< 1 Sama’ila 25 >

1 Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran.
Now Samuel died. All Israel gathered together and mourned for him, and they buried him in his house at Ramah. Then David rose and went down to the wilderness of Paran.
2 A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel.
There was a man in Maon, whose possessions were in Carmel. The man was very wealthy. He had three thousand sheep and one thousand goats. He was shearing his sheep in Carmel.
3 Ana ce da shi Nabal, sunan matarsa kuwa Abigiyel. Tana da hikima ga ta kuma kyakkyawa, amma mijinta mai rowa ne marar mutunci. Shi daga kabilar Kaleb ne.
The man's name was Nabal, and the name of his wife was Abigail. The woman was intelligent and beautiful in appearance. But the man was harsh and evil in his dealings. He was a descendant of the house of Caleb.
4 Lokacin da Dawuda yake a jeji, ya ji labari cewa Nabal yana askin tumaki.
David heard in the wilderness that Nabal was shearing his sheep.
5 Sai ya zaɓi samari goma ya aike su wurin Nabal a Karmel su gaishe shi a madadinsa,
So David sent ten young men. David said to the young men, “Go up to Carmel, go to Nabal, and greet him in my name.
6 su ce masa, “Ranka yă daɗe, ina maka fatan alheri, kai da gidanka da dukan abin da kake da shi!
You will say to him, 'Live in prosperity. Peace to you and peace to your house, and peace be to all that you have.
7 “Na ji cewa, yanzu lokacin askin tumaki ne. Sa’ad da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, kuma duk zamansu a Karmel ba abin da yake nasu da ya ɓata.
I hear that you have shearers. Your shepherds have been with us, and we did them no harm, and they missed nothing the whole time they were in Carmel.
8 Ka tambayi bayinka za su kuwa gaya maka. Saboda haka ka yi wa mutanena kirki, gama yau ranar biki ce. Ina roƙonka ka ba wa samarina, wato, bayinka, da ni ɗanka Dawuda, duk abin da kake iya ba su.”
Ask your young men, and they will tell you. Now let my young men find favor in your eyes, for we have come on a festive day. Please give whatever you have on hand to your servants and to your son David.'”
9 Da mutanen Dawuda suka isa wurin Nabal, suka ba wa Nabal wannan saƙo a sunan Dawuda, sai suka jira.
When David's young men arrived, they said all of this to Nabal on David's behalf and then waited.
10 Nabal ya ce wa mutanen Dawuda, “Wane ne wannan Dawuda? Wane ne wannan ɗan Yesse? Yawancin bayi suna tayar wa iyayengijinsu a kwanakin nan.
Nabal answered David's servants, “Who is David, and who is the son of Jesse? There are many servants these days who are breaking away from their masters.
11 Don me zan ɗauki burodina da ruwana, da kuma naman da na yanka saboda masu yin wa tumakina aski in ba mutanen da ban ma san inda suka fito ba?”
Should I take my bread and my water and my meat that I have killed for my shearers, and give it to men who come from I do not know where?”
12 Mutanen Dawuda suka juya suka koma. Da suka iso sai suka faɗa wa Dawuda abin da Nabal ya ce.
So David's young men turned away and came back, and told him everything that was said.
13 Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa yă rataya takobinsa.” Sai duk suka yi haka. Dawuda kuma ya rataya nasa. Mutum wajen ɗari huɗu suka tafi tare da Dawuda, mutum ɗari biyu kuwa suka zauna suna gadin kayansu.
David said to his men, “Every man strap on his sword.” So every man strapped on his sword. David also strapped on his sword. About four hundred men followed after David, and two hundred stayed by the baggage.
14 Ɗaya daga cikin bayin Nabal ya gaya wa Abigiyel matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko da bayinsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su.
But one of the young men told Abigail, Nabal's wife; he said, “David sent messengers out of the wilderness to greet our master, and he insulted them.
15 Waɗannan mutane kuwa sun yi mana kirki ƙwarai, ba su ba mu wata wahala ba. Babu abu guda da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su.
Yet the men were very good to us. We were not harmed and did not miss anything as long as we went with them when we were in the fields.
16 Dare da rana sun zama mana katanga kewaya da mu, a duk tsawon lokacin da muke kiwon tumakinmu kusa da su.
They were a wall to us both day and night, all the while we were with them tending the sheep.
17 Ki yi nazari a kai, ki ga ko za ki iya yin wani abu, domin masifa yana nan rataye a wuyan maigidanmu da dukan iyalin gidansa. Shi mugun mutum ne wanda ba wani da zai iya yin masa magana.”
Therefore know this and consider what you will do, for evil is plotted against our master, and against his whole house. He is such a worthless fellow that one cannot reason with him.”
18 Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna.
Then Abigail hurried and took two hundred loaves, two bottles of wine, five sheep already prepared, five measures of parched grain, one hundred clusters of raisins, and two hundred cakes of figs, and laid them on donkeys.
19 Sai ta ce wa bawanta, “Yi gaba, zan bi ka”. Amma ba tă gaya wa Nabal, mijinta ba.
She said to her young men, “Go on before me, and I will come after you.” But she did not tell her husband Nabal.
20 Da tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa suna gangarowa zuwa wajen da take. Sai ta tafi, ta sadu da su.
As she rode on her donkey and came down by the cover of the mountain, David and his men came down toward her, and she met them.
21 Bai daɗe ba da Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abinsa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta.
Now David had said, “Surely in vain have I guarded all that this man has in the wilderness, so that nothing was missed of all that belonged to him, and he has returned me evil for good.
22 Bari Allah yă yi duk abin da ya ga dama da ni in na bar ko ɗaya daga mazan da suke da tare shi, gobe da safe.”
May God do so to me, David, and more also, if by the morning I leave so much as one male of all who belong to him.”
23 Da Abigiyel ta ga Dawuda, sai ta gaggauta ta sauka daga kan jaki, ta rusuna a gaban Dawuda da fuskarta har ƙasa.
When Abigail saw David, she hurried and got down from her donkey and lay before David facedown and bowed herself to the ground.
24 Ta fāɗi a ƙafafunsa ta ce, “Bari laifin yă zama nawa, ranka yă daɗe. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka ji abin da baiwarka za tă ce.
She lay at his feet and said, “On me alone, my master, be the guilt. Please let your servant speak to you, and listen to the words of your servant.
25 Kada ranka yă daɗe, yă kula da Nabal, mugun mutumin nan. Shi dai kamar sunansa ne, sunansa Wawa ne, kuma wawanci yana cikinsa. Amma ni baiwarka, ban ga mutanen da ranka yă daɗe ya aika ba.
Let not my master regard this worthless fellow, Nabal, for as his name is, so is he. Nabal is his name, and folly is with him. But I your servant did not see the young men of my master, whom you sent.
26 Da yake yanzu, ya mai girma, Ubangiji ya hana ka zubar da jini da kuma ɗaukan wa kanka fansa, muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, bari maƙiyinka da dukan waɗanda suke niyya su cuci shugabana su zama kamar Nabal.
Now then, my master, as Yahweh lives, and as you live, since Yahweh has restrained you from bloodshed, and from avenging yourself with your own hand, now let your enemies, and those who seek to do evil to my master, be like Nabal.
27 Bari kuma ka karɓi wannan kyautar da baiwarka ta kawo don samarin da suke binka.
Now let this present that your servant has brought to my master be given to the young men who follow my master.
28 Ina roƙonka ka gafarta wa baiwarka laifinta gama tabbatacce Ubangiji zai ba shugabana dawwammamiyar sarauta, gama kana yin yaƙin Ubangiji ne. Kuma ba wani mugun abin da zai same ka muddin kana a raye.
Please forgive the trespass of your servant, for Yahweh will certainly make my master a sure house, because my master is fighting the battles of Yahweh; and evil will not be found in you so long as you live.
29 Ko da yake wani mutum yana fafaranka domin yă kashe ka, Ubangiji Allahnka zai kiyaye ranka. Amma za a wurgar da rayukan maƙiyanka kamar yadda ake wurga dutsen majajjawa.
Though men rise up to pursue you to take your life, yet the life of my master will be bound in the bundle of the living by Yahweh your God; and he will sling away the lives of your enemies, as from the pocket of a sling.
30 Sa’ad da Ubangiji ya cika kowane alherinsa da ya yi wa shugabana alkawari, ya kuma keɓe shi sarki a bisa Isra’ila,
Yahweh will have done for my master everything he promised you, and has appointed you leader over Israel.
31 kada yă zama cewa zuciyarka ta ba ka laifi ko ka damu cewa kana da alhakin jini, kada ka yi ramuwa da kanka. Sa’ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, ka tuna da ni, baiwarka.”
This will not be a staggering burden for you—that you have poured out innocent blood, or because my master attempted to rescue himself. For when Yahweh will do good for my master, remember your servant.”
32 Dawuda ya ce wa Abigiyel, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki don ki same ni yau.
David said to Abigail, “May Yahweh, the God of Israel, be blessed, he who sent you to meet me today.
33 Bari Allah yă albarkace ki saboda hikima yanke hukuncinki da kuma hana ni zubar da jini da ɗauka wa kaina fansa da hannuna a wannan rana.
Your wisdom is blessed and you are blessed, because you have kept me today from bloodshed and from avenging myself with my own hand!
34 Ubangiji, ya hana ni in yi miki ɓarna. Da ba don kin zo kin sadu da ni ba, na rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila Mai Rai, babu ko ɗaya daga cikin mazan gidan Nabal da zai rage gobe da safe.”
For in truth, as Yahweh, the God of Israel, lives, he who has kept me from hurting you, unless you had hurried to come meet me, there would certainly have not been left to Nabal so much as one male baby by morning.”
35 Sa’an nan Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa daga hannunta, ya kuma ce mata, “Ki koma gida kada ki damu, na ji koke-kokenki, zan kuma biya miki bukatarki.”
So David received from her hand what she had brought him; he said to her, “Go up in peace to your house; see, I have listened to your voice and have accepted you.”
36 Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye.
Abigail went back to Nabal; behold, he was holding a feast in his house, like the feast of a king; and Nabal's heart was merry within him, for he was very drunk. So she told him nothing at all until the morning light.
37 Da safe sa’ad da Nabal ya natsu, sai matarsa ta gaya masa dukan abin da ya faru. Sai zuciyarsa ta tsinke, ya zama kamar dutse.
It came about in the morning, when the wine had gone out of Nabal, that his wife told him these things; his heart died within him, and he became like a stone.
38 Bayan kusan kwana goma, Ubangiji ya bugi Nabal, sai ya mutu.
It came about ten days later that Yahweh attacked Nabal so that he died.
39 Da Dawuda ya sami labarin mutuwar Nabal, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya sāka mini a kan irin renin da Nabal ya yi mini. Ya hana bawansa yin mugunta, ga shi ya ɗora wa Nabal muguntar da ya yi.” Sai Dawuda ya aika wa Abigiyel cewa tă zama matarsa.
When David heard that Nabal was dead, he said, “May Yahweh be blessed, who has taken up the cause of my insult from the hand of Nabal and has kept back his servant from evil. He has turned Nabal's evil action back on his own head.” Then David sent and spoke to Abigail, to take her to himself as wife.
40 Bayin Dawuda suka tafi Karmel suka ce wa Abigiyel, “Dawuda ya aike mu gare ki, mu zo mu ɗauke ki ki zama matarsa.”
When David's servants had come to Abigail at Carmel, they spoke to her and said, “David has sent us to you to take you to him as his wife.”
41 Sai ta rusuna da fuskarta har ƙasa ta ce, “Ni baranyarka ce, na shirya in bauta maka in kuma wanke ƙafafun bayin shugabana.”
She arose, bowed herself with her face to the ground, and said, “See, your female servant is a servant to wash the feet of the servants of my master.”
42 Abigiyel ta tashi da sauri ta hau jaki, ta kuma sa’yan mata biyar da suke mata hidima su bi ta, suka tafi tare da’yan saƙon Dawuda. Ta kuwa zama matarsa.
Abigail hurried and arose, and rode on a donkey with five servant girls of hers who followed her; and she followed David's messengers and became his wife.
43 Dawuda a lokacin ya riga ya auri Ahinowam daga Yezireyel, dukansu suka zama matansa.
Now David had also taken Ahinoam of Jezreel as a wife; both of them became his wives.
44 Amma Shawulu ya aurar da Mikal,’yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake daga Gallim.
Also, Saul had given Michal his daughter, David's wife, to Paltiel son of Laish, who was of Gallim.

< 1 Sama’ila 25 >