< Προς Φιλιππησιους 2 >

1 Εἴ τις οὖν παράκλησις ἐν Χριστῷ, εἴ τι παραμύθιον ἀγάπης, εἴ τις κοινωνία πνεύματος, εἴ τις σπλάγχνα καὶ οἰκτιρμοί,
Idan akwai wani abin karfafawa cikin Almasihu. Idan da wata ta'aziyya daga kaunarsa. Idan akwai zumunta a Ruhu. Idan da tatausan jinkai da tausayi.
2 πληρώσατέ μου τὴν χαρὰν ἵνα τὸ αὐτὸ φρονῆτε, τὴν αὐτὴν ἀγάπην ἔχοντες, σύνψυχοι, τὸ ἓν φρονοῦντες,
Ku cika farin cikina don ku zama da tunani irin haka, kuna da kauna daya, kuna tarayya cikin Ruhu daya, ku kasance da manufa iri daya.
3 μηδὲν κατ’ ἐριθείαν μηδὲ κατὰ κενοδοξίαν, ἀλλὰ τῇ ταπεινοφροσύνῃ ἀλλήλους ἡγούμενοι ὑπερέχοντας ἑαυτῶν,
Kada ku yi komai cikin sonkai ko girman kai. A maimakon haka cikin zuciya mai tawali'u kowa na duban wadansu fiye da kansa.
4 μὴ τὰ ἑαυτῶν ἕκαστοι σκοποῦντες, ἀλλὰ καὶ τὰ ἑτέρων ἕκαστοι.
Kada kowa ya dubi bukatun sa, amma yana lura da bukatun wadansu.
5 τοῦτο φρονεῖτε ἐν ὑμῖν ὃ καὶ ἐν Χριστῷ Ἰησοῦ,
Ku yi tunani cikin hanya wadda ke cikin Almasihu Yesu.
6 ὃς ἐν μορφῇ θεοῦ ὑπάρχων οὐχ ἁρπαγμὸν ἡγήσατο τὸ εἶναι ἴσα θεῷ,
Wanda ya yi zama cikin siffar Allah, bai mai da daidaitarsa da Allah wani abin da zai rike ba.
7 ἀλλὰ ἑαυτὸν ἐκένωσεν μορφὴν δούλου λαβών, ἐν ὁμοιώματι ἀνθρώπων γενόμενος· καὶ σχήματι εὑρεθεὶς ὡς ἄνθρωπος
Maimakon haka, ya wofintar da kansa. Ya dauki siffar bawa. Ya bayyana cikin kamannin mutane. An same shi a bayyane kamar mutum.
8 ἐταπείνωσεν ἑαυτὸν γενόμενος ὑπήκοος μέχρι θανάτου, θανάτου δὲ σταυροῦ.
Ya kaskantar da kansa, ya yi biyayya har ga mutuwa, mutuwa ta gicciye.
9 διὸ καὶ ὁ θεὸς αὐτὸν ὑπερύψωσεν καὶ ἐχαρίσατο αὐτῷ τὸ ὄνομα τὸ ὑπὲρ πᾶν ὄνομα,
Saboda haka Allah ya ba shi mafificiyar daukaka. Ya ba shi suna wanda yafi kowanne suna.
10 ἵνα ἐν τῷ ὀνόματι Ἰησοῦ πᾶν γόνυ κάμψῃ ἐπουρανίων καὶ ἐπιγείων καὶ καταχθονίων,
Domin a cikin sunan Yesu kowace gwiwa za ta durkusa, gwiwoyin wadanda ke cikin sama da kuma duniya da kuma karkashin duniya.
11 καὶ πᾶσα γλῶσσα ἐξομολογήσηται ὅτι κύριος Ἰησοῦς Χριστὸς εἰς δόξαν θεοῦ πατρός.
Kuma kowanne harshe zai furta cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne, zuwa daukakar Allah Uba.
12 Ὥστε, ἀγαπητοί μου, καθὼς πάντοτε ὑπηκούσατε, μὴ ὡς ἐν τῇ παρουσίᾳ μου μόνον ἀλλὰ νῦν πολλῷ μᾶλλον ἐν τῇ ἀπουσίᾳ μου, μετὰ φόβου καὶ τρόμου τὴν ἑαυτῶν σωτηρίαν κατεργάζεσθε·
Domin wannan kaunatattuna, kamar yadda kullum kuke biyayya ba sai ina nan kadai ba. Balle yanzu da bananan, ku yi aikin cetonku da tsoro da far gaba.
13 θεὸς γάρ ἐστιν ὁ ἐνεργῶν ἐν ὑμῖν καὶ τὸ θέλειν καὶ τὸ ἐνεργεῖν ὑπὲρ τῆς εὐδοκίας.
Gama Allah ne yake aiki a cikinku ku yi nufi duka da aikata abin da zai gamshe shi.
14 πάντα ποιεῖτε χωρὶς γογγυσμῶν καὶ διαλογισμῶν,
Ku yi kowanne abu ba tare da gunaguni da gardama ba.
15 ἵνα γένησθε ἄμεμπτοι καὶ ἀκέραιοι, τέκνα θεοῦ ἄμωμα μέσον γενεᾶς σκολιᾶς καὶ διεστραμμένης, ἐν οἷς φαίνεσθε ὡς φωστῆρες ἐν κόσμῳ,
Domin ku zama marasa abin zargi kuma masu gaskiya, 'ya'yan Allah marasa aibi. Ku yi haka domin ku haskaka kamar haske a cikin wannan duniya, a tsakiyar karkatacciyar da gurbatacciyar tsara.
16 λόγον ζωῆς ἐπέχοντες, εἰς καύχημα ἐμοὶ εἰς ἡμέραν Χριστοῦ, ὅτι οὐκ εἰς κενὸν ἔδραμον οὐδὲ εἰς κενὸν ἐκοπίασα.
Ku rike kalmar rai da karfi domin in sami dalilin daukaka Almasihu a ranarsa. Sa'annan zan san cewa ban yi tseren banza ba, ban kuma yi wahalar banza ba.
17 ἀλλὰ εἰ καὶ σπένδομαι ἐπὶ τῇ θυσίᾳ καὶ λειτουργίᾳ τῆς πίστεως ὑμῶν, χαίρω καὶ συνχαίρω πᾶσιν ὑμῖν·
Ko da ana tsiyaye ni kamar sadaka a kan hadaya da kuma hidimar bangaskiyarku, na yi farin ciki, kuma na yi farin ciki tare da ku duka.
18 τὸ δὲ αὐτὸ καὶ ὑμεῖς χαίρετε καὶ συνχαίρετέ μοι.
Kamar haka kuma sai ku yi farin ciki, ku yi farin ciki tare da ni.
19 Ἐλπίζω δὲ ἐν κυρίῳ Ἰησοῦ Τιμόθεον ταχέως πέμψαι ὑμῖν, ἵνα κἀγὼ εὐψυχῶ γνοὺς τὰ περὶ ὑμῶν.
Amma na yi niyya in aiko da Timoti wurin ku ba da dadewa ba, domin ni ma in sami karfafuwa idan na san al'amuran ku.
20 οὐδένα γὰρ ἔχω ἰσόψυχον ὅστις γνησίως τὰ περὶ ὑμῶν μεριμνήσει,
Gama bani da wani wanda halinmu yayi daidai da nasa, wanda yake juyayin ku da gaskiya.
21 οἱ πάντες γὰρ τὰ ἑαυτῶν ζητοῦσιν, οὐ τὰ Χριστοῦ Ἰησοῦ.
Domin duka ribar kansu suke nema bata Yesu Almasihu ba.
22 τὴν δὲ δοκιμὴν αὐτοῦ γινώσκετε, ὅτι ὡς πατρὶ τέκνον σὺν ἐμοὶ ἐδούλευσεν εἰς τὸ εὐαγγέλιον.
Amma kun san darajar sa, kamar yadda da ke hidimar mahaifisa, haka ya bauta mani cikin bishara.
23 τοῦτον μὲν οὖν ἐλπίζω πέμψαι ὡς ἂν ἀφίδω τὰ περὶ ἐμὲ ἐξαυτῆς·
Shi nake sa zuciyar in aiko maku ba da dadewa ba idan naga yadda al'amura nake gudana.
24 πέποιθα δὲ ἐν κυρίῳ ὅτι καὶ αὐτὸς ταχέως ἐλεύσομαι.
Amma ina da gabagadi cikin Ubangiji cewa ni da kaina zan zo ba da dadewa ba.
25 Ἀναγκαῖον δὲ ἡγησάμην Ἐπαφρόδιτον τὸν ἀδελφὸν καὶ συνεργὸν καὶ συνστρατιώτην μου, ὑμῶν δὲ ἀπόστολον καὶ λειτουργὸν τῆς χρείας μου, πέμψαι πρὸς ὑμᾶς,
Amma ina tunanin yakamata in sake aiko maku da Abafaroditus, shi dan'uwana ne, abokin aiki, da abokin yaki, manzon ku da kuma bawa domin bukatu na.
26 ἐπειδὴ ἐπιποθῶν ἦν πάντας ὑμᾶς, καὶ ἀδημονῶν διότι ἠκούσατε ὅτι ἠσθένησεν.
Da shike yana marmarin ku duka, ya damu kwarai da shike kun ji yayi rashin lafiya.
27 καὶ γὰρ ἠσθένησεν παραπλήσιον θανάτῳ· ἀλλὰ ὁ θεὸς ἠλέησεν αὐτόν, οὐκ αὐτὸν δὲ μόνον ἀλλὰ καὶ ἐμέ, ἵνα μὴ λύπην ἐπὶ λύπην σχῶ.
Da gaske yayi rashin lafiya har ya kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayin sa, ba shi kadai ba, amma har da ni, domin kada in yi bakin ciki kan bakin ciki.
28 σπουδαιοτέρως οὖν ἔπεμψα αὐτὸν ἵνα ἰδόντες αὐτὸν πάλιν χαρῆτε κἀγὼ ἀλυπότερος ὦ.
Domin haka na yi niyyar aiko shi, saboda idan kun sake ganinsa za ku yi farin ciki ni kuma in kubuta daga juyayi.
29 προσδέχεσθε οὖν αὐτὸν ἐν κυρίῳ μετὰ πάσης χαρᾶς, καὶ τοὺς τοιούτους ἐντίμους ἔχετε,
Ku karbi Abafaroditus da dukan murna cikin Ubangiji. Ku ga darajar mutane irin sa.
30 ὅτι διὰ τὸ ἔργον Χριστοῦ μέχρι θανάτου ἤγγισεν, παραβολευσάμενος τῇ ψυχῇ ἵνα ἀναπληρώσῃ τὸ ὑμῶν ὑστέρημα τῆς πρός με λειτουργίας.
Domin saboda aikin Almasihu ne ya kusan mutuwa. Ya sadakar da ransa domin ya bauta mani domin ya cika hidimar da ya kamata ku yi mani.

< Προς Φιλιππησιους 2 >