threw the bodies out, and went to the inner shrine of the house of Baal.
26 suka fitar da dutsen tsafi daga haikalin Ba’al, suka kuma ƙone shi.
They brought out the pillars that were in the house of Baal and burned them.
27 Suka farfasa dutsen tsafin Ba’al, suka kuma rushe haikalin, mutane suka mai da wurin salga har yă zuwa yau.
They broke down the pillar of Baal, and broke down the house of Baal, and made it a latrine, to this day.
28 Ta haka Yehu ya hallaka butar Ba’al a Isra’ila.
Thus Jehu destroyed Baal out of Israel.
29 Duk da haka, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba, wato, yin sujada ga siffofin maruƙa na zinariya a Betel da kuma Dan.
However, Jehu didn’t depart from the sins of Jeroboam the son of Nebat, with which he made Israel to sin—the golden calves that were in Bethel and that were in Dan.
30 Ubangiji ya ce wa Yehu, “Tun da yake ka aikata abin da yake mai kyau a idanuna, ka kuma yi wa gidan Ahab dukan abin da yake a zuciyata, ina yin maka alkawari cewa zuriyarka za su yi mulkin Isra’ila har tsara ta huɗu.”
Yahweh said to Jehu, “Because you have done well in executing that which is right in my eyes, and have done to Ahab’s house according to all that was in my heart, your descendants shall sit on the throne of Israel to the fourth generation.”
31 Duk da haka, Yehu bai mai da hankali ya kiyaye dokokin Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa ba. Bai rabu da zunubin Yerobowam, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba.
But Jehu took no heed to walk in the law of Yahweh, the God of Israel, with all his heart. He didn’t depart from the sins of Jeroboam, with which he made Israel to sin.
32 A kwanakin sai Ubangiji ya fara rage girman Isra’ila, Hazayel ya yi nasara a bisa Isra’ila a ko’ina a yankinsu
In those days Yahweh began to cut away parts of Israel; and Hazael struck them in all the borders of Israel
33 gabas da Urdun, cikin dukan ƙasar Gileyad (yankin Gad, da na Ruben, da na Manasse), daga Arower wajen Kwarin Arnon ya ratsa Gileyad zuwa Bashan.
from the Jordan eastward, all the land of Gilead, the Gadites, and the Reubenites, and the Manassites, from Aroer, which is by the valley of the Arnon, even Gilead and Bashan.
34 Game da sauran ayyukan mulkin Yehu, da dukan abin da ya yi, a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
Now the rest of the acts of Jehu, and all that he did, and all his might, aren’t they written in the book of the chronicles of the kings of Israel?
35 Yehu ya huta tare da kakanninsa, aka binne shi a Samariya. Yehoyahaz kuma ya ci sarauta bayansa.
Jehu slept with his fathers; and they buried him in Samaria. Jehoahaz his son reigned in his place.
36 Yehu ya yi sarautar Isra’ila a Samariya shekara ashirin da takwas.
The time that Jehu reigned over Israel in Samaria was twenty-eight years.

< 2 Sarakuna 10 >