< Numbers 28 >

1 And Jehovah speaketh unto Moses, saying,
Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
2 'Command the sons of Israel, and thou hast said unto them, My offering, My bread for My fire-offerings, My sweet fragrance, ye take heed to bring near to Me in its appointed season.
“Ka umarci Isra’ilawa cewa, ‘Ku tabbatar kun miƙa mini hadaya ta abinci ta wuta mai daɗin ƙanshi a gare ni, a daidai lokaci.’
3 'And thou hast said to them, This [is] the fire-offering which ye bring near to Jehovah: two lambs, sons of a year, perfect ones, daily, a continual burnt-offering;
Ka gaya musu, ‘Ga hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, da za ku miƙa wa Ubangiji, raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya, marasa lahani.
4 the one lamb thou preparest in the morning, and the second lamb thou preparest between the evenings;
A miƙa rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma,
5 and a tenth of the ephah of flour for a present, mixed with beaten oil, a fourth of the hin;
tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau.
6 a continual burnt-offering, which was made in mount Sinai, for sweet fragrance, a fire-offering to Jehovah;
Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
7 and its libation, a fourth of the hin for the one lamb; in the sanctuary cause thou a libation of strong drink to be poured out to Jehovah.
Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki.
8 'And the second lamb thou dost prepare between the evenings; as the present of the morning, and as its libation thou preparest — a fire-offering, a sweet fragrance to Jehovah.
Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa shi da yamma, tare irin hadaya ta lallausan gari, da hadaya ta sha da ka yi da safe. Wannan hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
9 'And on the sabbath-day, two lambs, sons of a year, perfect ones, and two-tenth deals of flour, a present, mixed with oil, and its libation;
“‘A ranar Asabbaci, za a miƙa’yan raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya marasa lahani, tare da hadaya ta sha, da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai.
10 the burnt-offering of the sabbath in its sabbath, besides the continual burnt-offering and its libation.
Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace Asabbaci, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da ta hadaya ta sha.
11 'And in the beginnings of your months ye bring near a burnt-offering to Jehovah: two bullocks, sons of the herd, and one ram, seven lambs, sons of a year, perfect ones;
“‘A rana ta fari ga kowane wata, za a miƙa wa Ubangiji hadayun’yan bijimai biyu, rago ɗaya, da’yan tumaki bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu kuma marasa lahani.
12 and three-tenth deals of flour, a present, mixed with oil, for the one bullock, and two-tenth deals of flour, a present, mixed with oil, for the one ram;
Da kowane bijimi, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi uku bisa goma na efa; da ɗan rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi biyu bisa goma na efa;
13 and a several tenth deal of flour, a present, mixed with oil, for the one lamb; a burnt-offering, a sweet fragrance, a fire-offering to Jehovah;
da kowane tunkiya kuma, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai, na kashi ɗaya bisa goma na efa. Wannan hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
14 and their libations are a half of the hin to a bullock, and a third of the hin to a ram, and a fourth of the hin to a lamb, of wine; this [is] the burnt-offering of every month for the months of the year;
Da kowane bijimi, za a kasance da hadaya ta sha, na rabin kwalabar ruwan inabi; da rago kuwa, a kasance da kashi ɗaya bisa uku; da kowace tunkiya kuma, a kasance da kashi ɗaya bisa huɗu. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane sabon wata na shekara.
15 and one kid of the goats for a sin-offering to Jehovah; besides the continual burnt-offering it is prepared, and its libation.
Ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadaya ta sha, za a miƙa bunsuru ɗaya ga Ubangiji, hadaya ce don zunubi.
16 'And in the first month, in the fourteenth day of the month, [is] the passover to Jehovah;
“‘Za a yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga wata na fari.
17 and in the fifteenth day of this month [is] a festival, seven days unleavened food is eaten;
A rana ta goma sha biyar ga wannan wata, za a yi biki; kwana bakwai za a ci burodi marar yisti.
18 in the first day [is] an holy convocation, ye do no servile work,
A rana ta farko, za ku yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi na kullum ba.
19 and ye have brought near a fire-offering, a burnt-offering to Jehovah: two bullocks, sons of the herd, and one ram, and seven lambs, sons of a year, perfect ones they are for you;
Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, rago ɗaya, da’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya; dukansu kuma marasa lahani ga Ubangiji.
20 and their present, flour mixed with oil, three-tenth deals for a bullock, and two-tenth deals for a ram ye do prepare;
Da kowane bijimi, a shirya kashi ɗaya bisa uku na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda kuwa, a shirya kashi biyu bisa goma na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;
21 a several tenth deal thou preparest for the one lamb, for the seven lambs,
da kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
22 and one goat, a sin-offering, to make atonement for you.
A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara.
23 'Apart from the burnt-offering of the morning, which [is] for the continual burnt-offering, ye prepare these;
Ku shirya wannan tare da hadaya ta ƙonawa ta kowace safiya.
24 according to these ye prepare daily, seven days, bread of a fire-offering, a sweet fragrance, to Jehovah; besides the continual burnt-offering it is prepared, and its libation;
Ta haka za a shirya abinci don hadayar da aka yi da wuta, kowace rana, har kwana bakwai don daɗin ƙanshi ga Ubangiji; a shirya shi haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadaya ta sha.
25 and on the seventh day a holy convocation ye have, ye do no servile work.
A rana ta bakwai, za ku yi tsattsarkan taro, amma ba za a yi aikin da aka saba yi kullum ba.
26 'And in the day of the first-fruits, in your bringing near a new present to Jehovah, in your weeks, a holy convocation ye have; ye do no servile work;
“‘A ranar nunan fari, sa’ad da za ku miƙa wa Ubangiji hadayar sabon hatsi, a lokacin Bikin Makoni, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba.
27 and ye have brought near a burnt-offering for sweet fragrance to Jehovah: two bullocks, sons of the herd, one ram, seven lambs, sons of a year,
A miƙa hadaya ta ƙonawa da’yan bijimai biyu, rago ɗaya da’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
28 and their present, flour mixed with oil, three-tenth deals to the one bullock, two-tenth deals to the one ram,
Da kowane bijimi a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai;
29 a several tenth deal to the one lamb, for the seven lambs;
da kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
30 one kid of the goats to make atonement for you;
A haɗa da bunsuru guda don yin muku kafara.
31 apart from the continual burnt-offering and its present ye prepare [them] (perfect ones they are for you) and their libations.
A miƙa waɗannan tare da hadayarsu ta sha, haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadayarta ta sha. A tabbata dabbobin nan marasa lahani ne.

< Numbers 28 >