< 1 Sarakuna 2 >

1 Da lokacin mutuwar Dawuda ya yi kusa, sai ya gargaɗe Solomon ɗansa, ya ce,
As the day of David's death approached, he commanded Solomon his son, saying,
2 “Ina gab da bin hanyar da kowa a duniya zai bi. Saboda haka ka yi ƙarfin hali, ka nuna kanka namiji,
“I am going the way of all the earth. Be strong, therefore, and show yourself a man.
3 ka kiyaye abin da Ubangiji Allahnka yake bukata. Yi tafiya a hanyoyinsa, ka kiyaye ƙa’idodi, da umarnai, da dokoki, da kuma farillansa, kamar yadda suke a rubuce a Dokar Musa, don ka yi nasara a cikin kome da za ka yi, da kuma inda za ka tafi.
Keep the commands of Yahweh your God to walk in his ways, to obey his statutes, his commandments, his decisions, and his covenant decrees, being careful to do what is written in the law of Moses, so you may prosper in all you do, wherever you go,
4 Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, ‘In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.’
so that Yahweh may fulfill his word which he spoke concerning me, saying, 'If your sons carefully watch their conduct, to walk before me faithfully with all their heart and with all their soul, you will never cease to have a man on the throne of Israel.'
5 “Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa.
You know also what Joab son of Zeruiah did to me, and what he did to the two commanders of the armies of Israel, to Abner son of Ner, and to Amasa son of Jether, whom he killed. He shed the blood of war in peace and put the blood of war on the belt around his waist and on the shoes on his feet.
6 Ka yi da shi gwargwadon hikimarka, amma kada ka bari yă gangara kabari da furfura cikin salama. (Sheol h7585)
Deal with Joab by the wisdom you have learned, but do not let his gray head go down to the grave in peace. (Sheol h7585)
7 “Amma ka yi alheri ga’ya’yan Barzillai mutumin Gileyad, ka sa su kasance a cikin waɗanda suke ci a teburinka. Sun goyi bayana sa’ad da nake gudu daga ɗan’uwanka Absalom.
However, show kindness to the sons of Barzillai the Gileadite, and let them be among those who eat at your table, for they came to me when I fled from Absalom your brother.
8 “Ka tuna, akwai kuma Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim, wanda ya yi ta yin mini muguwar la’ana a ranar da na tafi Mahanayim. Sa’ad da ya gangara ya same ni a Urdun, na rantse masa da sunan Ubangiji na ce, ‘Ba zan kashe ka da takobi ba.’
Look, there is with you Shimei son of Gera, the Benjamite of Bahurim, who cursed me with a violent curse on the day I went to Mahanaim. Shimei came down to meet me at the Jordan, and I swore to him by Yahweh, saying, 'I will not put you to death with the sword.'
9 Amma yanzu, kada ka ɗauke shi marar laifi. Kai mutum ne mai hikima; za ka san abin da za ka yi da shi. Ka kawo furfuransa zuwa kabari da jini.” (Sheol h7585)
Now therefore do not let him go free from punishment. You are a wise man, and you will know what you ought to do to him. You will bring his gray head down to the grave with blood.” (Sheol h7585)
10 Sa’an nan Dawuda ya huta tare da kakanninsa. Sai aka binne shi a Birnin Dawuda.
Then David slept with his ancestors and was buried in the city of David.
11 Ya yi sarauta shekaru arba’in a bisa Isra’ila. Wato, shekaru bakwai a Hebron da kuma talatin da uku a Urushalima.
The days that David reigned over Israel were forty years. He had reigned for seven years in Hebron and for thirty-three years in Jerusalem.
12 Solomon kuwa ya zauna a kan kujerar sarautar mahaifinsa Dawuda, mulkinsa kuwa ya kahu sosai.
Then Solomon sat on the throne of his father David, and his rule was firmly established.
13 To, sai Adoniya, ɗan Haggit ya tafi wurin Batsheba mahaifiyar Solomon. Ita kuwa ta tambaye shi ta ce, “Lafiya?” Ya amsa ya ce, “I, lafiya.”
Then Adonijah son of Haggith came to Bathsheba the mother of Solomon. She said, “Do you come peacefully?” He replied, “Peacefully.”
14 Sa’an nan ya ƙara da cewa, “Ina da ɗan wani abin da zan faɗa miki.” Ta ce, “Faɗa.”
Then he said, “I have something to say to you.” So she replied, “Speak.”
15 Sai ya ce, “Kamar yadda kika sani, mulkin nan nawa ne. Dukan Isra’ila suna ɗaukana a matsayin sarki. Amma abubuwa suka canja, sai mulkin ya koma ga ɗan’uwana; gama ya zo masa daga Ubangiji ne.
Adonijah said, “You know that the kingdom was mine, and that all Israel expected me to be king. But things changed, and the kingdom was given to my brother, for it was his from Yahweh.
16 Yanzu ina da roƙo guda da zan yi gare ki. Kada ki hana mini.” Ta ce, “Sai ka faɗa.”
Now I have one request of you, and do not turn away from my face.” Bathsheba said to him, “Speak.”
17 Sai ya ci gaba, “In kin yarda, ki yi magana da Sarki Solomon, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce yă ba ni yarinyan nan, Abishag, mutuniyar Shunam, tă zama matata.”
He said, “Please speak to Solomon the king, for he will not turn away from your face, so that he may give me Abishag the Shunammite as my wife.”
18 Batsheba ta ce, “Da kyau, zan yi magana da sarki dominka.”
Bathsheba said, “Very well, I will speak to the king.”
19 Sai Batsheba ta tafi wurin Sarki Solomon don tă yi masa magana a kan Adoniya. Sarki ya miƙe tsaye don yă sadu da ita, ya rusuna mata, ya kuma zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo wa mahaifiyar sarki kujerar sarauta, ta kuwa zauna a gefen damansa.
Bathsheba therefore went to King Solomon to speak to him for Adonijah. The king rose to meet her and bowed down to her. Then he sat down on his throne and had a throne brought for the king's mother. She sat at his right hand.
20 Ta ce, “Ina da ɗan roƙon da zan nema ka yi mini. Ina fata ba za ka hana ni ba.” Sai sarki ya amsa ya ce, “Mahaifiyata, sai ki faɗa in ji, ba zan hana miki ba.”
Then she said, “I wish to ask one small request of you, for you will not turn away from my face.” The king answered her, “Ask, my mother, for I will not turn away from your face.”
21 Saboda haka sai ta ce, “Ka sa a ba wa ɗan’uwanka Adoniya, Abishag mutuniyar Shunam tă zama matarsa.”
She said, “Let Abishag the Shunammite be given to Adonijah your brother as his wife.”
22 Sarki Solomon ya amsa wa mahaifiyarsa ya ce, “Me ya sa kika roƙar wa Adoniya Abishag mutuniyar Shunam kawai? Ki ma sa a ba shi mulkin mana. Ai, shi yayana ne. I, ki roƙa dominsa, da domin Abiyatar firist, da kuma domin Yowab ɗan Zeruhiya mana!”
King Solomon answered and said to his mother, “Why do you ask Abishag the Shunammite for Adonijah? Why do you not ask the kingdom for him also, for he is my elder brother—for him, for Abiathar the priest, and for Joab son of Zeruiah?”
23 Sai Sarki Solomon ya rantse da sunan Ubangiji ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani, idan ban sa Adoniya ya biya wannan roƙo da ransa ba!
Then King Solomon swore by Yahweh, saying, “May God do so to me, and more also, if Adonijah has not spoken this word against his own life.
24 Yanzu kuwa, muddin Ubangiji yana a raye, shi wanda ya kafa ni sosai a kan kujerar sarautar mahaifina Dawuda, ya kuma kafa mini mulki kamar yadda ya yi alkawari; za a kashe Adoniya yau!”
Now therefore as Yahweh lives, who has established me and set me on the throne of David my father, and who has made me a house as he promised, surely Adonijah will be put to death today.”
25 Saboda haka Sarki Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada yă kashe Adoniya; ya kuwa kashe shi.
So King Solomon sent Benaiah son of Jehoiada, and Benaiah found Adonijah and put him to death.
26 Ga Abiyatar firist kuwa sarki ya ce, “Tafi gonarka a Anatot. Ka cancanci ka mutu, amma ba zan kashe ka yanzu ba, domin ka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji Mai Iko Duka a gaban mahaifina Dawuda, ka kuma sha wahala tare mahaifina.”
Then to Abiathar the priest the king said, “Go to Anathoth, to your own fields. You are worthy of death, but I will not at this time put you to death, because you carried the ark of the Lord Yahweh before David my father and suffered in every way my father suffered.”
27 Saboda haka Solomon ya cire Abiyatar daga aikin firist na Ubangiji, ya cika maganar da Ubangiji ya yi a Shilo game da gidan Eli.
So Solomon dismissed Abiathar from being priest to Yahweh, that he might fulfill the word of Yahweh, which he had spoken concerning the house of Eli at Shiloh.
28 Sa’ad da labarin ya kai wurin Yowab, wanda ya haɗa kai da Adoniya, ko da yake bai haɗa kai da Absalom ba, sai ya gudu zuwa tentin Ubangiji, ya kama ƙahonin bagade ya riƙe.
The news came to Joab, for Joab had supported Adonijah, though he had not supported Absalom. So Joab fled to the tent of Yahweh and took hold of the horns of the altar.
29 Aka faɗa wa Sarki Solomon cewa Yowab ya gudu zuwa tentin Ubangiji, yana kuma kusa da bagade. Sai Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada ya ce, “Je ka kashe shi!”
It was told King Solomon that Joab had fled to the tent of Yahweh and was now beside the altar. Then Solomon sent Benaiah son of Jehoiada, saying, “Go, execute him.”
30 Sai Benahiya ya shiga tentin Ubangiji ya ce wa Yowab, “Sarki ya ce, ‘Ka fita!’” Amma Yowab ya amsa ya ce, “A’a, a nan zan mutu.” Sai Benahiya ya ce wa sarki, “Ga yadda Yowab ya amsa mini.”
So Benaiah came to the tent of Yahweh and said to him, “The king says, 'Come out.'” Joab replied, “No, I will die here.” So Benaiah returned to the king, saying, “Joab said he wanted to die at the altar.”
31 Sai sarki ya umarci Benahiya ya ce, “Yi kamar yadda ya faɗa. Ka kashe shi, ka kuma binne shi, ka wanke ni da gidan mahaifina daga laifin jini marasa laifin da Yowab ya zubar.
The king said to him, “Do as he has said. Kill him and bury him so that you may take away from me and from my father's house the blood that Joab shed without cause.
32 Ubangiji zai sāka masa saboda jinin da ya zubar, domin ba da sanin mahaifina Dawuda ne ya fāɗa wa mutum biyun nan da takobi ba. Dukansu biyu, Abner ɗan Ner, shugaban mayaƙan Isra’ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban mayaƙan Yahuda, mutane ne mafi kyau da kuma mafi adalci fiye da shi.
May Yahweh return his blood on his own head, because he attacked two men more righteous and better than himself and killed them with the sword, Abner son of Ner, the captain of the army of Israel, and Amasa son of Jether, the captain of the army of Judah, without my father David knowing it.
33 Bari alhakin jininsu yă koma a kan Yowab da kuma zuriyarsa har abada. Amma bari salamar Ubangiji tă kasance a kan Dawuda da zuriyarsa, da gidansa, da kuma mulkinsa, har abada.”
So may their blood return on the head of Joab and on the head of his descendants forever. But to David and his descendants, and to his house, and to his throne, may there be peace forever from Yahweh.”
34 Sai Benahiya ɗan Yehohiyada ya haura ya bugi Yowab, ya kashe shi, ya kuwa binne shi a gidansa a ƙauye.
Then Benaiah son of Jehoiada went up and attacked Joab and killed him. He was buried in his own house in the wilderness.
35 Sai sarki ya sa Benahiya ɗan Yehohiyada ya zama shugaba a bisa mayaƙa a matsayin Yowab, ya kuma sa Zadok firist a wurin Abiyatar.
The king put Benaiah son of Jehoiada over the army in his place, and he put Zadok the priest in Abiathar's place.
36 Sa’an nan sarki ya aika aka kawo Shimeyi, ya kuma ce masa, “Ka gina wa kanka gida a nan a Urushalima, ka zauna a ciki, kada ka kuskura ka tafi wani wuri.
Then the king sent and called for Shimei, and said to him, “Build yourself a house in Jerusalem and live there, and do not go out from there to any other place.
37 Gama ran da ka fita, ka haye Kwarin Kidron, ka tabbata za ka mutu, alhakin jininka kuwa zai koma kanka.”
For on the day you go out, and pass over the Kidron Valley, know you for certain that you will surely die. Your blood will be on your own head.”
38 Shimeyi ya amsa wa sarki ya ce, “Abin da ka faɗa yana da kyau. Bawanka zai yi kamar yadda ranka yă daɗe sarki, ya faɗa.” Shimeyi kuwa ya yi zama a Urushalima na dogon lokaci.
So Shimei said to the king, “What you say is good. As my master the king has said, so your servant will do.” So Shimei lived in Jerusalem for many days.
39 Amma bayan shekaru uku, biyu daga cikin bayin Shimeyi suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma’aka, sarkin Gat. Aka faɗa wa Shimeyi cewa, “Bayinka suna a Gat.”
But at the end of three years, two of the servants of Shimei ran away to Achish son of Maacah, the king of Gath. So they told Shimei, saying, “See, your servants are in Gath.”
40 Da jin haka, sai ya tashi ya shimfiɗa wa jakinsa abin zama, ya hau, ya tafi Gat wurin Akish domin neman bayinsa. Shimeyi kuwa ya dawo da su gida daga Gat.
Then Shimei arose, saddled his donkey and went to Achish in Gath to seek his servants. He went and brought his servants back from Gath.
41 Da aka faɗa wa Solomon cewa Shimeyi ya bar Urushalima zuwa Gat, har ya dawo.
When Solomon was told that Shimei had gone from Jerusalem to Gath and had returned,
42 Sai sarki ya aika a kawo Shimeyi, ya ce masa, “Ban sa ka rantse da sunan Ubangiji, na kuma ja maka kunne cewa, ‘A ranar da ka kuskura ka bar nan ka tafi wani wuri, ka tabbata za ka mutu ba’? A lokacin ka ce mini, ‘Abin da ka faɗa yana da kyau. Zan kuwa kiyaye.’
the king sent and called for Shimei and said to him, “Did I not make you swear by Yahweh and testify to you, saying, 'Know for certain that on the day you go out and go to any other place, you will surely die'? Then you said to me, 'What you say is good.'
43 To, me ya sa ba ka kiyaye rantsuwar da ka yi ga Ubangiji, ka kuma yi biyayya da umarnin da na ba ka ba?”
Why then have you not kept your oath to Yahweh and the command that I gave you?”
44 Sarki ya ce wa Shimeyi, “Ka sani a zuciyarka dukan muguntar da ka yi wa mahaifina Dawuda. Yanzu Ubangiji zai sāka maka saboda muguntarka.
The king also said to Shimei, “You know in your heart all the wickedness that you did to my father David. Therefore Yahweh will return your wickedness on your own head.
45 Amma za a yi wa Sarki Solomon albarka, sarautar Dawuda kuma za tă kasance a tsare a gaban Ubangiji har abada.”
But King Solomon will be blessed and the throne of David will be established before Yahweh forever.”
46 Sai sarki ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada, yă fita, yă bugi Shimeyi, yă kashe shi. Ya kuwa kashe shi. Mulki kuwa ya kahu sosai a hannun Solomon.
Then the king gave a command to Benaiah son of Jehoiada. He went out and put Shimei to death. So the rule was well established in Solomon's hand.

< 1 Sarakuna 2 >